Home Labarai Tsohon Gwamnan Kaduna ya maka ICPC Kotu Yana Neman Diyar Biliyan 1

Tsohon Gwamnan Kaduna ya maka ICPC Kotu Yana Neman Diyar Biliyan 1

5
0

El-Rufai Ya maka hukumar ICPC a kotu yana neman su biya shi diyyar Naira Biliyan 1bn Saboda Mamaye Gidansa ba bisa ƙa’ida ba.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El‑Rufai, ya kai ƙara a kotu yana neman a biya shi Naira biliyan 1 saboda abin da ya kira mamaye gidansa ba bisa ka’ida ba da jami’an Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC) suka yi.

Rahotanni sun bayyana cewa El-Rufai ya shigar da karar ne a Federal High Court da ke Abuja, ta hannun lauyoyinsa, yana mai zargin cewa takardar izinin binciken da aka yi amfani da ita wajen shiga gidansa ba ta cika sharuddan doka ba.

A cikin takardar karar, El-Rufai ya ce jami’an ICPC tare da wasu jami’an tsaro sun shiga gidansa da ke Aso Drive a Abuja, inda suka gudanar da bincike tare da kwashe wasu takardu da na’urorin lantarki.

Ya ce matakin ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya, domin yana take masa ‘yancin sirri da mutunci, wanda ya sa yake neman kotu ta ayyana binciken a matsayin haramtacce.

El-Rufai ya kuma bukaci kotu ta umarci a mayar masa da dukkan kayayyakin da aka dauka daga gidansa, tare da biyan shi Naira biliyan 1 a matsayin diyya saboda abin da ya kira cin zarafin hakkinsa.

Lamarin na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da cece-kuce kan binciken da wasu hukumomin gwamnati ke yi kan wasu lamurra da suka shafi tsohon gwamnan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here