Home Daga Marubutanmu RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 22

RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 22

21
0

NA

Ruƙayya Ibrahim Lawal (Ummu Intisar)

PP 22

Har a wannan lokacin ba ta saurarawa shan magungunan da yake nemo mata ba saboda shi ne ma mai ƙoƙarin sayen magungunan ko da mama ta labartawa Abban nasu labarin matsalar Surayyah da ta ji daga bakinta da shedu a gun Ahmad kasa amincewa ya yi ya ce shi
‘yarsa qlau take lokacin aurenta ne bai yi ba a daina mannawa bayin Allah sharri.

Da maman ta matsa da zancen ya amince musu a kan neman magani amma fa ya tabbatar musu ƙwandalarsa ba za ta yi ciwo ba a wurin magance matsalar labarin ƙanzon kurege.

Dalilin magungunan hayaƙi da take amfani da su ya saka dole suka raba shimfida da Minal ta fara kwana a ɗakin Innare ga ma lokacin kwanciyar bazara ya shige an fara ruwan damana.

Wasu watanni biyu suka sake shuɗewa shiru Ahmad bai tada zancen ba ya ma ɗauke ƙafarsa daga gidansu ya kuma rage nemanta a waya, idan ta tambayi dalili sai ya ce ayyuka ne suka yi sha kansa.

Watarana da ta zame mata baƙar rana a cikin ranakun tarihin rayuwarta ita ce ranar da ta tayarwa Ahmad zancen baikonsu a ranar da ta gan shi kwatsam ya zo hira da yamma.

Cike da nauyin zuciya da na harshe ya furta mata kalmar “Ki yi haƙuri Surayyah Allah ya gani ina matuƙar ƙaunarki amma…”

Kasa ƙarasawa ya yi ya ɓame bakinsa tare da juyawa ya shige motarsa ya tada ita bai ma ba ta damar yin tambaya.

A yanayin yadda ta ga fuskarsa da juyawar da ya yi ya tafi ya sanyayar mata da jiki matuƙa, karaya ta yi mata saukar bazata a cikin zuciya.

‘Yanzu shi kenan shi ma Ahmad na rasa shi? Ko dai ba ni da rabon yin aure ne a rayuwa?’ Tambaya ta ƙarshe da ta ziyarto ta ta ƙara karya mata ɗan sauran ƙwarin gwuiwar da ya rage mata ta shige cikin gidan fuskarta shaɓe-shaɓe da hawayen da suka kasa tsayuwa.

Ga shi a wunin ranar ba kowa a gidan sai ita kaɗai kasancewar mama da Aishatu sun je wuni gidan family nasu maman, ‘yar ƙaramin ƙaninsu ce ta haihu shi ne ake taron suna ta tabbatar kuma ba za su dawo ba sai dare.

Ɗaki ta shige can uwar ɗaka ta zauna ta rasa me ke yi mata daɗi a duniyar. A da ta yi tunanin za ta iya rabuwa da Ahmad cikin sauƙi, sai a yanzu ta gano ashe abin ba shi da sauƙi kamar yadda ta yi hasashe da fari. Wayarta ta ciro ta tura masa saƙon karta kwana (text message) kamar haka;

Idan ma wasa kake yi mini Ahmad kadaina domin hatsarinta zai iya tarwatsa ƙwaƙwalwata. Ka faɗa mini cewa wasa kake don Allah Ahmad, ina sonka irin son da ban taɓa kwatanta irinsa ga wani ɗa namiji ba a nan duniya.

Ta tura masa sannan ta ajiye wayar a cinyarta ba tare da ta fita daga cikin sunansa ba tana mai ƙura wa wayar ido ba ta ko ƙyaftawa. Tazarar mintuna uku a tsakani sai ga saƙonsa ya shigo ta cafko wayar da duka ƙarfinta ta matso da ita kusa da idanunta.

Rufe idon ta yi ta sake buɗewa tana fatar ganin saƙon ya goge ko kuma ya sauya daga abin da ta karanta daga farko. Ta sake murza idanunta da kyau ta ware su a kan screen ɗin wayar fuskarta na bayyanar da tashin hankali. Da gaske so take ta tantance ko idonta ƙarya ya gane mata, sai dai ga dukkan alamu iya gaskiyar abin da ke rubuce a saƙon zuciyarta ta karanta.

Baki na ɓari ta sake karantawa a fili “Iya gaskiyar kenan na faɗa miki, na yanke wannan hukuncin ne ba don son zuciyata ba sai don hakan ya zama wajibi a gare ni. Ba abin da za ki ƙara sani daga gare ni bayan wannan. Ki yafe mini idan na cutar da ke a tsawon zamanmu.”

Sai a lokacin zuciyarta ta yi ƙoƙarin tunkuɗo nauyin da take ji zuwa waje ta hanyar fashewa da kuka da ta yi, ta yasar da wayar gefe tana ci gaba da rera kuka mai sauti tana sambatun da ba ma ta san tana yi ba.

“Kar ka mini haka Ahmad, ka riga ka yi dashe mai ƙwari a zuciyata wanda ba zan iya tumɓuke shi cikin sauƙi ba. Me ya sa za ka yi haka a lokacin da na gama sakankancewa damuwata ta zo ƙarshe?”

Ta zagaita da zancen saboda kukan da ci ƙarfinta ta ci gaba da rera shi da ƙarfi kafin
ta ɗora sambatun da faɗar

“Idan iyayenka ne suka hana ka aurena ni zan je har gabansu na durƙusa na roƙe su. Idan kuma don matsalar da kake zato a kaina ce ai na samu lafiya. Me ya sa za ka guje ni?”

Yi take tana kallon bango kamar Ahmad ɗin na tsaye a gun. Sosai ta sha kuka a ranar don sai da ta ɓata awa biyu tana yin shi har sai da idanunta suka fara damƙewa.

Ta sha ji ana faɗar kuka yana iya makantar da mutum ba ta yarda ba sai a ranar saboda idonta har ya fara liƙewa ga ta ita kaɗai babu mai rarrashi.

Haƙiƙa tana matuƙar son Ahmad, rayuwar soyyyarsu da irin kulawar da ya ba ta ba za su taɓa goguwa ba a tarihin rayuwarta.

Sai a lokacin ne take ƙara jin zafin gorin rashin aure da ake yi mata, a wannan ranar sai da ta tuna duk wani gori da kunnuwanta suka taɓa tsinkayo mata kuma suka tsaya mata a rai.

Mama kuwa ba su suka dawo gidan ba sai bayan magariba tun daga ƙofar shigowa ciki da ta ga haske ya baje a tsakar gidan ta shigo da fara’arta tana faɗar “Yauwa, Alhamdullillah akwai nepa, yanzu kin ga wanka kawai zan yi na kwanta na sha iska na gaji.” Ta ƙarashe zancen da sauti mai bayyanar da gajiyar da ta ambata.

A’ishatu tana ‘yar dariya ta ce “Kai mama aikin me kika yi? Zaune fa kawai kike abinki kina ba da umurni…”
Ba ta ƙarasa ba idonta ya sauka kan sharar da aka fara ba a ƙarasa ba ta taɓo mama tana nuna mata “Mama kalli aikin mata.”

Mama ta girgiza kai cikin takaici ta nufi cikin ɗakin tana faɗar “Ina ita hamshaƙiyar? Ni tun da muka shigo ma ban ji ɗuriyarta ba kar dai fita ta yi ta bar mini gida a buɗe…”
Bakinta ta yi wa linzami saboda hango Surayyah da ta yi zaune kan kujerar zaman mutum ɗaya da ke fuskantar ƙofar ta kifa kanta.

Tsoro ya bayyana a fuskar maman ta nufe ta don ganin me ya same ta sai dai tana matsowa tana ƙara jiyo sautin ajiyar numfashinta.

ƁANGAREN HALISA

Halisa ta ci gaba da tsayuwa a bayan Igen har ta buɗe ɗakinta ta shige ta bi ta ciki tana jira ta ji ta ba ta amsa a kan abin da ta je ta yo a gidan maman amma shiru ta ƙi tamkata. Ganin hakan ya saka a shagwaɓe ta zagayo daidai inda fuskar Igen take ta tsaya gabanta a shagwaɓe tana faɗar “Ni ki faɗa mini me kika yi wa mamana?”

Haɗe fuska ta yi tana faɗar “Sai na ji shaƙa da maƙura zan faɗa. Yau ga yarinyar kawai, ina ƙoƙarin ƙwatar miki ‘yanci kina hauka, to idan kin damu da jin me ya faru ai kin san ƙofar gyatumar taki kya iya zuwa ki tambayo ko ma ki kira ta a waya.”

Cikin ƙunƙuni Halisa ta juya za ta bar ɗakin tana faɗar “Tab! So kike ta san ina da waya ta kusa kashe ni? Ni dai ba a kyauta mini ba ehe…”

Tana ƙoƙarin fita daga ɗakin kenan ta jiyo faɗowar mutane cikin gidan faram-faram, sai a lokacin ma ta tuna abin da ta aikata a waje ta koma ciki da hanzari fitsarin da take ƙoƙarin riƙewa yana neman ƙwace mata, da ma shi za ta je yi ta ci karo da su. Ta laɓe a bayan Igen tana leƙe ta gefe.

Igen ce ta cire hannun Halisa daga cumuimuyetan da ta yi ta baya tana faɗar “Ke ni sake ni kin wani damuƙe ni haka kamar wacce ta ga abin tsoro…”

Ba ta ƙarasa zancen ba ta jiyo muryar mace a tsakar gidan cikin ƙaraji tana faɗar “Tana ina mahaukaciyar? Yau za ki san kin taɓo tsuliyar dodo. Yaron nawa ɗaya jàl kamar rai shi kika nakasta?”

Igen ce ta yo gaba cikin mamaki tana kallon Talatu da ke ta faman cira da ɗaga murya. Halisa na ganin hakan ta sake ƙugun kakar a ɗari ta shige ƙarƙashin gado ta ɓuya domin a ɗabi’a ita kura ce ga tsoro ga ban tsoro.

Igen ta ƙarasa inda Talatun ke tsaye tana jijjiga ƙafa “Wai me ya faru haka Talatu kika shigo mini ba ko sallama kina ta faman masifa?”

“Au! Mahaukaciyar jikar taki ba ta sanar miki abin da ta aikatawa yarona ba?”

Yatsa Ige ta ɗaga tana girgiza shi da faɗar “Kul kar ki ƙara zagin ‘yar cakwaina domin za ki ji ba daɗina ke dai ki faɗi abin da ya kawo ki ahto!.”

Duk da a hasale Talatun take amma a haka ta kwashe komai da ya faru a yadda ta ji labari gun waɗanda ke kusa da wurin da abun ya faru ta faɗawa Ige.

“Yanzu ina yaron?” Ige ta tambaya a gajarce.

“An tafi da shi asibiti ko ganinsa ma ban samu yi ba, ta nan na faro in ji dalili kafin in wuce can.”

“Ina zuwa.” Ige ta faɗa tana shigewa cikin ɗakin da ƙafafuwanta da suke harɗewa wani zubin idan tana tafiya. Can bayan mintuna biyu ta fito da kuɗi ‘yan dubu-dubu guda biyar ta miƙawa Talatu tana faɗar “Karɓi wannan ki je a saya masa magani, amma kar in ji kin taɓa mini jika don kuwa hukuma ce za ta raba mu.”

Cike da jin haushi Talatu ta bi kuɗin da kallon wulaƙanci ta fita tana mitar ita lafiyar yaronta ta fi mata kuɗi kuma ita ba mayyarsu ba ce don ta fi ƙarfin dubu biyar dai. Kuma Igen ta jira ta ga me zai biyo baya har tana ƙarawa da furucin “In sha Allahu sai Halisa ta tagayyara a rayuwa kamar yadda take jefa mutane a wahala.”

Daga wannan maganganun ta fice ta bar tsohuwar tsaye a gun tana kumfar baki.

Al’amarin Halisa dai tun bayan da Al’amin ya sauke ta a mashin ya juya bai sake waiwayo rayuwarta ba gaba ɗaya saboda ya tsorata da al’amurranta.

Da fari ya so ya sake nemanta ya jarraba ko zai iya jure zama da ita, to amma ko da shi ya iya yin hakan ya tabbatar iyayensa ba za su jure ba wannan dalilin ya sa ya tilastawa zuciyarsa haƙura da ita domin Hausawa suna cewa maganin kar a yi kar a soma.

Tafiyarsa sai ya zamana kamar ya dakatar da dukan samari daga waiwayarta duk kuwa da tarin farinjinin da take da shi.

Ko kaɗan wani bai sake tare ta ko ya turo ko ta ji labarin saƙon soyayyarsa ba, ga ragowar maƙalallen son Hayat da ya ƙi ficewa daga zuciyarta a haka ta shafe shekaru biyu shiru. Tun ba ta damuwa har ta fara saka damuwa a ranta duk da dai tun a shekarar farko ta rabuwarsu ta watsar da batun Hayat ta kama karatunta na boko gadan-gadan shi take ba dare ba rana. A haka har aka shiga shekara ta ukun.

Sai dai abin da Halisa ba ta sani ba shi ne mazaje da yawa suna son kawo mata caffa amma tun daga ƙofa ake tare su a sanar da su halayenta da na kakarta, waɗanda kuma suka kasance ‘yan unguwar ko da sun nuna ra’ayinta iyayensu ke dakatar da su da furucin ba za a gurɓata musu zuri’a da auren taɓararriya irin ta ba.

A washe garin rana ta biyu ga babbar sallah da ranar da an Sakkwatawa suke yi wa laƙabi da Ranar Rabo, a wannan ranar Allah ya yi abin da yake binne a cikin ƙasa zai tsiro a gan shi.

Akwai wata mata a can bayan layinsu ana kiranta da Rabi bakinki ka ja miki, suna mutunci sosai da Ige domin ita Rabin ƙawa ce a wurin Mariya ‘ya mace tilo da Igen ta haifa.
Wannan dalilin ya saka ta wanko ƙafafunta ta zo yi wa innar tasu barka da sallah, shigowarta kedawuya sai ga Mariyar kamar haɗin baki. Sun ji daɗin haɗuwa da juna suka zauna aka ɓarke da hirar yaushe gamo, Ige ta zubo musu soyayyen naman rago da sarakananta suka gyaro mata shi aka aiko mata, ta dire musu farantin da ta kusa cikowa a gabansu. Halisa ta sayo musu fiyawota suna ci suna zuba zance a nan ne garɗin nama ya ratsa Rabi ta buɗi baki ta ce “Kai duniya ba amana Mariya! Ke dai ki ga mutum…
Yanzu a ce wai Tukur ne zai shiga ya fita yana kore manema auren Halisa ai…”

Sai a lokacin ta ankara da katoɓarar da ta aikata ta rufe bakinta da tafin hannu ta yi tsuru-tsuru kamar wacce ta yi gulmar sarki a kunnen faɗawa.

“Ya kika yi shiru Rabi? Ƙarasa mana, Tukur dai wannan namu na cikin gida?”

Ta yi furucin da maɗaukakin mamaki tana nuna hanyar sashen gidan gandun nasu.

Rabi ba ta da zaɓin da ya zarce ta ƙarasa ɓarnar da ta fara don haka ta gyaɗa kai alamar eh jiki a mace.

Ai kuwa sai ganin Ige suka yi kamar an jefo ta daga sama ta tsaya a gaban shimfiɗarsu da ke ƙofar ɗakin tana faɗar “Rabi yi mini dallah-dallah, me Tukur ɗin ya je yana faɗa a kan ‘yar cakwaina?”

Jiki a sanyaye ta fara magana “Ni ma a gun Maigidana na ji labarin sanda ya shigo yana mitar Tukur ba shi da kirki bai taɓa ganin butulallen bawa irinsa ba. A nan na tambaye shi me ya faru ya labarta mini wai ko zuwa neman auren farko da aka yi na Halisa shi ne ya tare iyayen yaron ya shirya musu ƙarya da gaskiya a kan ‘yar yayan nasa.
Haka ko baya-bayan nan da ya ji ƙishin-ƙishin wani na ƙaunarta zai zaga ya je har unguwarsu yaron gun iyayensa ya shirya musu zantukan ɓatanci har ƙazafi ya yi mata wai gantalalliya ce barbaɗaɗɗiya a cikin maza take zama su ne abokananta.

Har yara gare shi da yake bazawa suna saka masa ido a kanta su suke kawo masa rahoto da zarar ta yi sabon saurayi ko sun ji labarin mai sonta.”

Ige ta matuƙar fusata da jin wannan labarin ta juya jikinta na kakkarwa za ta fice Mariya ta yi saurin tare ta tana mata magiya “Don Allah Inna kar ki ce za ki je wurinsa da maganar nan ko ba yanzu ba. Ke uwa ce a gare mu duka bai kamata ki yi hakan ba, ki bar shi da halinsa in sha Allahu aniyarsa kansa za ta koma. Idan kika bari ya san kin san da wannan abun zai canza taku ne, haka shi maƙiyi yake.”

Cak Igen ta ƙame kamar wacce zancen ya shige ta da gaske sai ajiyar numfashi take saukewa cike da mamaki.

“Haba Mariya ai ke kin san komai, me yarinyar ta tsare masa? Miye Halilu bai yi masa ba a rayuwar nan? Sana’ar da yake taƙama da ita ma Halilun ne ya koya masa ya kuma ba shi jari amma da wannan zai saka masa? Tilon ‘yar tasa mace da ya bari wacce yake ƙauna sama da komai ita zai lalatawa suna a gari?”

Girgiza kai Mariya ta yi cikin alhini ta ce

“Na san komai Inna amma don Allah ki yi haƙuri ki koma ki zauna.”

Ige ba ta sake magana ba ta ja malgwaɗaɗɗin kafafuwanta da suka fara juyewa kaɗan ta koma cikin ɗaki ta yi shiru.

UMMU INTISAR CE

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here