Sabbin alkaluman amincewar jama’a na kasa baki daya sun nuna cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da kaso 30 kacal na amincewar jama’a, wanda hakan babban hukunci ne ga gwamnatin da ta jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali da kuma kasa cika muhimman nauyinta na tafiyar da tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da tabbatar da tsaro.
Binciken da kamfanin Eagle Badger Data Analytics (EBDA) ya gudanar a fadin kasar nan ya nuna cewa kashi 30.2 cikin dari ne kawai ke amincewa da yadda Shugaba Tinubu ke tafiyar da mulki, yayin da kashi 47.5 cikin dari ke nuna rashin amincewa, sannan mafi yawan ‘yan kasa sun bayyana cewa rayuwarsu ta kara tabarbarewa tun bayan hawansa mulki.
A gare mu a jam’iyyar ADC, muhimmancin wannan rahoto a bayyane yake. Shugaban kasa da ke da kaso 30 kacal na goyon bayan jama’a bayan shekara uku a mulki ya rasa amincewar al’ummar Najeriya. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, kusan mutum bakwai cikin goma na ‘yan Najeriya ko dai ba su gamsu ba ne, ko kuma ba su yarda da alkiblar da ake tafiya da kasar ba. Wannan ba kalubalen siyasa ba ne kawai, wannan kin amincewa ce ta kasa baki daya.
Abin da ya fi daukar hankali a rahoton shi ne yadda kashi 62 cikin dari na ‘yan Najeriya suka ce rayuwarsu ta fi muni yanzu fiye da lokacin da Shugaba Tinubu ya hau mulki a watan Mayun 2023. Kashi 23.3 cikin dari ne kawai suka ce rayuwarsu ta inganta. Abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda kashi 42.4 cikin dari suka bayyana kansu a matsayin wadanda rayuwarsu ta kara tabarbarewa matuka a cikin shekaru ukun da suka gabata.
Wadannan alkaluma sun tabbatar da abin da ‘yan Najeriya ke fuskanta a kullum. Iyalai ba sa iya sayen kayan abinci na yau da kullum. Kudin sufuri sun yi tsada matuka. Kananan sana’o’i suna durkushewa. Matasa na fama da rashin aikin yi da karancin damammaki. Miliyoyin mutane masu kokarin neman na kansu sun kasa samar wa iyalansu rayuwa mai kyau.
Rahoton ya kuma nuna cewa farashin kayan abinci ya karu da sama da kaso 90 tun daga watan Mayun 2023, yayin da gaba daya hauhawar farashi ta kai kusan kaso 80. Wadannan ba alkaluman ‘yan adawa ba ne. Hakikanin abubuwa ne da ‘yan Najeriya ke gani a kasuwanni kowace rana.
Gwamnati na ci gaba da bayyana nasarorin tattalin arziki a takardu, amma ‘yan Najeriya ba alkaluma suke ci ba. Abinci suke ci. Kudin gida suke biya. Kudin makaranta suke biya. Kudin mota suke biya. Kuma suna fuskantar matsalar tsaro. A duk wadannan bangarori kuwa, rayuwa ta kara tsananta a karkashin wannan gwamnati.
Gazawar ba ta tsaya a tattalin arziki kadai ba. Hatta binciken ya nuna cewa matsalar tsaro na daga cikin manyan damuwar ‘yan Najeriya. A sassa da dama na kasar nan, manoma ba sa iya zuwa gonakinsu cikin aminci. Al’ummomi na ci gaba da fuskantar hare-haren ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane, da sauran masu aikata laifuka. Dubban mutane sun rasa rayukansu, yayin da miliyoyi ke rayuwa cikin tsoro da rashin tabbas.
Abin takaici shi ne, bayan shekara uku a mulki, gwamnati ba za ta iya cewa ta gaji wadannan matsaloli ba. Yanzu duk alhakin yana kan Shugaba Tinubu da gwamnatinsa. Ana auna shugabanci ne da sakamako, ba uzuri ba.
Abin da ya kamata ya kara damun Shugaban kasa shi ne yadda binciken ya nuna alaka kai tsaye tsakanin tabarbarewar rayuwar jama’a da rashin amincewa da gwamnati. Daga cikin ‘yan Najeriya da suka ce rayuwarsu ta kara muni a karkashin wannan gwamnati, sama da kashi 73 cikin dari sun nuna rashin amincewa da yadda Shugaban kasa ke gudanar da mulki.
Saboda haka, hukuncin da ‘yan Najeriya suka yanke a bayyane yake. Wannan gwamnati ta kasa inganta rayuwar jama’a, ta kasa kare kudaden shiga na gidaje, ta kasa samar da isassun damammaki ga matasa, kuma ta kasa dawo da amincewar jama’a game da makomar kasar nan.
Jam’iyyar ADC ta yi imanin cewa Najeriya ta cancanci fiye da haka. ‘Yan Najeriya sun cancanci gwamnati da ta fahimci cewa ci gaban tattalin arziki ya kamata ya kasance ana gani a gidaje, ba a tarukan manema labarai kadai ba. Sun cancanci shugabanci da zai fifita samar da ayyukan yi a kan farfaganda, tsaro a kan uzuri, da sakamako a kan surutu.
Yayin da kasar nan ke tunkarar shekarar 2027, wannan bincike ya kamata ya zama gargadi. ‘Yan Najeriya na magana a fili.
