Home Rahoto Lauyoyi a Kwara sun fara yajin aiki don gwamnati ta hana masu...

Lauyoyi a Kwara sun fara yajin aiki don gwamnati ta hana masu Alawus

11
0

Lauyoyin Gwamnati a Jihar Kwara sun fara yajin aiki na sai baba-ta-gani akan rashin biyan su alawus

Lauyoyin da ke aiki a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kwara sun fara yajin aiki na sai baba-ta-gani saboda zargin rashin biyan wasu alawus da su ke bin gwamnati, tare da neman daidaita albashi da sauran hakkokinsu da na alkalan kotunan majistare a jihar.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa kungiyar lauyoyi ta kasa, wato Law Officers Association of Nigeria (LOAN) reshen Jihar Kwara ce ta sanar da fara yajin aikin, inda ta umarci mambobinta su dakatar da duk wani aiki a hukumance har sai gwamnati ta biya bukatunsu.

Shugaban riko na kungiyar, Kehinde Ayorinde, ya ce yajin aikin zai ci gaba har sai gwamnatin jihar ta dauki matakin warware matsalolin da suka gabatar.

Kungiyar ta bayyana cewa tana neman a biya mambobinta ragowar alawus na kayan daki na shekarar 2020, da kuma alawus na rigar aiki na shekarun 2024, 2025 da 2026. Haka kuma tana bukatar a aiwatar da daidaita albashi da sauran sharuddan aiki na lauyoyin gwamnati da na alkalan kotunan majistare.

A cewar kungiyar, matakan da ta dauka sun biyo bayan karewar wa’adin kwanaki bakwai da ta bai wa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq domin magance matsalolin, amma ba a samu biyan bukata ba. Ta kuma ce duk kokarin da aka yi na tattaunawa da gwamnati bai haifar da sakamako ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here