Home Siyasa 2027: ADC ta zargi Tinubu da kafa jam’iyyar NDC domin raunata ƴan...

2027: ADC ta zargi Tinubu da kafa jam’iyyar NDC domin raunata ƴan adawa

2
0

Jam’iyyar ADC ta zargi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyarsa ta APC da hannu wajen kafa sabuwar jam’iyyar NDC, tana mai cewa an ƙirƙire ta ne domin kawo cikas ga haɗin kan ƴan adawa kafin zaɓen 2027.

ADC ta ce kafa NDC wata dabara ce ta rarraba ƙuri’un ƴan hamayya da rage ƙarfin jam’iyyun adawa da ke shirin ƙalubalantar gwamnatin APC mai mulki.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa maimakon ƙarfafa dimokaraɗiyya, an samar da NDC ne domin haddasa rabuwar kai a tsakanin ƴan adawa.

Sai dai APC ta musanta zargin, tana mai cewa ba ta da wata alaƙa da kafa jam’iyyar NDC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here