Gwamnatin Tarayya ta haramta wa masu samun digirin girmamawa (Honorary degree) amfani da taken “Dr” a gaban sunayensu a kowace irin mu’amala.
Ministan Ilimi, Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a Abuja, tare da cewa amfani da wannan take daga irin wadannan mutane ya zama bata suna ko karya game da cancantar ilimi, wanda daga yanzu za a rika daukarsa a matsayin zamba ta ilimi, tare da daukar mataki na doka ga duk wadanda suka yi kunnen kashi.






