Home Siyasa Atiku Ga ADC: Najeriya Na Buƙatar Shugaban Da Zai Iya Mulki, Ba...

Atiku Ga ADC: Najeriya Na Buƙatar Shugaban Da Zai Iya Mulki, Ba Mai Ɗaukar Hankali A Kafafen Sada Zumunta Ba

4
0

Atiku Ga ADC: Najeriya Na Buƙatar Shugaban Da Zai Iya Mulki, Ba Mai Ɗaukar Hankali A Kafafen Sada Zumunta Ba

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya buƙaci jam’iyyar ADC da ta fifita cancanta, ƙwarewa da gogewa wajen zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027.

Atiku ya ce Najeriya na cikin matsin tattalin arziƙi, matsalar tsaro da tarin basussuka, don haka ƙasar ba za ta iya ɗaukar shugabancin “gwaji” ba.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya bayyana cewa zaɓe ba a lashe shi da surutun kafafen sada zumunta kawai ba, yana mai cewa shugabanci na buƙatar tsari, dabaru da ƙwarewar gudanarwa.

“Najeriya na buƙatar shugaban da ya shirya tsaf domin gyara ƙasa, ba wanda zai dogara da farin jini a intanet kawai ba,” inji shi.

Ya ƙara da cewa ADC na da babban alhakin zaɓar ɗan takarar da zai iya kalubalantar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

Rahotanni na nuna cewa kalaman Atiku na zuwa ne yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan waɗanda ke neman tikitin shugaban ƙasa a ƙarƙashin ADC kafin zaɓe mai zuwa.
Ku biyo Mikiya TV domin samun sahihan labarai cikin gaggawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here