KANA NAKA..!
Wattpad:JamilaUmar315
Mallakar:Janafty
Arewabook:Jamilaumarjanafty
🅿️19
Saboda Zumud’i ko fargaba zan ce, sai wajen uku saura na dare na iya samun, barci kuma cikin ikon Allah Kasala da nauyin jiki sun kasa barina na tashi na dauro alwala.
nayi salollin Nafila sai dai ina daga kwancen ban daina Hailala da ambaton Allah akan dukkan lamurana ba.
Washegari kamar yadda na saba tashi da wuri haka na tashi, na shirya yara na sama musu abun kari. sukaci sakamakon sun saba tafiya ba abinci,yau din ma haka suka tafi sai dai kamar yadda na sabar musu sai sunci sun koshi suke tafiya yadda kafin yunwa ta jigatasu, lokacin sun dawo gida sai na ba ma kowannen su Goran ruwan faro guda d’aya sun tafi da shi koda bukatar shan ruwan ya taso musu.
Suna tafiya nima ban zauna ba, na fara shiri falo kawai na gyara Dakin yara kuma nace sai na dawo nayi wankana na shirya kaina shima Ahmad na shiryasa bayan na Dama mai kokon sa. na duramai a wani karamin jug,Sauri sauri nake yin komai kada farkon fari kuma nayi latti na samu Tsoffin littafan su Amir da suka gama amfani da shi na Dauka da pencil saboda rubutu duk da ban iya Turanci ba, kuma ban iya Hausa ba, ai na iya rubutu da ajami kuma ina iya karantawa shiyasa ban damu ba.
na tabbatar ma kaina duk abunda na Rubuta zan iya ganesa.
Na hada da katin shaidana na goya Ahmad a baya na daukan mai wasu kayan. ko da ya bata na jikinsa na fito Falo Tara saura,naci karo da Yaya Ishaq a falon yana waya kallo d’aya nayi mai ban kara ba,shi kuma ganin kamar tafiya zan yi yasa ya katse wayar Hannunsa,ta gabansa na gifta cikin yanayin mganata nace”Ina kwana..”
Ina fad’in haka na kama hanya zan fice sai ya mike jiya ya kwana yana mamakina sai da yaga abunda nayi yau sannan ya amince da gaske nake yi,sai ya saka baki ya kirani da karfi na Dakata na juyo ina kallonsa kai tsaye yace”Ina kike shirin zuwa..?
Ni kuma sai naga kamar yana batamin Lokaci sai na juya ina fadin”In da na fad’a maka jiya..Ina Sauri ne kada na makara”
Na fada ina jimke dubu d’ayan da na Dauko cikin kayana sun sha ajiya tun Kudin da Yaya Isa ya bani ne Lokacin da ya maidoni gida, Dubu buya kad’ai na Taba ukun suna na nan ina Boye da su, sai da hakan ta faru na Daga hannu nagodema Allah domin zasu yi min amfani.
Kawai sai naga ya sha gabana a matukar fusace cikin d’aga murya yace”Ni kike nuna ma ban isa dake ba Fa’iza..?
Baya naja ina fadin”Ban ce baka isa ba.Sai dai na nuna maka isar taka ce wannan karon, bazata isa a wajena ba ka bani hanya na wuce ina bata Lokacina”
Sai ya tare hanyar ni kuma sai na kasa wucewa cikin Daka tsawa yace”Ki koma nace ba inda zaki je”
Sai nayi wani kayattacen mirmishi takaici na Fahimci in na zauna haka Ishaq zai cigaba da Nakasa rayuwata kamar yadda ya saba to wannan karon ya makaro domin d’an zaki ya riga ya girma.
Sai kawai na kallesa ido cikin ido kafin nace”Sai dai kayi hakuri wannan karon bazan ji mganarka ba.Na fada maka tun Ranar da ka zabi Zainab da Ahalinta sama da ni..Nima Daga wannan ranar na zab’i Rayuwata da ya’yana sama da kai”
Mganganuna sun dake sa sai ya kasa motsi har na raba ta gefensa na wuce abuna,Kafin na fita sai da nayi addu’an fita gida,sannan na karisa gidan Sa’adatu muka gaisa na kwanto mata Ahmad Allah yasa yayi barci ta karbe sa tare da kuninsa tamin Fatan Alheri daganan na fita na samu Adaidaita sai cikin gari.
Makarantar ta yan mata ne zallah suna barayin su sannan mu kuma inda zamu zauna wani babban aji ne, ko da nazo mata sun fara taruwa sai dai ma’aikatan basu riga sun kariso ba,na gaisa da matan dake kusa dani muka zauna jiran su tara da wani abu suka iso,,Rukuni rukuni suka jeramu a layi mun nuna katin shaidarmu sannan suka sanyamu a rukunin da zamu fara koyan abunda ya kawomu.
Ni rukunin girke girken aka sanya ni shi zasu fara koyar damu sai sun gama sai ayi barayin Had’a lemuka da rana ne Rukunin Koyar da Turaren wuta da Had’a Dilka..
Sai na Fahimci da Safe duk abun ci ne zasu koyar damu shiyasa sai suka raba abun,Ni dai ban tsaya kalle kalle ba na saka ido sosai,ina Fahimtar komai masu koya mana Rukunin Farko,Su biyu ne dukkan su mata ne, Daga ganinsu sun san kan aikin su Sanye da Fararen riga da Hula na masu kirkin da muke gani a Kwatin Talabijin.
Ranar farko wainar kwai suka koya mana da miyar gyada mai allayahu,sosai na karu na kuma rubuta sunayen abubuwan da suke fad’amana bamu gane ba,Suna yi suna yi mana bayani yadda zamu fahimta sannan in baka gane ba sai kayi Tambaya komai da komai na girken girken su, sun zo da shi suka kafa karamin Dakin girki a babban D’akin da muke ciki, nayi tambaya in da naga ban gane ba.kuma sun kara yi min bayani suna da Sauki kai matuka da iya mu’amala.
Daman kuma Koyar damu ne aikin su, har kuma mh iya sun kuma tabbatar mana da cewa zamu iya girke girke masu kyau da inganci.bayan an gama dukkanmu muka D’andana mu biyar ne a rukunin Girke girken,muna ta santi saboda yayi dadi sannan da alkawarin in muka koma gida zamu gwada mu gani.
Sai rukuni na biyu Had’a lemuka,Zobo suka fara koya mana Had’ashi,Duk da na iya zobo sai naga nawa shirme ne ashe ga inda ake zobo nan,Ranar anan Rukunin ya kare shima sun bamu mun sha dad’i,Daga karshe sukace in da bamu gane ba mu yi mgana ni dai akwai karambani daman duk abunda ban ji ba sai da na tambaya suka kara gayamin,Ranar farko kawai da fara zuwana naji araina zan iya komai insha Allahu na dawo gida da Farinciki na iske Ishaq baya gidan ban Damu ba daman na fita da key da na ga ya Kulle gidan sai na bude bayan na Biya na Dauko Ahmad.
Ko girki ban yi ba Dakunan kawai na gyara na share, Lokaci yayi na makara ma a rukunin Rana sai d’aya da Rabi na isa har an fara an raba mutane kowa da Rukuninsa sai da na nuna Katina sannan aka kaini Rukuni na,Abu na farko da suka fara koya mana yadda zamu had’a Turaran kamshi na Icce ne ranar shi mukayi har aka tashi,shima in da bamu gane ba suna bamu ikon Tambaya in da kuma zaka manta sai ka Rubuta na dawo gida karfe hudu da Rabi na yammah na biya gidan Sa’adatu na kara dauko Ahmad sallah kawai nayi na shiga kitchen Saboda yan makaranta suna hanyar Dawowa.
Duk da na gaji ammh ban damu in dai aikin wahala ne na saba shi kuma ya zame min jiki,sai da nayi wanka sannan naji dadin jikina Yara suka dawo makaranta da yammah suna ta Tambayan Daadan su nace ya fita bansani ba,ko saboda abun da ya faru ne sai da yaran suka gaji da jiran sa, suka kwanta sannan ya Dawo ina Falo ina Tattara kayan da suka zubar daya shigo nayi mai sannu da zuwa bai amsani ba sannan bai kalleni ba. ya shige bangaransa a raina nace ko nace a banza.
Washegari ma ya rigani fita,Nima ko Lokaci nayi na yi tafiyata kamar jiya,Sai dai na Fahimce zan rika shan wahala in dai ina jeka ka dawo sai na yanke shawaran in mukayi sati uku, zan fara zama achan sai mun gama Rukunin rana sannan zan dawo gida gabadaya kud’ina kada su kare wajen adaidaita na rasa mafita.
Yaya Ishaq kuma tun daga wannan sa’insan tsakanin mu mgana bata kara Hadamu ba, ni dai ina fita Hakkinsa in mun had’u ina gaishesa shine baya amsani duka duka kwana Hud’u yayi ya koma ko sallama bai yi min ba. ganewar ma da nayi bai kwana agidan ba nasan duk tsanaani in dai yana gari to zai kwana agidansa.nima ko na tattarasa na watsar domin da gaske nake yi na zabi Rayuwata da Rayuwar ya’yana sama da tashi Rayuwar.
Na cigaba da zuwa wajen koyon sana’o’i na hankalina kwance kusan indai akace wannan abun shi kad’ai ne Hope din ka da Fatan ka to gabad’aya Tunanin ka da Rayuwarka zaka Dorasa akansa ne,ya kuke gani in hakan ta faru da mace irina da daman jiran mafita take yi..?to kamar misalin nice Domin na maida gabad’aya Hankalina da natsuwata kan abunda nake koya,Shiyasa duk nafi kowa ganewa a Duka Rukunina tun bamu Rufe wata ba Ma’aikatan suke yaba hazakata da Kokarina,Gashi abubuwa Hudu nake koya ammh kwakwalwata tana Daukan abubuwa dadama. sannan ina gane duk abunda aka koya mana.
Muna rufe wata d’aya da Farawa na koma ina zuwa sau d’aya in na tafi sai Hudu nake dawawo saboda in aka tashi Rukunin Safe sai na zauna sai Rukunin yammah Tunda ma’aikatan suna nan suma ka’ida sai Hudu na yammah suma suke tashi, duk abunda muke yi suna daukan komai sannan suna Rubutawa saboda suna turama kungiyar Bayanan komai.
Yau da gobe zara bata bar komai ba kudin hannuna suka kare sai na koma takawa da kafata yara na fita makaranta nake fita da nisa sosai kafin na kai na jigata ammh hakan nake Daurewa na sama kaina yakinin ba wanda ya isa ko ya samu yana kwance, sai da ya fita ya wahala,Muna Hutu Ranar jumma’a duk sati sau Shidda kenan to ranar ne nake samun na gyara gida, har yi ma yara wanki da Sauran aikace aikace ni kaina nasan na Rame saboda wahala.
Badariya sai da muka raba rabin watanninmu sannan tazo gida ranar wata jumma’a muka hadu a bakinta nake jin Anty Binta tazo sau biyu bana gida ta je ta fad’ama Mama sai Fada take,Tana fadamin Maman ta kira Yaya Ishaq din tamai mgana ba’a san me ya fada mata ba,basu kara mganar ba,Badariya tace ita dai tayi gum da bakinta bata tofa ba, tana ji Mama na fad’an na fara gantalin bin gidajen makota.nayi dariya nace gwara da kika yi shuru baki ce musu komai ba.
Araina naji mamaki ban Dauka Yaya Ishaq zai yi Laushi ba ni dai abunda na sani bazan zauna Damar da na Dade ina jiranta ta Kubcemin ba,Bandamu domin ba ta su nake ba ta kaina nake da ni da ya’yana. Badariya taji dadin yadda na fadamata muna koyan abubuwa da Dadama,sannan wahalata ta ragu saboda Sa’adatu ta Daukemin Laluran Ahmad sai abun yazomin da Sauki,Ban gayama kowa ba So nake ko yan Karofi na basu mamaki Fata na da Dakiyata azabeni cikin mutanen goman da za’a basu tallafi saboda zai yi min matukar amfani.
Yadda Yaya Ishaq ya tattarani da ni da ya’yana gefe d’aya.haka nima na tatrarasa na watsar Sai dai ya’yansa ban isa na cire musu tunaninsu akan sa ba,ko bakomai mahaifin su ne,ya zama Dolen su ni kuma ko da yake mijina ai ba Dole na ba ne,Na riga na jigata da tafiyar kasan da nake yi ammh ban ji ko sau d’aya na gaza ba nayi fashi sau Biyu shima Ahmad ne yayi ta zazzabi ba Halin na fita na bar shi kuma zuwa da yara an hana, shiyasa na zauna na Kula da shi har yaji sauki muna gabda cinye wattani ukun mu,Badariya ta dawo wajena da kwana ashe Mama da Anty Binta Abuja sukaje sulhu Zainab ta samu ciki sai suka yi sa’insa da Ishaq akan Farhan bai yi kwari ba, zata zubar da cikin shi kuma ya hana ita kuma sai ta Ture mganarsa ta yi mgana da mahaifinta yace ta zubar, tako je aka markadesa shine rigima ta kai su ga Har Ishaq din ya mari zainab din ai ko Badariya tace Mahaifinta ya Kira Mama yana fadin Ishaq ya gama marin auransa kuma sai yayi mganinsa sai ya yi kararsa a kotu,Ai ba jaka ya aura masa ba.shine Mama ta rud’e ta yi ma Anty Binta mgana ta rakata suka tafi Abuja su sulhunta mganar.
A raina sai nace tun yanzu..? Auran barikin fa kenan,ai na Dauka ko me zainab tayi Yaya Ishaq zai yi hakuri da ita,tunda ita yar so ne kuma ita ya zaba ban dai nuna komai ba nayi fatan Allah ya Daidaita su Saboda ni bazan yi Dariya don haka ta faru ba Namiji ai duk inda yake yana amsa sunan sa na Namiji ne.
Wajen kwananta hud’u a gida na sannan su Mama suka dawo, sai ta koma gida Saboda harkan gabana nake yi yasa ban damu da na Bibiya ya suka kare ba,Nidai bana fatan tun yanzu auran su ya samu matsala ina Fatan su tara kyakyawan zuru’an da Yaya Ishaq yake mafarki da fata ko zai daina kallona a matsayin wacce ta zama Sillar shiga tsakaninsa da mafarkinsa da Burinsa.
Mun cigaba da zuwa muna koyan abubuwan da ake koya mana har ga shi yau da gobe bata bar komai ba zamu kammalah,Watanni uku kamar kwana uku ne a wajen Ubangijinmu,Ranar jumma’a muna Hutu asabar zamu gama gabad’aya ranar Lahadi kuma za’a sallame mu da Takardan shaidar abunda muka koya, a kuma wajen za’a bama wad’anda suka chanchanta tallafi.
Ranar jumma’an ina gida tunda bama zuwa ranar Sai ga Badariya da Raliya sun zo min da labari mai dadi bayan mun gaisa na kawo musu ruwa su Amir suna haraban gida suna waasa.
Raliya ta kalleni tana fadin”Anty Fa’iza ina tayaki Murna kin yi abu mai kyau, Hajiyar mu tana ta fad’amin a duk report din da ake kawo musu a duka Rukunin da kike Dauka kin zama zakara sosai ma’aikatan suke yabawa da kokarin ki”
Sai naji dadi na godema Allah acikin Raina Badariya na gefenta tace”Ai Anty Fa’iza ba daga nan ba Raly ni daman nasan zata iya”
Raliya tace”Haka na fad’a ma Hajiya..Nidai mun zo cin sauyin Sabon girki ne Anty Fa’iza me zamu samu..?
Na mike ina Dariya nace”Daman jiya alalan mai kifi da kwai aka koya mana yau daman ina da niyar gwadawa”
Ihu suka saka gabadayan su Badariya tace”a hada mana har da lemu mai Dadi don Allah”
Sai nace to a raina ammh ina Tunanin ina zan samu kudin kifi da kwai, tunda ina da wake kamar Badariya ta sani taja Raliya suka fita ba jimawa sai ga shi sun dawo da cefane har da kankana da kankara sukace Lemun kankana suke so nan da nan ko na shiga Kirchen na fara aiki suka shigo suna Tayani da hira da d’an taimakon da bazai gagara ba.
Nikan Waken Amir na aika ya kai mana makota muke da gidan nikan, kusa da gidan Habiba ne daman in dai aike ne ko nika kusa haka to Amir nakan aika Tunda ba nisa sosai,cikin awa uku muka gama alalan kwai da kifi na kuma had’a musu lemun kankana nan sukayi sallar mangariba suka zauna suka ci suna santi Raliya tace”Anty Fa’iza in da saura a samin a leda sai na kai ma Hajiyarmu alalan nan taci taji itama”
mirmishi kawai nayi daman na Mudu daya da rabi nayi na Dibar mata da yawa tace kowa sai yaci a gidansu ta karishe da Fadin”Zan miki tallah Anty Fa’iza dole mu bude Fa’iza Kitchen”
Badariya tace”Sosai ai Oder zamu fara yi wannan girki ai ko Hotel ko Restaurant albarka”
Haka suka yi ta zuzuta girkin da zasu tafi mukayi sallama suka tabbatar min da jibi zasu zo tunda taron a babban Hall din makarantar su ta Umaru musa yar’aduwa za’ayi.
Washegari da mukaje gwaji dukkanmu mukayi,Ma’aikatan duka gefe suka koma suka bar mana abunda zasu yi ranar, Kunun gyad’a muka yi bangaran abun sha kuma ni na zama zakaran rukunin mu sai bangaran girki kuma yam ball muka yi ma’ana Fanken doya,shima ni na zama zakara na Rana ma rukunin hada Kolaccha ma ni na Jagoranci Rukunin mu,haka bangaran had’a Dilka da Halawa anan wajen muka mulkama kafafun mu da Hannuwan mu,wasu har da Fuska ni dai ban saka ba,Sannan mun had’a Turaren Humra na ruwa mai kamshi shima muka goga a jikin mu saboda muji yanayin kamshin,Ranar sai Yammah na dawo gida su Amir gidan Sa’adatu suka zauna sai da na dawo.
Ranar Lahadi kuma na fada ma su Amir su yi min addu’a yau zan gama abun da nace musu ina yi suka yi ta cewa Umma Allah ya baki sa’a na amsa da Ameen.
Saboda taron gamawa ne Tare da Ahmad naje bansan makarantar ba, mai adaidaitan ya kaini hall din ba Boyayye ba ne ina zuwa na tambayi inda ake taro wasu yanmata suka nuna min, da wuri naje wasu duk basu zo ba ammh naga wasu daga cikin mu.
Karfe sha d’aya aka fara taron manyan mata masu alaqa da kungiyar duk sun zo ciki har da Hajiyar su Raliya na ganta ba su gayyato yan jarida ba Saboda basa son duniya ta sani su don Allah suka yi,Sai mu kawai da muka samu Horan sai kuma yan’uwan wasu daga ciki da ma’aikatan da aka Dauka suka koyar damu sai yan kallo.
Su Badariya sun zo su da gayyar kawayen su sai dai hannu suka Dagamin, tunda su suna baya mu kuma gaba akace mu jeri mu Talatin din da muka samu Horan.
Bayan jawaban godiya da kuma Fatan alheri ga wannan kungiyar aka gayyaci wata Hajiya Zubadai itace kamar ma’ajin kungiyar reshen Jahar katsina ta fito tayi jawabi akan manufar kungiyar da kuma manufar taron da suka shirya garemu na mata talatin da suka koyar da su sana”o’i goma.
daganan aka bata sunayen mu ta rika kiran mu d’aya bayan d’aya muna karban Takardan shedar abunda muka koya ni ce ta goma acikin wad’anda ta kira Fa’iza sidi karofi. Dayake tana amfani da amsa kuwwa abun mgana, najita na fita Ahmad na goye a bayana ta bani Takardata sai da nayi Hawaye,Ina gani wata ta kusa da ita nayi mata rad’a a kunne ta kalle tace”Fa’iza sidi karofi ko..?
Na jinjina mata kai sai ta bani Hannu muka gaisa cikin kayattacen mirmishinta tace”Weldone Fa”iza”
Duk da ban ji me tace ba nasan yabo ne sai na jinjina mata kai sannan na koma na zauna,ina Duba Takardan Hannuna da Turanci ne sunana kad’ai na iya ganewa aciki,ammh nasan ko a hakan na tsaya na cinma wata gagarumar nasara a rayuwata ba Nakasashe sai Mai nakasar zuciya, sannan akace babu maraya sai Raggo. in ka tashi ka nema bayan ka bama Allah zabi to shi kuma Allah zai saka maka da kyakyawan sakamako.
An cigaba da kiran mu har zuwa ta karshe sannan wata Hajiya laila daga kaduna itace mai rike da mikamin P.R.O na kungiyar ta fito zata bada shedar girmamawa ga wad’anda suka zama zakaru a rukuninsu,Allahu Akbar ban taba zata ba, Ba zato ba Tsammani naji sunana Fa’iza sidi karofi na fita aka bani wani d’an kwalba mai ban sha’awa da sunana ajiki sannan matar ta tsaidani tayi jawabi da turanci sannan tayi da Hausa tana mgana akan cewa ina da Hearing problem, sannan ban yi boko ba.ammh na iya zama ta farko a fanni masu kokari a dukkan abunda na Koya, sannan ta sake bani wani abu nazare a wuya na ta makalamin na Girmamawar na koyi abu hudu masu wahala a acikin wattani Uku,Sai tafi raf raf ta bani Hannu muka gaisa har tana yi ma Ahmad dake bayana wasa ko da na koma na zauna sai na daga hannuwana sama ina fadin”Allah na gode maka..Alhamdullahi ya Allah dukkan wata ni’ima daga gareka ne”
Matan dake kusa dani suna ta min murna ina amsawa bakina har kunni na juya ina hangen su Badariya ta D’agomin hannu na Daga mata kyautan da takardan da aka bani, ita kuma sai ta Dagamin babban yatsanta alamun jinjina.
Bayan ni an kira mata uku suma an basu lambar girmamawa ta zama zakaru a rukuninsu,Daganan an wakilta uku daga cikin mu suka fita suyi jawabin godiya ni dai nace bazan iya ba Saboda ban taba fita gaban jama’a nayi mgana ba ko karban kyatuttukan ma Dakyar na iya fita kamar zan fadi haka na rika ji.
Ma’aikatan da suka koyar damu suna sun yi jawabin godiya ga wannan kungiyar sannan sun gode mana Bisa yadda muka basu had’in kai har muka koyi abunda ake so mu koya har kwalliya ta biya kudin sabulu.
Daganan sai suka koma gefe suna mganganu bayan minti goma aka sanar da kungiya ta ware zakaru guda goma da kungiya zata bama tallafi,Sauran kuma da ba’a basu ba,ba domin ba su kai ba ne a’a haka tsarin kungiya take suma nan gaba zasu iya samu.
Gabana sai ya fara fadi na riga nayi yakinin ko ba’a bani ba bazan bari abunda na koya ya tafi a banza ba sai ga shi nice ta Biyu Fa’iza sidi karofi Hawaye sharr suka zubomin na kasa sharesu bakina har kunne na fita. Kudin a Farar takarda ne an nade sannan ga sunan kungiyar ajiki Hajiyar su Raliya ta bani na Duka har kasa zan karba sai kawai na Daidaici gabas duk da goyon Ahmad dake bayana ban damu ba nayi Sudujul Shukur sai Hall din ya Dau Tafi da kabbara ina dagowa ina hawaye Shabe shabe na saka hannuwa bibbiyu na karb’a sai ta bani abun mgana tace nayi godiya,muryata ta shake ga kuka sannan ga yanayina cikin mganata nace”Alhandulillah ya Allah Godiyar ta sace.Domin abu mai kyau ko akasasin sa daga gare sa ne,Ina godiya ga wannan kungiyar na gode..Madallah da mutanen kirki, madallah da mutanen kwarai masu karamci.
Nagode Allah ya jibanci lamuran ku, kamar yadda kuka jibanci namu Allah ya suturtaku kamar yadda kuka suturtamu Allah ya albarkaci dukiyar ku da ya’yan ku da iyalan ku gabadaya, Allah yasa wannan aikin taimakon naku ya zama mizanin ku a gidan Aljannah..Nagode Nagode, na yaba ubangiji ya gani sannan yafini yabawa”
Ina ma wannan kungiya fatan alheri Nagode”
Duk da mganar bata fita sosai ammh sun fahimta sai tafi su kuma suna ta amsawa da Ameen,ina tahowa muka had’e da Badariya muka Rungume juna Fadi take”Congratulation Anty Fa’iza”
Ahmad da yaji matsa sai kuka na Sauke shi ta Dauke sa ta dagasa Sama tana fadin”Kai yau ranar farin cikin Umman ka ne ba kuka”
An ta kiran sauran ana basu suna addu’a mata da yawa muna cikin wata Rayuwa masu kuka in an basu suna da yawa,asauran da ba’a basu ba suma ance kungiya zata san abunda zatayi musu daga karshe sun horemu da mu tashi Tsaye mu mori abunda muka koya, acikin Gidajen mu da kadan kad’an watarana sai mu zarce Tunanin mai Tunanin sun Hore mu kada mu zama ballagazun mata mu zama mata wad’anda zasu iya shiga ko’ina saboda kansu da ya’yansu. maraici ba komai ba ne in dai mace ta mike ta nema to zata samu da yardan Allah,Sannan sun horemu da mu gyara kanmu mu zama masu tsafta da kwalliya da ado saboda kada mu zama Borori a gidan mazajen mu, ni dai ban bi ta kan wannan mganar ba saboda da mata masu kyau da nasaba ake yi ba irin mu da muka ke da nakasu a komaii ba, abu daya na sani wannan wajen da nazo ya kara Budemin ido akan rayuwa na Fahimci harkan nema ba bambamci mai kyau ko mara kyau in ka iya kawai ka Huta.
sai biyu na rana aka tashi Taron Haka Badariya da Raliya suka rikamin Gayya gayyan kawayen su muna gaisawa,Badariya ko bata gajiya da Fadin matar yaya na ne fa Sai naji wani abu ya soki raina ko yayan nata bai taba nunani haka acikin mutane kamar ta ba, shiyasa nake kaunar Badariya kwatankwancin yadda take kaunata.
Nayi sallama da matan da muka saba dasu yayin koyan abubuwan da muka koya,Ban samu ganin Hajiyar su Raliya ba suna cikin mutane sai nace Badariya ta bari ta rakani har gida nayi mata godiya.
Ranar saboda farinciki ina komawa gida na tasa kudin nan a gabana ko Bude su ban yi ba ina ta ma Allah kirari da Hamdala,Yara suna Dawowa makaranta na rika daga su sama ina Juyi afalo fad’i nake yi”Umma tayi nasara ya’yan Umma..nayi nasara”
Sai suma suka rika murna suna tsalle Har da Amir ma kamasu na Rumgume hawaye suka gocemin komai na zama a duniya ya’ya ne karfina da ba domin su da ban san kuma ya zan yi ba.
Na shiga gidan sa’adatu washegari nayi mata godiya kwana uku tsskani Badariya tazo mukaje gidan su Raliya chan kusa da anguwan su Anty mahma ce nayi mata godiya tana yaba’min har tace Raliya ta kawo mata alala yayi dadi suna bada girke girken Suna ko Birthday, ko biki in sha Allahu Zata saka arika nema na nace nagode sannan tace nayi shawara da mijina ko yan’uwa na samu wani abun sana’a na siya da kudin hannuna wanda zai taimake ni kada na kashe su a banza nace mata in sha Allahu,muka yi mata sallama ta bani sabulai da Turare kamshi da kudi tace na siya ma Ahmad sweet muka fito ina ta yaba kirkin matar a hanya nace Badariya in ta na da kudi a waya ta kira mun Goggo tace tana da shi,ta ko daga waya ta kirata bayan ta Dauka ta ma zata Hafsat take nema sai tace mata tana bayi
Bayan sun gaisa,Sai Badariya tace Fa’iza ke son mgana da ita.
Yadda Goggo ta jini cikin farinciki yasa ina cewa ina son ganinta tace”Zan zo in sha Allahu gobe daman kamar kin san cikin satin nan nace zan leko na dubaki,najiki cikin farinciki fa:i daga gani wani babban albishir ne ko Ishaq ne ya biya miki Umra”.?
Bansan Lokacin da na kyalkyace da Dariya ba,Itama nasan zolayata take yi.muka rabu akan sai tazo, daganan Badariya ta nufi gida nima na Dawo gida.
Kwana Biyu tsakani sai ga Goggo Ya Isa ya kawota da Safe bayan mun gaisa na basu ruwa na Dauko kudin da Kyautar da aka bani da Takardan shedan abunda muka koya, na sauke gabanta lokaci d’aya na kora mata jawabin komai bakina har kunne Goggo ta Dauki kudin ta farke ta Fiddo su sabbin yan Dubu Dubu ta nuna ma Isa tana fadin”Isa kaga Bud’i daga Allah ko..?.
Yaya isa ya karba ya gani duka kayan ya jinjina kai kafin yace”Lalle Fa’iza na tayaki murna dakyau”
Goggo tace”Duka kyauta Fa”iza..?
Na gyada kai ina Mirmishi Goggo tace”Masha Allah..Allah ya saka musu da alheri Allah ya biya su kudin nan sunzo a daidai daman mun yi mgana da Sauran yan’uwanki nace su had’a miki kudi wanda zaki rike ki fara wata sana’ar zama haka bazai yuyu ba,sai kuma muka ga abun alheri ai shikenan ma fad’uwa tazo daidai da zama kenan”
Goggo tace na ijiye kud’in zata koma in na chan sun hadu zata sake dawowa,na tambayi Goggo dame zan fara na sana’a?
Da sauri Yaya Isa yace”Ki fara da sai da zobo da Kunun aya, da ruwa tunda kin koya kuma kin iya sauran sana’o’in ko daga baya sai ki fara bazai gagara ba”
Nima na yarda da shawaran sa haka ma Goggo sun tafi da niyar goggo zata kawo min kudin in su hada na bangaran su.
sai na had’a dashi Tare da Yaya Isa zasu kara dawowa.sai ayi shawaran Fridge din da za’a siya mai kyau, wanda zan fara sana’ar dashi.
Janafty


