MUHIMMANCIN KULA DA LAFIYAR ƘWAƘWALWA A RAYUWAR YAU DA KULLUM
Shin kin taɓa yin murmushi a gaban mutane alhali a cikin zuciyarki kina fama da damuwa da ba ki iya bayyana wa kowa?
Shin ka taɓa jin kamar rayuwa ta yi maka nauyi, tunani ya yi maka yawa, amma ka kasa samun wanda za ka buɗe wa zuciyarka?
Wannan na daga cikin dalilan da ya kamata mu fahimci muhimmancin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa.
Lafiyar ƙwaƙwalwa wani muhimmin ɓangare ne na lafiyar ɗan Adam wanda mutane da dama ba sa ba shi kulawar da ta dace. Sau da yawa idan aka ambaci lafiya, abin da mutane ke fara tunawa shi ne lafiyar jiki, kamar zazzaɓi, ciwon kai, ciwon ciki ko wasu cututtuka. Amma mutane da yawa suna mantawa cewa ƙwaƙwalwa ma tana buƙatar kulawa kamar yadda sauran sassan jiki suke buƙata.
Lafiyar ƙwaƙwalwa tana da alaƙa da yadda mutum yake tunani, ji, mu’amala da mutane da kuma yadda yake fuskantar ƙalubalen rayuwa.
Me ya sa kula da lafiyar ƙwaƙwalwa yake da muhimmanci?
Na farko, yana taimaka wa mutum wajen sarrafa damuwa da matsalolin rayuwa. Rayuwa tana cike da ƙalubale, amma samun kyakkyawar lafiyar ƙwaƙwalwa yana taimaka wa mutum wajen fuskantar matsaloli cikin nutsuwa.
Na biyu, yana taimaka wa mutum wajen samun kyakkyawar mu’amala da sauran mutane. Mutumin da yake kula da lafiyar ƙwaƙwalwarsa zai fi samun damar fahimtar kansa, sauraron wasu da kuma magance saɓani cikin hikima.
Abubuwan da ke iya shafar lafiyar ƙwaƙwalwa
Akwai abubuwa da dama da za su iya shafar lafiyar ƙwaƙwalwar mutum, daga cikinsu akwai:
- Matsin tattalin arziki da rashin kuɗi.
- Matsalolin aure da rashin fahimtar juna.
- Rashin kulawa da tausayi daga waɗanda ake tsammanin za su ba da kulawa.
- Yawan tunani da damuwar rayuwa.
- Rashin isasshen barci da hutawa.
- Fuskantar cin zarafi ko wasu abubuwan da suka raunata zuciya.
- Keɓewa da rashin samun wanda za a iya tattaunawa da shi.
Ta yaya za mu kula da lafiyar ƙwaƙwalwarmu?
Yana da kyau mutum ya riƙa samun isasshen barci, cin abinci mai gina jiki, motsa jiki da kuma ba wa kansa lokacin hutawa.
Haka kuma, yana da kyau mutum ya riƙa tattaunawa da mutanen da ya yarda da su idan yana fuskantar damuwa. Kada mutum ya riƙa ɗaukar dukkan nauyin matsalolin duniya a kansa shi kaɗai.
Idan damuwa ta yi tsanani, ta daɗe ko ta fara hana mutum gudanar da ayyukansa na yau da kullum, yana da kyau ya nemi taimakon ƙwararren ma’aikacin lafiya.
Haka kuma, ya kamata mu daina yi wa mutanen da ke fama da matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa kallon raini ko ɗaukar su a matsayin marasa hankali. Suna buƙatar kulawa, fahimta da taimako, ba cin mutunci ba.
Saƙonmu zuwa ga al’umma a wannan gaɓar;
Mu fahimci cewa ba duk wanda yake murmushi ne yake cikin farin ciki ba. Ba duk wanda yake shiru ba ne yake lafiya, kuma ba duk wanda ya kasa bayyana damuwarsa ba ne yake nufin babu abin da yake damunsa ba.
Wani lokaci kalma mai daɗi na iya zama babban taimako ga wanda yake cikin damuwa.
Ku tuna cewa: Kula da lafiyar ƙwaƙwalwa ba rauni ba ne, alama ce ta sanin darajar kai da kuma muhimmancin rayuwa.
#Managarciya




