Home Rahoto Atiku ya ce zai tabbatar da ci gaba da aikin haƙo man...

Atiku ya ce zai tabbatar da ci gaba da aikin haƙo man fetur a yankin Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe

28
0

Ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin cewa idan aka zaɓe shi, zai dawo da tallafin man fetur da kuma tallafin wutar lantarki domin rage wa ’yan Najeriya nauyin tsadar rayuwa.

Atiku ya bayyana hakan ne a yau yayin taron gangamin neman zaɓensa da aka gudanar a jihar Bauchi.

Ya kuma yi alƙawarin dawo da cikakken tsaro a yankin Arewa maso Gabas da sauran sassan ƙasar baki ɗaya.

Haka kuma, Atiku ya ce zai tabbatar da ci gaba da aikin hako man fetur a yankin Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.

—MIKIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here