‘Yan sanda a jihar Kebbi sun kama wasu mutum biyu da ake zargi suna da alaƙa da yin garkuwa da wasu sabbin sojoji da ba su daɗe da soma aiki ba a hanyar Anka zuwa Bukuyum a Zamfara.
Waɗanda ake zargin Abubakar Mallan Abubakar dake ƙauyen Gargam, Bagega, a Anka, Zamfara da Usman Muhammadu a garin Ajera, Ilorin, jihar Kwara, an kama su shekaranjiya Assabar a wani samame bayan samu ingantattun bayanai.
A binciken da ake gudanarwa ɗaya daga cikin wanda ake zargi ya ba da bayanin yanda suka yi garkuwa da sojojin uku a hanyar Kwanar Mayanchi, da wani Kabiru Hassan Riɓah da wasu mutum biyu daga Zuru, amma dukkansu sun koma ga iyalansu.
Rundunar ‘yan sanda tana cigaba da bincike kafin ɗaukar mataki na gaba.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Umar M. Haɗeja ya yabawa jami’an da suka yi ƙwazon tare da ba da tabbacin zaƙulo sauran masu laifi a lamarin.





