Atiku Abubakar Ya Yi Alƙawarin Dawo Da Tallafin Man Fetur Idan Aka Zaɓe Shi Shugaban Ƙasar Najeriya
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi a matsayin Shugaban Ƙasar Najeriya, zai dawo da tallafin man fetur.
Ya kuma ce duk wanda ya wawure kuɗaɗen tallafin Najeriya, dole ne ya mayar da kuɗin.
Wannan kalamin nasa zai faranta rayuwar mutanen Nijeriya Musamman talakawa ganin yanda suke shan wahala saboda janyen tallafin man fetur da aka yi.
Tun ranar da aka janye tallafin man fetur aka shiga damuwa da matsatsi wanda har yanzu ba a fita daga cikinsa ba.






