Home Labarai ฦ˜ungiya ta buฦ™aci gwamnatin Sokoto ta ษ—auki mataki kan Shaikh Lukuwa da...

ฦ˜ungiya ta buฦ™aci gwamnatin Sokoto ta ษ—auki mataki kan Shaikh Lukuwa da Matashi Mai Barewa don kaucewa hatsaniya

8
0

ฦ˜๐˜‚๐—ป๐—ด๐—ถ๐˜†๐—ฎ๐—ฟ ๐—œ๐—›๐—ฅ๐—–-๐—ฅ๐—™๐—ง ๐˜๐—ฎ ๐—ฏ๐˜‚ฦ™๐—ฎ๐—ฐ๐—ถ ๐—š๐˜„๐—ฎ๐—บ๐—ป๐—ฎ๐˜๐—ถ๐—ป ๐—ฆ๐—ผ๐—ธ๐—ผ๐˜๐—ผ ๐˜๐—ฎ ษ—๐—ฎ๐˜‚๐—ธ๐—ถ ๐—บ๐—ฎ๐˜๐—ฎ๐—ธ๐—ถ ๐—ธ๐—ฎ๐—ป ๐—บ๐—ฎ๐˜€๐˜‚ ฦ™๐—ผฦ™๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐—ป ษ—๐—ฎ๐˜‚๐—ธ๐—ฎ๐—ฟ ๐—ฑ๐—ผ๐—ธ๐—ฎ ๐—ฎ ๐—ต๐—ฎ๐—ป๐—ป๐˜‚ ๐—ฎ๐—ธ๐—ฎ๐—ป ๐—ฆ๐—ต๐—ฒ๐—ถ๐—ธ๐—ต ๐— ๐˜‚๐˜€๐—ฎ ๐—Ÿ๐˜‚๐—ธ๐˜‚๐˜„๐—ฎ ๐—ฑ๐—ผ๐—บ๐—ถ๐—ป ๐˜๐—ฎ๐—ฏ๐—ฏ๐—ฎ๐˜๐—ฎ๐—ฟ ๐—ฑ๐—ฎ ๐˜‡๐—ฎ๐—บ๐—ฎ๐—ป ๐—น๐—ฎ๐—ณ๐—ถ๐˜†๐—ฎ ๐—ฎ ๐—ท๐—ถ๐—ต๐—ฎ๐—ฟ

ฦ˜ungiyar kare haฦ™ฦ™in bilโ€™adama ta International Human Rights Commission โ€“ Relief Fund Trust (IHRC-RFT), ta buฦ™aci Gwamnatin Jihar Sokoto da jamiโ€™an tsaro su gaggauta ษ—aukar mataki kan masu ฦ™oฦ™arin ษ—aukar doka a hannu, musamman dangane da lamarin Sheikh Musa Lukuwa.

A wata sanarwa da Daraktan Hulษ—a da Jamaโ€™a na IHRC-RFT a Jihar Sokoto ya fitar ga manema labarai a daren Talata, ฦ™ungiyar ta yi Allah-wadai da abin da ta bayyana a matsayin gazawar hukumomin tsaro wajen ษ—aukar mataki kan wasu kalamai da Sheikh Musa Lukuwa ya yi da kuma ikirarin da wasu matasa suka yi akan Malamin.

ฦ˜ungiyar ta ce kalaman na iya haifar da tashin hankali da tada zaune tsaye, yayin barazanar matasan masu dauke da makamai kan iya rura wutar rikici a jihar.

IHRC ta yi kira ga Gwamnatin Sokoto da jamiโ€™an tsaro da su ษ—auki matakin gaggawa domin dakile duk wani abu da ka iya haifar da sabon rikici.

IHRC-RFT ta kuma yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da bin doka da oda, tare da kare zaman lafiya da tsaron alโ€™ummar jihar Sokoto.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here