Home Labarai Sarkin Kano ya karya dokar gwamnatin Kano ta hana hawan doki

Sarkin Kano ya karya dokar gwamnatin Kano ta hana hawan doki

52
0

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya hau doki daga Ƙofar Mata zuwa filin wasa na Sani Abacha da ke Kano, domin halartar taron bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya.

Siyasarmu TV ta rawaito, gwamnatin Jihar Kano ta sanar a ranar 27 ga Satumba cewa ta dakatar da dukkan nau’o’in jerin gwanon Durbar da hawan dawakai a cikin birnin Kano har sai baba ta gani.

Gwamnatin ta ce an ɗauki matakin ne bisa shawarar Majalisar Tsaron Jihar, saboda fargabar yiwuwar arangama da kuma matsalar tsaro.

Wani faifan bidiyo da Premier Radio ta wallafa ya nuna yadda Sarkin Muhammadu Sanusi II ya hau doki tare da rakiyar tawagarsa, inda suka nufi filin wasa na Sani Abacha domin halartar bikin ranar ’yancin kan Najeriya.

Matakin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamnatin Kano ta sanya dokar dakatar da hawan dawakai a cikin birnin, bayan wani taron hawan doki da Aminu Ado Bayero ya gudanar a Kano, lamarin da ya sake janyo cece-kuce kan rikicin masarautar Kano da kuma yadda ake aiwatar da dokar hawan dawakai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here