Jam’iyyar ADC ta kaddamar da shafin rajistar mambobi kyauta ta yanar gizo a fadin kasa, a wani bangare na shirye-shiryen zaben 2027.
A cikin sanarwar da sakataren yada labaranta na kasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta umarci tsofaffin mambobinta da su sabunta tare da tabbatar da bayanansu a sabon tsarin dijital, bisa tanadin dokar zabe ta 2026 da kuma ka’idojin hukumar zabe ta kasa.
INEC dai ta fara sanar da cewa za a gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya a ranar 20 ga Fabrairu, 2027, sannan na gwamnonin jihohi da ‘yan majalisun dokokin jihohi a ranar 6 ga Maris, 2027.
Sai dai bayan korafe-korafe kan cewa ranakun sun yi daidai da watan Ramadan, Majalisar Dattawa ta gyara sashe na 28 na dokar zabe, inda ta rage wa’adin sanarwar zabe daga kwanaki 360 zuwa 300 domin bai wa INEC damar sauya jadawali.
A karkashin sabon jadawalin, an bukaci jam’iyyun siyasa su mika cikakken rijistar mambobinsu ta yanar gizo kafin ranar 2 ga Afrilu, 2026.






