Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 38

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 38

20
0

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

SHAFI NA 38📑

__ 📖 Tashi Aunty hauwa tayi zata wuce ɗaki tace wa Umma halima, “hmmm nikan ae bazan iya zama inuwa ɗaya da Abdallah ba, don wani irin son girma ne da shi, kuma bazan bashi Aisha ba don duka zai na mata, fuskan shi babu fara’a ko kaɗan”, ta faɗa lokacin data ƙarasa shiga ɗakinta.

Murmushi Umma halima tayi tana jujjuya kanta, “yaro yarone” ta faɗa ita kaɗai tana murmushi, a haka Mama ta fito suka ci gaba da hiran su.

Uncle Abdallah lecturer ne a ABU Zaria, yana koyar da English, sannan kuma masters yake da shi, zuwa yanzu yana PHD ɗin shi, kuma ya kusa ƙarasawa, shi mutum ne ɗan bokon gaske, saidai wani halinshi guda ɗaya na ƙin son shiga mutane, shine abun da duk familyn su basu so, domin kafin kaga murmushi a fuskar shi toh sai wani muhimmin abu na gaske, kuma baya shigewa kowa kuma koda mahaifin shi ne, da sun gaisa zaka ga yaja bakin shi ya tsuke, saidai yayita bin mutane da kallo, sau dayawa ma idan kaji muryanshi toh shida Baba Umar ne, amma ya wuce shi bazaka ji bakin shi ba, kullum zaka ganshi da laptop kawai ya na danne dannen shi a ciki, Abdallah kenan.

Rayuwa babu wuya, yau ana saura kwana ɗaya Aunty hauwa tafita a takaba, duk wani a halin gidan Baban Narabi sunzo wuni gidan, duk wanda ka dubi fuskan shi zaka ga yanayi na jimami a tare da shi, zuwa azahar su Ummi da Abba suka ƙaraso Narabi, domin mu an bar mu a chan lagos, gidan abokin Abba aka kaimu, da yamma kuma sai ga Uncle Abdallah ya iso, amma ko kaɗan bai leƙa inda Aunty hauwa ta ke ba, aikowa yayi aka ɗauka mishi Aisha kawai, inda suka san shine yazo, ganin haka Aunty hauwa tafara nuna ɓacin ranta da fargaban kada ya ɗauke Aisha, Ummi ce tayita bata haƙuri tana nuna mata ta kwantar da hankalinta Abdallah bai isa ya ɗauki yarinyar ba bada izinin Baban shi ba, kuma ae bayi da mata ina zaikaita? Haka dai Aunty hauwa ta kwantar da hankalinta.

Washegari Baban Narabi yasaka aka taho da ita chan main house ɗinsu, inda lokacin kuma ƙanin Bappanta da kuma Uncle Auwal sunzo daga misau, a lokacin ne taga limamin garin da wani alƙali da wasu ƴan’uwan Baban Narabi guda biyu, abin tausayi a ranan aka raba gadon Baba Umar kaf, bayan anyi mishi addu’o’i, dukkan ilahirin gidan kuka sukeyi, abin tausayi hattah Baban kasa daurewa yayi, shima kukan ya dinga yi kaman yau aka mishi rasuwan.

Bayan komai ya lafa, Baban Narabi ya danƙa gadon Aisha gaba ɗaya a hannun Abba, sannan ya ɗauki kason shi daya gada ya raba shi kashi uku, ya ɗauki kashi biyu ya ƙarawa Aisha, sannan ya ɗauki kashi ɗaya ya danƙawa Uncle Abdallah yace, “Abdallah wannan dukiyar dana gada ne a wurin ɗan’uwaka, amma ina son duk wani abu da zai kai lada kabarin shi kamun da shi, yazamo sadaƙatul jariya wa Umar ɗina”, ya ƙarasa yana share hawayen shi, shima Uncle Abdallah sunkuyar da kai yayi yana share hawayen shi.

Baban Narabi hana su Aunty hauwa tafiya yayi a ranan yace su bari sai gobe da safe idan Allah ya kaimu, babu yadda suka iya haka suka kwana a gidan, washe gari da safe motan Uncle Abdallah yazo ya ɗauke su har misau, amma bashi ya kaisu ba wani abokin shine, Ummah halima tayi kuka kaman ranan aka mata rasuwan, haka dukkan su ƴan gidan suka haɗa mata da kaya mai ɗumbin yawa wai na fita takaba, mazan su da matansu, har da iyayen Aunty suwaiba sun aiko mata kusan kala uku da kaya wa Aisha, uban gayyan kuma akwati guda ya haɗawa Aisha, amma ita ko zani ɗaya bai mata ba.

Sun koma misau basu fi kwana biyu ba Ummi ta tattara su suka wuce lagos,ta kai kusan wata uku acan aikin ta ya samu a specialist hospital bauchi, lokacin ya zama dole ta yaye Aisha, bayan ta tafi ne kuma Uncle Abdallah yazo ya duba Aisha.

Duk yadda mutane suka so auren Aunty hauwa da Uncle Abdallah abin yaci tura, don Baban Narabi babu yadda baiyi da uncle Abdallah ba amma sai yace wai ae ita bata ƙiran shi ta gaishe shi, haka Baban zaiyi ta faɗa amma Uncle Abdallah yayi shiru.

Aisha tanada 3yrs mu kuma muna da 8yrs uncle Abdallah yayi aure, inda ya auri wata yarinyar ƴar zaria, student ɗin shi ce, a lokacin ya fara tayar da maganan shifa so yake riƙon Aisha ya dawo hannun shi, ganin haka Abba ya neme shi yayi mishi kacha-kacha, yace mishi koda Baba Umar yana raye tunda yayi mishi alƙawarin ya bashi Aisha, to ko shi bai isa ya karɓi Aisha ba ballantana shi Abdallan, shima Baban Narabi bai ƙyale shi ba, inda Umma Halima da Aunty Amina suka nuna mishi bai kyauta ba, dama ya yadda ya auri hauwa ne toh ko hutu sai Aisha ta dinga zuwan musu, amma bai da ikon karɓan Aisha a hannun Baba Gambo, haka suka mishi babu daɗi, rai a ɓace ya miƙe yana duban Aunty hadiza da tunda aka fara maganan bata ce uffan ba, ita dai kuka kawai ta keyi, ya dubeta yace, “kin sa mutane a gaba kina ta kuka, toh ni kuma yayah kuke so nayi? Kullum sai kuce wai na auri Hauwa, meye riban auren tan bayan ba bani riƙon ƴar za’ayi ba? Kuma ita kun taɓa ce mata ta aure ni? Kalan kusa yarinya ta rainani nace ina sonta”, ya faɗa kaman zaiyi kuka.

Hararan shi Aunty Amina tayi sannan tace, “dalilin ka kenan da yasa kaje ka auri wanda ta kusan sa’ar ka? Don wallahi wannan mata taka fadilan tayi kusan sa’ar ka, kuma tunaninka ita hauwan ce yakamata tace tana sonka? Ina ka taɓa ganin anyi haka”?

“Toh ae sai kuce mata kun bata ni bawai ni ayita mun masifan naje na zubar da girmana a gabanta ba, ga shi dama yarinyar ba kunya bane da ita, sai tayi tayiwa mutum kallon sa’anta, ni ko na aure ta wallahi bazan ɗauki raini ba a wurinta, gashi ita tana bauchi ni ina zaria yayah za a yi”?

Yana gama faɗin abinda yake ranshi yaja tsaki shi kaɗai, murmushi Umma halima tayi, tana duban shi tace, “tun farko mai yasa baka ce kai girman kai bane yake damunka a ranka, har saida komai ya ƙure tukun zaka nuna mana gaskiyan abinda na daɗe ina ganin zahirin shi a fuskar ka”?, Aunty Amina ta dubi Umma halima tace, “kaman yayah lokaci ya ƙure Umma”?.

Ajiyan zuciya Umma halima tayi, “Amina wallahi tun rasuwar Umar Allah yaga zuciyata naso Abdallah ya auri matar nan hauwa, saboda gaskiya ƴar mutuncine, amma Abdallah yaƙi ɗaga kai, toh ni muna zumunci da iyayenta sosai, yau baifi sati ba Mamanta ta ke gaya mun wani likita a wurin aikin su ya tura manyan shi domin neman auren ita hauwar, kuma iyayenta sun amince da shi, yanzu maganar danake miki ma zuwa nanda wani watan auren za’ayi”.

Share hawayen ta Aunty hadiza tayi ta dubi Umman su tace, “toh Umma ayi wa Baba magana mana a tura maganan yayah Abdallan, ina ga ae zasu fi sun na yayah Abdallan akan wani daban”, ta faɗa kaman zatayi kuka.

Shima Abdallan shiru yayi yana jiran yaji mai Umma halima zata ce, amma abin mamaki sai Umma Halima tace, “gaskiya bamu isa yanzu mu tura maganan Abdallah ba, bayan tun farkon rasuwar Mahaifinta sai da yayi magana da Baban ku akan ko zai tuntuɓi Abdallah akan Hauwan? Amma firr Abdallah yaƙi maganan, toh yanzu kuma ae bamu da bakin cewa muna so”.

Tashi yayi bai ce musu uffan ba ya bar cikin ɗakin Umma haliman, dukkan ido suka bishi da shi babu wanda ya hana shi fitan da zaiyi.

Aunty hauwa tana zaune a gidan wani cousin ɗinta wani likitane, yayan Aunty Ummi matar uncle auwal, yana zaune a cikin drs quaters da take kusa da asibitin, da yake night duty ta keyi ranan tana gida babu inda taje, suna zaune da matar yayan nata mai suna Aunty uwani, matace mai matuƙar kirkin gaske, duk yadda mutane suke nuna mata illar zaman Aunty hauwa a gidan ta bai dame ta ba, kowa yana ce mata mace kyakkyawa kuma yarinya ƙarama bata tsoro ta aure mata miji? amma ko kaɗan bata kula su, a haka har Aunty hauwa ta haɗu da wani Dr ɗan garin Azare wato Dr basheer.

Suna zaune akan dinning ita da ƴar Aunty uwani mai suna Nabeeha, tana ta mata assignment ɗin da aka bata, ita kuma Aunty uwani tana cikin parlourn tana zaune tana kallon wani indian film.

Ringing wayan Aunty hauwa ya fara, ganin baƙon number ta daɗe tana kallo har sai da ya kusa tsinkewa tukun ta ɗauka, “idan kina gida ki fito ina ƙofar gida”, abin mamaki ya bata, ɗago wayan tayi ta duba numbern sannan ta mayar da wayan kunnenta tace, “ban gane da wa nake maganan ba, don banida number”?, “Baban Aisha ne, kina gida ne”?

Jiki a sanyaye ta amsa mishi da “ehh” bai jira wani abu ba ya kashe wayan, shiru tayi tana duban Aunty uwani da ta ke kallon ta ita ma, ta gane mai wayan tun ɗaukan ta taji irin muryan Baba Umar, amma tsoronta shine, bai taɓa ƙiranta ba a rayuwar shi, toh ko lafiya yau yazo har inda take”?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here