Malamin addinin musulunci Shaikh Musa Ayuba Lukuwa ya tsallake rijiya da baya a yayin da wani matashi ya yi yinƙurin hallakashi bayan kammala sallar Jumu’a a masallacinsa, lokacin da yake gaisawa da mabiyansa.
Matashin wanda ya tafi sallah a masallacin domin ya ga bayan malamin ya fito da yuƙa doguwa in da ya yanka masa a wuya kafin mutane su farmasa da duka har suka kashe shi matashin.
Wani shedun gani da ido ya faɗawa waƙilinmu cewa ‘a gaba na komai ya faru shi Malam(Musa Lukuwa) yana da al’adar bayan kammala sallah ya gaisa da mutane kafin ya shiga gida a haka da yake yi yana gaisawa da mutane sai ya zo gaban yaron bayan ya ba da baya ya zaro wata doguwar yuƙa kamar zarto ya yanke shi a maƙoshi an yi nasara yuƙar ba ta shiga sosai ba.
“Da mutane suka ga abin da yaron ya aikata anan suka dirar masa da duka har sai da ya daina motsi da suka tabbatar ransa ya fita, nan almajiran na Lukuwa suka yi yunkurin ƙona shi da wuta amma wasu suka hana,” kalaman majiyar.
A lokacin da Aminiya ta isa wurin ta samu an tafi da Sheikh Lukuwa Asibiti domin duba raunin da ya samu don yi masa magani.
Jami’an ‘yan sanda da motoci sama da biyar sun isa masallacin in da suka kwantar da tarzoma tare da ɗaukar gawar matashin zuwa asibiti.
Zuwa yanzu an sanya jami’an ‘yan sandan Mopol a masallacin domin ganin an hana ɓarkewar kowane tashin hankali a masallacin.
Hukumar ‘yan sandan jihar Sakkwato ta tabbatar da faruwar hatsaniya da ta yi sanadiyar kashe matashi a jihar ta yi kira mutane su zauna lafiya domin samun lumana.
A bayanin da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar DSP Ahmad Rufa’i ya sanyawa hannu aka baiwa manema labarai a Jumu’a ya ce “da ƙarfe 1:50 mun samu labarin wani matashi ya kai farmaki masallaci Lukuwa, binciken ya nuna ya shiga masallaci ya kai hari ga Malam Lukuwa bayan kammala sallar Jumu’a.”
Ya ce matashin ya yi amfani da yuƙa ya daɓa a gefen wuya na hagu, anan take wasu suka far masa kafin jami’an tsaro su zo sun salwantar da rayuwarsa.
An dauki gawar margayin zuwa asibiti in da aka tabbatar da rasa ransa ta hanyar bayanin likita.
Malam Musa Lukuwa an tafi da shi asibitin ƙwararru ta jiha in da aka ba shi kulawa a ƙarshe aka mayar da shi gida.
Mutane a jihar sun yi tir da ɗaukar doka a hannu sun yi kira ga mutane su rungumi zaman lafiya da gujewa yin ramuwar gayya.
Kwamishinan ‘yan sanda CP Hayatu Hassan Shaffa ya roƙi mutanen jiha su zauna lafiya jami’an tsaro za su gudanar da bincike kan lamarin, kuma za a hukunta masu laifi.
An tura jami’an tsaro a yankin don dawo da doka da oda ya unguwar da lamarin ya faru ta Mabera.
Shaikh Musa Ayuba Lukuwa ya samu rashin fahimta tsakaninsa da mafiyawan mutanen jihar Sakkwato musamman mabiya ɗariƙar Tijjaniya da Ƙadiriyya tun bayan da ya karanta da fassara hadisi da cewa iyayen Annabin Rahama suna wuta.
Daga haka aka yi ta samun musayar kalamai a tsakanin bangarorin biyu, har wasu matasan malamai suka rubuta masa takardar neman zama da shi(muƙabala) domin suna ganin bai fahimci hadisin ba ne kuma abin ya yi cin zarafi ne ga Annabi.
Lukuwa bai karɓa tayinsu ba amma ya ayyana wasu malamai da su yake son zama a yi karatu in sun aminta.
Ana haka wani Matashi da ake kira Mai Barewa ya fitar da bayani a kafar sada zumunta ta zamani cewa ya yi alwashin sai ya kashe Musu Lukuwa duk in da ya gansa.
Da Malam Musa da almajiransa suka ga haka sai suka yi ƙorafi ga jami’an tsaro da gwamnatin Sakkwato kan wannan matashi in da jami’an tsaro suka kama shi kan yunƙurinsa wanda ya saɓa doka, aka gabatar da shi kotu, bayan da kotu ta ƙi ba da shi beli ne sai wasu matasa suka yi zanga-zanga tare da ƙona tayoyi kan lamarin daga baya jami’an tsaro suka shawo kan hatsaniyar da ta so tashi a manyan titunan Sakkwato.
Kwana biyu da haka a Laraba data gabata ƙungiyon addini suka kai ƙorafinsu a fadar gwamnatin jiha da fadar sarkin musulmi in da Khalifa Muslim Adamu Gobir ya yi magana da manema labarai bayan miƙa koken “ƙungiyoyin addini ne gaba ɗaya da suka shafi Ƙadiriyya da Tijjaniya da Da’awa da Sha’irrai da Jama’atu da sauransu, muka kai saƙonmu ga Sarkin Musulmi da Gwamnatin Sakkwato kan manufar wani malami da yake furta kalamai da ba su da daɗi ga janibin manzon Allah(S.A.W).
“Hankalin mutane a Sakkwato ya tashi gudun kar a bari matsala ta ɓarke a cikin gari suka kawo koke ga a fadar sarkin musulmi da Gwamnatin Sakkwato domin a ɗauki mataki.”
Barista Sani Abubakar Madawaki a madadin tsangayar malamai ya ce kalaman da malamin ke yi ɓatanci ne ga Annabi gudun matsala ake son akai malamin kotu saboda hana mutane su fusata.
Ya yi kira ga mutane kar su ɗauki doka a hannunsu.
A halin da ake ciki akwai fargaba da tsoron tashin hankali a jihar Sakkwato duk da jami’an tsaro suna kan ƙoƙarin ganin hankali ya kwanta bayan samun wannan hatsaniyar.
Amma da yawan mutane a jiha suna dakon matakin da gwamnatin Sakkwato za ta ɗauka kan lamarin ganin lamarin ya shafi addini.






