Home Uncategorized El-rufa’i ya maka ICPC kotu kan ta hana masa ganin iyalansa

El-rufa’i ya maka ICPC kotu kan ta hana masa ganin iyalansa

21
0

El-Rufa’i ya maka ICPC ƙara a kotu, ya nemi diyyar Bilyan N10bn kan hana iyalansa ganinsa

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya maka Hukumar ICPC ƙara a gaban kotu, yana zargin hukumar da hana iyalansa da lauyoyinsa damar ganinsa yayin da yake tsare.

El-Rufa’i ya nemi kotu ta umarci ICPC ta bai wa iyalansa da lauyoyinsa damar ganinsa, tare da neman diyya ta Naira biliyan 10 kan abin da ya ce tauye masa haƙƙinsa ne.

Lamarin ya ƙara jawo hankali kan tsare tsohon gwamnan da kuma binciken da hukumar ke gudanarwa a kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here