Home Siyasa NDC ta miƙa wa yankin Kudu tikitin shugaban ƙasa na 2027 don...

NDC ta miƙa wa yankin Kudu tikitin shugaban ƙasa na 2027 don yin wa’adi ɗaya

10
0

Jam’iyyar NDC ta ayyana cewa tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027 zai koma yankin Kudancin Najeriya domin wa’adi guda na shekaru huɗu.

Jaridar Tribune ta rawaito cewa, an cimma matsayar ne a babban taron ƙasa na jam’iyyar bayan ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Ogbaru ta jihar Anambra, Afam Victor Ogene, ya gabatar da ƙudirin wanda wakilan jam’iyyar suka amince da shi.

Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa bayan kammala wa’adin shekaru huɗu, tikitin shugaban ƙasa zai koma yankin Arewa kai tsaye.

Wannan mataki ya buɗe hanya ga tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, da sauran masu neman takara daga Kudu domin sayen fom ɗin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.

Rahotanni sun ce matakin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da sauya sheƙa da haɗa ƙarfi tsakanin manyan ‘yan siyasa gabanin zaɓen 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here