Home Labarai A wani sabon hari ‘yan bindiga sun kashe mutane Biyar a Sakkwato 

A wani sabon hari ‘yan bindiga sun kashe mutane Biyar a Sakkwato 

20
0

A wani sabon hari da ‘yan bindiga suka kai a Litinin cikin ƙaramar hukumar Raɓah ta jihar Sakkwato sun kashe mutum biyar.

Wata majiya ta ce da misalin ƙarfe 3:00 na  rana Litinin ‘yan bindiga sun tare hanyar Rabah zuwa Maikujera in da suka buɗa  wuta ga wasu mutane dake  zirga-zirga ba li ba la.

‘Yan bindigar bayan sun kashe mutanen suka wuce ba tare da sun ɗauki komai ko neman wani bahasi ba.

Mutanen su biyar da suka kashe mutum biyu ‘yan ƙauyen Angamba ne, biyu  sun fito daga Tofa, sai ɗaya daga  garin Rabah yake, dukkansu a ƙaramar hukumar Rabah suke.

Akwai waɗanda suka ji rauni a lokacin harin suna karɓar kulawa a Asibiti kamar yadda majiyar ta sanar.

Ƙaramar hukumar Raɓah tana cikin wurare da ke fama da matsalar tsaro tsawon lokaci lamarin sai ya yi sauƙi ya sake ta’azzara.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda jiha DSP Ahmad Rufa’i duk ƙoƙarin jin ta bakinsa lamarin ya faskara domin ba ya kusa ga waya a lokacin kiransa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here