Ɗan takarar shugaban Nijeriya na jam’iyyar, ADC, Atiku Abubakar, ya soki yunkurin gwamnatin Tinubu na neman bashin Dala miliyan 500 daga Bankin Duniya.
A cikin wata sanarwa da daraktan sadarwa na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na ADC, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce, babu wani shugaban ƙasa mai barin gado da ke da haƙƙin dora wa wanda zai gaje shi sabon nauyin bashi kwanaki kadan kafin miƙa mulki.




