Daga Mohammed Awwal Umar
Gwamnatin Neja ta jawo hankalin al’umma na sanya idanu akan bakin da ke shigowa cikinsu, musamman duba da yanayin tsaro da ake fuskanta.
Kwamishinan ma’aikatar jin dadin manoma da makiyaya, Hon. Umar Sanda Rebe ne yayi kiran lokacin rufe tatsirin Alkur’ani mai tsalki a garin Shakwata wanda shugaban kungiyar Gamayyar mahaddata Alkur’ani da malaman tsangaya ta kasa reshen jihar Neja, Gwani Hussaini Abubakar Shakwata ya jagoran ta. Hon. Umar Rebe yayi kiran ne lokacin da yake wakiltar gwamna Umar Mohammed Bago a taron rufe tafsirin na bana.
Gwamna Umar Bago, ya cigaba da cewar yanzu haka rahoto ya riski gwamnati cewar an sayar da filaye a yankin Shakwata zuwa Maitimbi kuma ba a san wadanda aka sayarwa wadannan filayen ba, wanda gwamnati da jami’an tsaro ba zasu lamunci irin wannan na cigaba da faruwa ba.
Gwamna Umar Bago, yace akwai bukatar kowani magidanci yasan makocin shi, saboda tantance irin bakin da ke shigowa musamman ganin jihar na makotaka da wasu jahohi kuma akwai damanmakin da baragurbi ke anfani da shi suna shigowa cikin al’umma suna cutar da su.
Da yake jawabi bayan kammala saukar Alkur’ani da addu’o’in zaman lafiya, shugaban karamar hukumar Chanchaga, Hon. Mustapha Jibrin Alheri, ya jawo hankalin al’umma a karamar hukumar Chanchaga kan zaman lafiya, inda ya kara da cewar akwai bukatar matasa su rungumi zaman lafiya, iyaye kuma dole su rike matsayinsu na iyaye wajen tsawatarwa.
Aikin ba na gwamnati ba ne ita kadai, aiki ne da duk wani dan kasa na gari zai bada na shi gudunmawa wajen samun zaman lafiya, yace maigirma gwamna da shugabannin kananan hukumomin jihar da jami’an tsaro a kowani lokaci idanunsu a bude wajen sanya idanu da kuma kokarin sauke nauyin da ke kan su na kulawa da hakkin al’umma da kuma tabbatar da samun tsaro a kasa.
Hon. Alheri, ya jawo hankalin al’umma da su taimakawa da shugabanni da addu’o’in alheri dan samun nasarar sauke nauyin da al’umma ta dora masu.
A na shi jawabin, shugaban kungiyar Huffazul Qur’an and Scholars Association Of Nigeria, Gwani Hussaini Abubakar Shakwata ya bayyana cewar kammala azumin watan Ramadan ba shi ne kammala karantarwar ba.
Ya zama wajibi jama’a su yi koyi da abubuwan da Ramadan ta karantar da a aikace, wanda hakan ne kawai zai baiwa mutum damar kusanci da ubangijin shi.
Taron dai ya samu halartar Hakimin Shaku inda ya wakilci mai martaba sarkin Minna, Dr. Umar Faruk Bahago, inda ya yabawa malaman da suka gudanar da tafsiran na bana a masarautar Minna, wajen jawo hankalin al’umma muhimmancin zaman lafiya, biyayya ga dokokin kasa, wanda hakan na nuna cewar Ramadan na tattare da alherai masu yawa, hadin kai, zaman lafiya da bada gudunmawar su wajen cigaban kasa.






