Home Siyasa Ɗaukar kofin Talauci: ADC ta yi martani mai zafi ga Gwamnatin Kebbi

Ɗaukar kofin Talauci: ADC ta yi martani mai zafi ga Gwamnatin Kebbi

3
0


Ɗaukar kofin Talauci a tsakanin jihohin Nijeriya: ADC ta yi martani mai zafi ga Gwamnatin Kebbi

Jam’iyyar ADC a  Kebbi, ta bayyana matukar takaicinta kan martanin gwamnatin Jihar Kebbi game da rahoton talauci da aka danganta da Hukumar  cigaba ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP), inda gwamnatin ta fi mayar da hankali wajen sukar dan takarar gwamnan ADC, Alhaji Abubakar Cika Malami, madadin gabatar da kwararrun hujjoji da za su karyata rahoton ko ta bayyana matakan da take dauka domin rage radadin talauci a jihar.
ADC ta bayyana cewa abin kunya ne gwamnati ta mayar da rahoton da ya shafi halin rayuwar al’ummarta zuwa rikicin siyasa, kamata ya yi  ta dauke shi a matsayin kira na gaggawa ga shugabanci nagari da kuma neman mafita ga matsalolin talakawa.
A bayanin da mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyar a jiha Injiniya Abubakar Atiku Musa ya rabawa manema labarai ya ce  idan gwamnati tana ganin rahoton bai dace ba, me ya hana ta kalubalanci masu binciken da hukumar da ta fitar da shi da sahihan bayanai da hujjoji? “Me ya sa aka mayar da martani ga Abubakar Cika Malami, SAN, alhali ba shi ne ya gudanar da binciken ko ya fitar da alkaluman ba?
“Shin laifin dan takarar ADC ne idan rahoton ya nuna cewa al’ummar Kebbi na fama da talauci? Ko kuwa laifin wadanda suka bayyana matsalar ne, ko kuma gazawar shugabanci wajen magance matsalolin jama’a ce ya kamata a tattauna a kai?
“Jam’iyyar ta jaddada cewa ba ta musanta  gwamnati ta gudanar da wasu ayyukan raya kasa ba, amma gina tituna, sayen motocin tsaro ko aiwatar da wasu ayyuka ba su isa su zama hujjar cewa an magance talauci ba. Abin da talaka yake bukata shi ne abinci a gidansa, aikin yi, ruwan sha, ingantaccen ilimi, kiwon lafiya da damar rayuwa cikin mutunci(samar da tsaro), a kalaman”

GWAMNATI TA JI TSORON ALLAH, TA DUBA HALIN DA TALAKAWA KE CIKI!
ADC ta tambayi gwamnatin Jihar Kebbi ko ba ta san halin kuncin rayuwa da jama’a ke ciki ba, musamman matsalolin tsadar abinci, rashin aikin yi da wahalar samun abubuwan more rayuwa.
“Shin gwamnatin APC ba ta san koke-koken da wasu daga cikin mambobinta da shugabanninta ke yi game da halin rayuwa ba? An ruwaito cewa wasu shugabannin APC a karamar hukumar Jega sun bayyana damuwarsu kan matsalar talauci. Idan har irin wadannan koke-koke suna fitowa daga cikin jam’iyyar da ke mulki, me za a ce game da talakawan da ba su da wata dama ta kai kukansu ga gwamnati?
“Talauci bai san  jam’iyya ba, ba ya bambance dan APC da dan ADC. Yunwa ba ta tambayar jam’iyyar da mutum yake goyon baya kafin ta shiga gidansa. Saboda haka, bai kamata a mayar da wahalar talakawa abin kare martabar siyasa ba.”
ADC ta yi kira ga Gwamna Nasir Idris da gwamnatin APC da su ji tsoron Allah wajen sauke nauyin da ke kansu na kula da rayuka, dukiyoyi da jin dadin al’ummar Jihar Kebbi. Mulki amanar jama’a ne, kuma duk wanda aka dora wa wannan amana yana da nauyin yin adalci, sauraron koke-koken al’umma da daukar matakan da za su inganta rayuwarsu.
BA MAGANGANUN SIYASA MUKAKE BUKATA BA, SAKAMAKON AIKI MUKE SO!
ADC ta bukaci gwamnatin Jihar Kebbi da ta daina mayar da hankali kan martani ga ‘yan adawa, ta fito fili ta bayyana alkaluman da za su nuna yadda talauci ya ragu, yawan mutanen da shirye-shiryenta suka fitar daga kangin talauci da kuma irin sauyin da talakawa suka samu a rayuwarsu.
“Idan gwamnati tana da hujjar cewa rahoton UNDP bai nuna ainihin halin da ake ciki ba, ta gabatar da bayananta domin jama’a su tantance. Amma karyata rahoto ba tare da gabatar da sahihan hujjoji ba, ko mayar da martani ga masu magana kan talauci, ba zai ciyar da al’ummar Kebbi gaba ba.”
Jam’iyyar ta jaddada cewa abin da jama’a suke bukata shi ne gwamnati mai tausaya musu, da sauraron kukansu da  samar da hanyoyin dogaro da kai, da kuma tabbatar da cewa kudaden jama’a suna haifar da ci gaba mai amfani ga rayuwarsu.
SAKON ADC GA GWAMNATIN KEBBI
ADC ta yi kira ga Gwamna Nasir Idris da ya mayar da hankali kan ayyukan da suka rataya a wuyansa, ya fifita bukatun talakawa a kan rigingimun siyasa, ya kuma dauki matakan gaggawa wajen magance matsalolin talauci, rashin aikin yi da rashin isassun muhimman abubuwan more rayuwa.
“Gaskiyar magana ita ce: Nasarar gwamnati ba ta tabbata da yawan kalaman kare kai, sai dai da irin sauyin da talaka yake gani a rayuwarsa. “Ba a zaben gwamnati domin ta yi gardama da masu sukarta; an zabe ta ne domin ta yi aiki, ta yi adalci, ta kuma sauke nauyin da ke kanta.
“Muna kira ga gwamnatin Jihar Kebbi da ta tuna cewa mulki na wucin gadi ne, amma amana da aka ba shugabanni nauyi ne da za a yi musu hisabi a kansa. Saboda haka, muna kira gare ta da ta ji tsoron Allah, ta yi wa talakawan Kebbi aiki da gaskiya da adalci, domin su ne suka ba ta amanar shugabanci.
“Talakawan Kebbi ba sa bukatar gwamnati da za ta karyata matsalolinsu; suna bukatar gwamnati da za ta magance su. Ba sa bukatar kalaman siyasa; suna bukatar abinci, aiki, ruwa, ilimi, lafiya da tsaro. Wannan shi ne hakkin jama’a, kuma sauke wannan nauyi shi ne babban aikin kowace gwamnati.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here