Home Rahoto An Kama Jami’in Soja kan zargin Safarar Tabar wiwi

An Kama Jami’in Soja kan zargin Safarar Tabar wiwi

15
0

Rundunar ’yan sanda ta kama wani jami’in Sojan Ruwa na Najeriya mai mukamin Lieutenant, Lt. James Emmanuel, tare da wani mutum mai suna Felix Dickson, bisa zargin safarar tabar wiwi.

An kama su a cikin wata motar Toyota Tacoma Hilux mai ɗauke da siren, inda jami’an suka gano kunshin tabar wiwi 248 da aka sanya cikin jakunkunan Ghana Must Go guda biyar.

Rahotanni sun ce mutanen biyu sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa kuma suna hannun ’yan sanda domin cigaba da bincike.

Daga Datti Assalafiy

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here