ฦ๐๐ป๐ด๐ถ๐๐ฎ๐ฟ ๐๐๐ฅ๐-๐ฅ๐๐ง ๐๐ฎ ๐ฏ๐ฦ๐ฎ๐ฐ๐ถ ๐๐๐ฎ๐บ๐ป๐ฎ๐๐ถ๐ป ๐ฆ๐ผ๐ธ๐ผ๐๐ผ ๐๐ฎ ษ๐ฎ๐๐ธ๐ถ ๐บ๐ฎ๐๐ฎ๐ธ๐ถ ๐ธ๐ฎ๐ป ๐บ๐ฎ๐๐ ฦ๐ผฦ๐ฎ๐ฟ๐ถ๐ป ษ๐ฎ๐๐ธ๐ฎ๐ฟ ๐ฑ๐ผ๐ธ๐ฎ ๐ฎ ๐ต๐ฎ๐ป๐ป๐ ๐ฎ๐ธ๐ฎ๐ป ๐ฆ๐ต๐ฒ๐ถ๐ธ๐ต ๐ ๐๐๐ฎ ๐๐๐ธ๐๐๐ฎ ๐ฑ๐ผ๐บ๐ถ๐ป ๐๐ฎ๐ฏ๐ฏ๐ฎ๐๐ฎ๐ฟ ๐ฑ๐ฎ ๐๐ฎ๐บ๐ฎ๐ป ๐น๐ฎ๐ณ๐ถ๐๐ฎ ๐ฎ ๐ท๐ถ๐ต๐ฎ๐ฟ
ฦungiyar kare haฦฦin bilโadama ta International Human Rights Commission โ Relief Fund Trust (IHRC-RFT), ta buฦaci Gwamnatin Jihar Sokoto da jamiโan tsaro su gaggauta ษaukar mataki kan masu ฦoฦarin ษaukar doka a hannu, musamman dangane da lamarin Sheikh Musa Lukuwa.
A wata sanarwa da Daraktan Hulษa da Jamaโa na IHRC-RFT a Jihar Sokoto ya fitar ga manema labarai a daren Talata, ฦungiyar ta yi Allah-wadai da abin da ta bayyana a matsayin gazawar hukumomin tsaro wajen ษaukar mataki kan wasu kalamai da Sheikh Musa Lukuwa ya yi da kuma ikirarin da wasu matasa suka yi akan Malamin.
ฦungiyar ta ce kalaman na iya haifar da tashin hankali da tada zaune tsaye, yayin barazanar matasan masu dauke da makamai kan iya rura wutar rikici a jihar.
IHRC ta yi kira ga Gwamnatin Sokoto da jamiโan tsaro da su ษauki matakin gaggawa domin dakile duk wani abu da ka iya haifar da sabon rikici.
IHRC-RFT ta kuma yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da bin doka da oda, tare da kare zaman lafiya da tsaron alโummar jihar Sokoto.






