Zababben gwamnan Sakkwato Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto ya aminta da nadin Malam Abubakar Bawa a matsayin sakataren hulda da ‘yan jarida a fadar gwamnatin jihar Sokoto.
Bayanin na kunshe ne a wata takarda da sakataren babban kwamitin karbar mulki na jamiyyar APC Ibrahim Dadi Adare ya rattabawwa hannu.
Zababben gwamnan ya taya murna ga sabon sakataren, ya kuma bukace shi da yayi amfani da kwarewar da yake da ita wajen ganin cewa an yayata shiraruwa da kuma tsare-tsaren gwamnati ga jama’ar jiha da wajenta.
Sanarwar ta ce wannan nadin dai ya soma nan take. Nadin da aka yi wanda shi ne na farko a gwamnatin da ake saran farwarta aranar Litinin mai zuwa.





