Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 10

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 10

2
0

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

SHAFI NA 10📑

__📖 “Kinsan duk wanda ya gan mu zai yi tunanin mu miji da mata ne, so idan nace mata ba haka bane ba zata yadda ba, zata tsaya ta yi ta damun mu da tambaya, kuma ma na lura so na ta keyi, tun ranan da na fara zuwa cin abinci nan wurin”.

ya ƙara sa maganan yana kallo na.

Tsakin da ban shirya ba na yi, ina duban shi kaman zan fashe a wurin na ce,
“tun da ka lura tana son ka ba sai ka daina zuwa cin abinci wurin ba, in banda kai ma, kana da mata ya ya zaka dinga sayen abinci a waje? Kawai ka daina zuwa don Allah Dr’mu”.

“Saidai idan zaki na dafa mun to sai na daina zuwa wurin, amma mata na ita bata iya girki ba, saya itama ta keyi kullum, ko kuma ni na dafa mana”.
cewar Dr Hussain.

Baki na buɗe ina kallon shi cike da mamaki,
“amma dai wallahi ta yi kyaun banza, ace mace ba zata yi girki wa mijin ta ba kam ai da sauran ta kuwa, kyaunta bai amfane ta komai ba, kace ashe dole su kazan mayu su dinga tsintar ka a wurare da yawa a ƙasan nan”.

“Hmmm wata rana naje wani wurin cin abinci ma haka su kayi ta bina, ɗayar bakiga kyaun ta ba, ina ga duk duniya ban taɓa ganin mai kyawun ta ba, gata ƴar duma-duma da ita, ranan kwana nayi banyi bacci ba, ina rufe ido na sai na ganta a ido na”.
ya faɗa yana jinjina irin kyaun da ya gani.

Kallon shi na ke yi baki da ido na a buɗe, “amma dai kam aljana ce ba mutum ba, don duk wacce ta fini kyau kam ai ta zama aljana, wallahi kadai na yawon sayen abinci, gara ma na dinga da fa maka kada wata rana ƴan gidan ku su samu labarin ka shiga jeji”.
na faɗa ina jin zuciya ta kaman zai fito waje.

Ɗaga kafaɗan shi yayi alaman duk yadda na gani haka za’ayi.

“Hmmm”.
kawai nace domin raina yayi matuƙar ɓaci da jin yadda ake son shi.

“Kinyi shiru baki ce komai ba”.
ya jefo mun tambaya yana tsaye a gate ɗin gidan mu domin jiran a buɗe mishi.

“To ni Humaira me zance? Kawai sakarar matar ka ta kasa kula da kai, common girki ba zata zauna ta maka ba, har sai kajin mayu sun haɗu sun lashe ka tukun tazo tana kukan wai ita ma tana son ka ko? Da ƙafanta a sandare kaman taɓarya, ni shiyasa ban cika son naga mace mai kyau da yawa ba, don wahalar da miji su keyi irin su, ballanta na kai da baka ganin kyaun kowa sai nata, to ko me zance? Sai dai na yi ta addu’an Allah ya kare ka daga sharrin su, ni daba ka ganin kyauna ni yazama mun dole na Kula da kai ai”.
Na faɗa raina a ɓace.

Haka muka yi parking na fita a motan ina duban shi nace, “to what time zamu koma asibiti wurin Amal? Kasan yau su Abbun ta zasu iso da dare”.

“Ki bari sai 6:00pm sai muje, idan yaso 9:00pm sai mu dawo”

Kaɗa kaina nayi alaman ya mun, sannan na wuce na yi side ɗina, ina shiga kwanciya nayi a parlor ina ta tunanin labarin da Dr ya bani wai yaga kyaun wata, ikon Allah ko me yasa ni baya ganin kyau na? Hmmm shi ya sani na faɗa a zuciya ta.

Muna shiga hospital ɗin muka ci karo da Dr Abdallah ya fito shi da wasu nurses guda biyu daga ɗakin, amma sakarai har ya manta abinda ya faru jiya, yana ganin mu ya fara mana murmushi kaman yaga wasu ƴan’uwan shi.

Da sauri Dr Hussain na ji ya saka hannun shi ya riƙo nawa hannun, fuskar shin nan kaman bai taɓa dariya ba, yadda kuka san ya shigo class yana lectures haka ya yi da fuskan, koma nace yama fi hakan.

Kallon fuskar shi na yi da nufin zan ƙwace hannu na, amma ganin yanayin fuskan na shi sai na nutsu na cigaba da bin shi a hankali, muna zuwa dab da Dr Abdallah, kawai sai yaja ya tsaya yana miƙawa Dr Hussain hannun shi ɗauke da murmushi, hannu Dr na ya miƙa amma fuskar shi bai ko sa ke ba, sai wani ƙara tantame ta da ya yi, suna gaisawa Dr Hussain ya ja hannu na da sauri muka shige ɗakin da Amal ta ke ciki, ko jiran mai Dr Abdallah ya ke faɗa mun bamu yi ba.

Muna shiga Amal ta harare ni ta kawar da kanta gefen da Dr ya ke tsaye tana gaishe shi, ita kuma nurse ɗin da ta ke zaune ta tashi ta fita ta bar mu, dariya na yi ina kallon ta nace,

“to laifin me na yi kika ƙi kallo na ballanta na ki amsa gaisuwan da na ke yi miki?”.

“ki koma da gaisuwan ki, tunda sai yanzu kika ga daman da wowa”.
ta faɗa ta na ƙara ɗaure fuskan ta.

Kallon Dr na yi da yake zaune a wani 2sitter da yake gefen gadon ta yana ta daddana wayan shi, bai ko kalle mu ba, dariya na yi na koma gefen shi na zauna ina cewa,

“Dr’n mu don Allah ka bata haƙuri, ka gaya mata kaine kace muje cin abinci shi yasa ma ban dawo ba ko”.
na faɗa ina neman shi ma ya ƙara na shi bayanin.

Kallon ta yayi ba tare da yace mata uffan ba, sai na ji tana cewa,
“Allah ya soki kinci Albarka cin Dr, amma da yau nayi fushi da ke, kinsan ɗazu ƙafana su kayi ta ciwo, har saida aka mun allura kusan guda biyu, kuma Abbu zasu iso wurin 7:30pm, shi yasa duk na damu da rashin ki”.

Haƙuri na bata nace mata ina nan har 9:00 insha’Allahu, sannan na matsa kusa da Dr ina leƙa abinda ya keyi a cikin wayan shi.

Juyowa ya yi kaɗan ya dube ni ta gefen idon shi, baice komai ba ya cigaba da abinda ya ke yi cikin wayan na shi, a hankali nace,

“Dr nah bani nima nayi game ɗin Angellah ɗin”.

bai kula ni ba ya cigaba da dannan wayan shi, ba’a ɗauki lokaci ba muka ji buɗe ƙofa da shigowan Dr Abdallah, ina ganin Dr babu shiri ya saka hannun shi ya matso dani kusa da shi sosai, yana miƙo mun wayan yana cewa,

“Babyn baby zo ki buga naga irin naki ƙwarewan? Idan kin kaini to zan miki kyautan ban mamaki, idan kuma na fiki to zaki mun kyautan duk abinda na faɗa”.
nima murmushin na keyi na karɓi wayan ina buga game ɗin, ko in da Dr Abdallah ya ke ban kalla ba.

Juyawa ya yi ya bar kallon mu, idon shi ya maida kan Amal yana gaya mata isowan su Abbu, yanzu zai wuce airpot, amma wurin 7:30 zasu shigo hospital ɗin, yana gama faɗa ya juya da sauri ya fita.

Da ido Dr Hussain ya bishi, sannan ya maido da hankalin shi kaina, a hankali yace, “bari na fita mosque nayi sallan magarib da isha, idan na idar zan dawo”.

Amsa mishi nayi da kaina ina miƙa mishi wayan, kallo na yayi kaɗan kafin ya saka hannun shi ya karɓa ya fita a ɗakin.

Dawo da kallo na nayi kan Amal ina murmushi nace, “sis ya ya jikin dai?”.

Harara na tayi ta ce, “ban sani ba, sai da ki ka gama soyayyan ki da Dr Hussain bayan ya tafi tukun zaki dawo nuna mun kulawan ƙarya”.

Buɗe baki nayi ina dariya nace,
” me yasa baki yadda da cewa babu komai tsakanin mu da shi ba? Mutumin da yake da mata da buhu-buhun ƴan mata kyawawa mai zai yi dani ƴar cukulan nan?”.

“Za kuji da shi ai daga ke har shi ɗin, mutumin da ake cewa ko cikin lectures ƴan uwan shi baya kula su, amma ke gaba ɗaya ya ɗauki time ɗin shi yana baki, kuma har yana fita da ke, yana kuma biye duk wasu shirmen ki, amma kina raina mun hankali wai babu komai tsakanin ku? To kada ki gaya mun, a barshi idan ya yi tsami zanji ai”.

Kama baki na yi ina hararan ta, ” amma Amal baki da hankali, ki rasa da wanda zaki ce ina soyayya sai da wanda yayi kusan haihuwa na? Bakiga yayi mun girma bane? ae wannan wayo zai na mun idan na aure shi, kawai dai muna shiri ne ki gane hakan”.

“Zan gane ai ranan da duk nagan ki a gidan shi”.
ta faɗa tana kumawa kwanciya.

Dariya na yi ban ce mata komai ba, sai tashi da nayi na shiga toilet ɗin nayi alwala domin yin sallan magrib.

Wallahi yau bazan iya typing mai yawa ba, duk a gajeye na ke, kuyi haƙuri da wannan.

JIKAR KULU, WANNAN SHAFIN NAKI NE KYAUTA NA BAKI, DUK YADDA KI KE SO KIYI DA SHI, NAGODE DA ƘOƘARIN DA KI KE MUN, ALLAH YA BAR ZUMUNCI.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here