Home Siyasa 2027: Mutuwa ta haɗa manyan ‘yan takarar gwamnan Sakkwato a karon farko

2027: Mutuwa ta haɗa manyan ‘yan takarar gwamnan Sakkwato a karon farko

35
0

Jana’izar Alhaji Mansur Sarkin Fadan Jarman Sakkwato da aka gudanar a gidan jarma Alhaji Ummaru Kwabo dake Unguwar Polo a birnin jihar Sakkwato  a Alhamis ta haɗa Gwamnan Sakkwato Alhaji Ahmad Aliyu da yake takara a jam’iyyar APC domin wa’adi na biyu da tsohon mataimakin Gwamnan Sakkwato Alhaji Manir Muhammad Ɗan’iya da yake yi wa  babbar jam’iyyar adawa ta ADC takarar Gwamna.

Margayin ɗan siyasa ne da ya yi fama da jinya a Asibitin Abuja kafin rasuwarsa.

Wannan ita ce haɗuwarsu ta farko a gaban jama’a tun bayan da suka zama ‘yan takara a mabambantan jam’iyyu.

Haɗuwar duk da ba wuri ne na murna ba an gansu sun mutunta juna tare da nuna siyasa ba da gaba ba, hakan ya aika saƙo a tsakanin magoya bayansu da ke suka tare da cin zarafin juna saboda bambancin ra’ayin siyasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here