Ba wani abin tashi hankali domin Asiwaju Bola Tinubu ya bar filin kamfe a lokacin da ba a tashi ba, kamar yadda wasu suke kokarin nunawa.
Punch ta ce Darektan yada labarai da hulda da jama’a na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a APC ya fitar da jawabi a kan abin da ya faru yau.
A ranar Larabar nan, Bola Tinubu da shugabannin APC suka je Minna, jihar Neja domin kamfe.
Hakan na zuwa ne bayan gangamin da aka yi a Kaduna.
A jawabin Bayo Onanuga, ya musanya rade-radin cewa an dauke dan takaran na jam’iyyar APC daga taronsu da aka yi a Minna ne saboda rashin lafiyar da ta taso masa.





