Jam’iyyar ADC ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta sakin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, tana mai cewa ci gaba da tsare shi ya saɓa wa ƙa’idojin dimokuraɗiyya da ‘yancin faɗin albarkacin baki.
A wata sanarwa da ta fitar, ADC ta bayyana El-Rufai a matsayin “fursunan ra’ayi” (Prisoner of Conscience), tana mai zargin cewa an tsare shi ne saboda ra’ayoyinsa da matsayinsa kan wasu batutuwan siyasa.
Jam’iyyar ta ce a tsarin dimokuraɗiyya, kowane ɗan ƙasa na da ‘yancin bayyana ra’ayinsa cikin lumana ba tare da fargabar tsangwama ko tsarewa ba. Saboda haka, ta buƙaci a sake tsohon gwamnan cikin gaggawa ba tare da wani sharadi ba.
ADC ta kuma yi gargadin cewa duk wani mataki da zai tauye ‘yancin faɗar albarkacin baki na iya haifar da ƙarin ce-ce-ku-ce da rashin yarda da tsarin dimokuraɗiyya a tsakanin al’umma.
