Home Siyasa INEC Za Ta Bi Dokar Kotu Kan Takarar Atiku a 2027

INEC Za Ta Bi Dokar Kotu Kan Takarar Atiku a 2027

18
0

INEC TA CE ZA TA BI DUK WANI HUKUNCIN KOTU KAN CANCANTAR ATIKU A ZAƁEN 2027

Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya ce hukumar za ta bi duk hukuncin da kotu ta yanke kan cancantar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, na tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Kamar yadda Jaridar TheCable da Punch suka ruwaito, Amupitan ya bayyana cewa INEC ba za ta yi watsi da hukuncin kotu ba, kuma duk matakin da za ta ɗauka zai dogara ne kan takardun hukuncin da kuma shawarwarin lauyoyinta.

Wannan na zuwa ne bayan wata Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke tsarin shugabancin kwamitin riƙon ƙwarya na ADC ƙarƙashin jagorancin David Mark, tare da soke wasu matakan da kwamitin ya ɗauka, ciki har da zaɓen fidda gwani da ya samar da Atiku a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.

Sai dai a ranar 12 ga Nuwamba, lauyan ADC ya bayyana cewa hukuncin kotun bai soke takarar Atiku kai tsaye ba, yayin da jam’iyyar ta ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin.

A gefe guda, Amupitan ya ce har yanzu INEC tana jiran samun kwafin hukuncin kotun da aka tabbatar da sahihancinsa kafin ta yanke matsaya kan batun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here