Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi zargin cewa wasu gwamnoni na komawa jam’iyyar APC ne saboda sun yi imanin cewa za a murde sakamakon zaɓen 2027.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata hira da Central TV, inda ya ce abin takaici ne yadda wasu ‘yan siyasa suka daina amincewa da ƙuri’un al’umma, suna ganin fadar shugaban kasa, hukumomin tsaro da hukumar zaɓe ta INEC za su yi aiki domin tabbatar musu da nasara.
Ya ce wannan tunani ne ke ƙara haddasa sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC, yayin da wasu masu riƙe da muƙamai ke neman fa’idar siyasa kafin babban zaɓen 2027.
Kwankwaso ya kuma yi gargaɗin cewa dimokuraɗiyyar Najeriya ba za ta samu ƙarfi ba sai idan ‘yan siyasa sun fifita ra’ayin masu zaɓe fiye da duk wata anfani ta siyasa.






