Home Daga Marubutanmu Ƙaddara Ta Riga Fata: Fita Ta 21

Ƙaddara Ta Riga Fata: Fita Ta 21

15
0

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE✍🏼
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU

Wannan shafin nakine MUM SAYYEED Allah ya bar zumunci

SHAFI NA 21📑

__📖 Murmushi nayi ganin ya buɗe idon yana mun alaman da yara sukewa iyayen su idan suna son abu a hana su, ganin ina murmushi shima ya maida mun martanin murmushin, “Baby kaman yau bazan iya bacci ba idan bamu tare, yayah za’ayi ne wai? Babyn ki fa abin tausayine fah”, ya faɗa yana ƙara matsuwa kusa da inda nake.

Murmushi nayi na ɗan matsa baya kaɗan, don yazo dab da ni har ina jin numfashin shi a kusa da ni, “Baby toh kasan babu yadda zan maka, domin Allah bai halattah kwanan mu wuri ɗaya ba, saboda haka kayi haƙuri ka koma ka kwanta, da safe zamuyi magana, yanzu kam ae ka ganni”, na faɗa ina ƙara sauƙe mishi murmushi.

“Babyn baby toh ae yakamata nayi wa Daddy magana domin ayi auren akan lokacin, don gaskiya ni nafara nema na rasa nutsuwa na akan ki, kuma ni irin su Faisal ɗin nan ba zasu barni na samu kwanciyar hankali ba”, ya faɗa yana harara na da wasa.

Dariya nayi mai ɗan sauti, “Baby aure kuma tun ban girma ba? Gaskiya ni sai nayi masters ma tukun nayi aure, nidai gaskiya naƙi ba yanzu ba”, na faɗa ina dariyan yadda ya buɗe ido da bakin shi yana kallo na cike da mamaki.

“Gaskiya bazai yiwu ba baby, ni bana son kodawo wani semester ma ba muyi aure ba, idan ba haka ba zan taro gidan nan da zama, da kike cewa baki girma ba, bazaki iya ɗaukan Babyn ki bane?” … Faɗin haka da yayi nayi sauri na rufe ƙofan da ƙarfi, na juya da gudu nayi cikin ɗakin mu ina dariya, da yake duk abun da mukeyi wayan mu yana kunnen mu babu wanda ya kashe, inajin dariyan shi ta cikin wayan yana cewa, “ƙarya na miki? Kuji mun ƴan matan nan da wayo, kina birkita ni da salon soyayyah ki kuma kina cewa baza muyi aure yanzu ba”? Ina jin shi nayi sauri na katse wayan nima ina dariya, kan bed ɗin na faɗa ina dariya ni kaɗai na.

“Don Allah ki koma parlor ki kwanta, sai kiyi ta sakarcin dariyan ki achan, yarinya anje an kunche miki kai da soyayyah zaki dawo ki sauƙe mun buhuhhunan haukan anan ko? Toh baki isa ba, koma kije chan ku kwana kuna gigita junan ku”, Amaal ta faɗa tana turo ni daga kan gadon.

Dariya nayi ina faɗin, “baza ki gane bane Amaal ɗita, bansan me nakeji ba acikin zuciyata ga me da Dr, ina mishi wani fitinannen so, wanda yana nema ya fi ƙarfin xuciyata”, na faɗa ina dafa zuciyar bayan na runtse idona.

Kallon mamaki Amaal ta ke mun, “kice bazamu gama school ba za a muku aure”?

Hararan ta nayi, “kaji mun Amaal, bamu gama school ba kuma a mun aure? ae ban girma ba tukun, gara dai sai nagama masters sai amana, lokacin na ƙara girma”.

“Chabb ae ko ba son shi kikeyi ba, tun da har son ya fara fin ƙarfin zuciyar ki ae sai a tattara mishi ke a haɗa ku gida ɗaya, ku cinye kanku da soyayyah, amma ni bazan yadda kije ya birkita ki kizo kina hana ni bacci ba, ehen gara ma ki gane”, Amaal ta faɗa tana komawa tana kwanciya.

Rayuwar yana ta tafiya, a yau muka fara exams ɗin wannan semester, gaba ɗaya mun koma wasu iri, domin dukkan mu muna so mu fito da sakamako mai kyau, duk da irin zafin da muke bawa kanmu, bamu rage komai ba ga me da soyayyah mu, duk abinda muke yi dole sai mun bada lokaci na musamman wa junan mu,una yiwa junan mu so na fitar hankali, gashi bamu iya ɗaukan lokacin bamu neme junan ba, haka wurin Amaal da Dr Abdallah, kullum suna tare da juna, duk yadda kake tunanin sun wuce wurin, domin wani irin kula Dr yake bawa Amaal, kaman ya maida ta ciki.

Daddy hankalin shi ya kwanta sosai, gashi Abbun Amaal yace mishi idan munyi hutu zai haɗa ni da Amaal muje muyi hutu tare a wurin su, domin shi Daddy yace baya son nazo hutu har sai na gama karatu na gaba ɗaya, saboda shi baiga me zai saka na taho hutun ba, gara shi idan anyi hutun ya zo mun, amma jin cewa Abbu yace zamuje wurin shi sai Daddy ya samu nutsuwa, domin dama tunanin shi ko naje gida bawani daɗin zama zamuyi da su Mama ba, gashi anyi auren Adda hafsat Adda Halima ce a gida, shima Yayah Ahmed dama na taho ana shirin auren shi, ganin basu damu dani da rayuwa ta ba, Daddy bai ko gaya mun anyi auren Yayah Ahmed ba.

Ranan da mukayi final exam ɗin mu, rana ce da bazan taɓa mantawa ba, domin a wannan ranan zuciyata ta aminta da irin son da Dr nah yake mun, sannan a wannan ranan na barwa zuciyata ko bai taɓa furta mun kalmar I Luv U ba, toh zan iya ƙarasa rayuwata da shi, domin ya nunawa duniya babu wata mace a zuciyar shi sama dani.

Bayan mun gama paper muna ta sallama da ƴan class ɗinmu, shi kuma yazo ɗaukan mu domin mu wuce gida, Amaal ta gajji da jirana saboda complain da ta keyi na ƙafan ta da yake ɗan mata ciwo, sai ta wuce cikin motan ta zauna, shi kuma Dr nah ya buɗe mun gaban motan yana jira nah, duk da nayi idon shi yana kai na, chan na gama abunda na keyi na taho zan shiga gaban motan inda yayi sauri ya buɗe mun daga inda ya ke zaune.

Ina dab da zan shiga kawai sai naji anyi wulli da ni gefe, wanda sai da nayi ƙoƙarin gaske na daka tar da kaina daga faɗuwa, juya wan da zanyi kawai sai naga Dr Khadijah ce ta wullar dani, ita kuma tayi sauri ta shige gaban motan.

Da sauri Dr Hussain ya fito daga motan ya taho inda na ke da gaggawa, hannun shi ya saka ya riƙo hannu na, hankalin shi tashe ya fara tambaya na, “Baby bakiji ciwo ba? Babu abinda ya same ki”? Ya na tambayan muryan shi da ƙarfi wanda yaja hankalin mutanen da suke wurin, kuma cikin tashin hankali ya keyi, ni kuma ganin hankalin shi ya tashi kuma duk idon mutane ya dawo kanmu, na juya na dubi Dr Khadijah, naga yadda ta buɗe baki da ido tana kallon Dr cike da mamaki, a zuciyata sai naji na raya bari na nuna mata matsayina a wurin Dr, kuka na fara nayi sauri na rungume shi ina faɗin, “Dr nah kaman hannu na data jawo zai tsinke na keji, Dr nah ciwo yake mun har bayana, ni tsoron ta nakeji Baby nah, kace ta tafi bana son ganinta”, na faɗa ina ɓoye fuskana a ƙirjinshi, wai duk na nuna mishi tsoron ganin ta nakeyi.

Ranshi a matuƙar ɓace ya saka hannu ya fisgota da ƙarfin gaske daga cikin motan wanda har sai da kanta ya bugu da jikin motan, wuntsilar da ita yayi da ƙarfi har saida ta faɗi ƙasa, sannan ya dawo dani gefen shi na hagu ya rungume ni ta gefe, ya ɗaga hannun shi na dama yana nuna ta da yatsa yace, “daga yau na miki tsakani da matar da zan aura, Khadijah daga yau na miki iyaka da rayuta, wallahi na rantse miki da Allah idan wani abu ya faru da ita daga rana mai kaman ta yau hukuma za ta mana iyaka ni dake, domin, Hummy bana iya haɗata da komai a rayuwata saboda ita ɗin rayuwa tace, itaɗin haskene a gare ni, duk wani abu da ya sameta marar kyau bazan taɓa yafewa kaina ba, saboda haka ki maida hankalin ki, kuma a yau zaki fuskanci waye Dr Hussain Mohd Aliyu, kuma a yau hukumar makaranta zata miki iyaka dani da iyalina, idan kuma ba a ɗauka hukuncin da yaka mata ba, toh dole na haɗaki da hukuman ƙasanan ɗauka ƙwaƙwaran mataki akan ki, domin taɓa baby”, ya saka hannu ya nuna mata ni, “kaman kin gayyato tashin masifar da tafi ƙarfin cutar corona virus na a wurina, saboda haka ki kiyaye”.

A lokacin shugaban makarantar dana department ɗin suka iso wurin, ga kuma wasu securities mata da aka ƙira suka iso, gaba ɗaya idon Dr Hussain yayi wani irin ja don tsabar masifah, ga wani rawa da jikin shi ya keyi, hannu shugaban makarantar ya saka ya ɗaga Dr Khadijah wanda gaba ɗaya kunya da tsoro ya kamata, sannan ya bubbuga kafaɗan Dr Hussain a hankali yace, “Dr zamu sake jan kunne wa Dr Khadijah a kashi na biyu, wanda idan bata gyara tsarin rayuwarta ba mun maka alƙawarin Makaranta za ta ɗauki hukunci mai ƙarfi gaske akanta, saboda kowa ya maka shaidah baka da abokin faɗa, kai ka bada rayuwar ka da lokacinka ne kawai akan aikin ka, babu wanda ya taɓa jin tsakanin ka da kowa, sai Khadijah da ta ke maka shishshigi, amma kayi haƙuri ka ɗauki sister ka ku tafi hospital a duba mata hannun, don bamu so iyayen yarinya suji wani abu ya samu ƴar su ta dalilin staff ɗinmu, domin zai jawo mana matsalah mai girman gaske”.

Sannan ya sallami student ɗin da suke tsatstsaye a wurin da sauran staffs ɗinsu, ya kuma umurchi Dr Khadija da ta wuce office ɗin shi, sannan ya dubi Dr Hissain yace, “Dr kamaida su ka taho akwai zama da zamuyi da kai da Khadijah a office ɗina”.

Muna isowa gate ɗin gidan mu ya juya ya dubi Amaal yace, “zaku iya shiga ciki ko na shigar daku”? Da sauri Amaal tace, “zamu iya gara kaje tun da ana nemanka da sauri a school, Dr kuma don Allah kayi haƙuri kaji”.

Kallona yayi bai iya amsa abinda Amaal ta faɗa ba, a hankali naji yace, “Baby hannun yana ciwo? Zaki iya daurewa na dawo sai na kaiki hospital, ko kuma na ƙira Dr Abdallah yazo ya duba mun hannun ki”?

Sheshsheƙa na fara yi alaman zanyi kuka, nayi sauri na kwanta akan ƙirjin shi inda na ɗauki hannu na na ɗaura a daidai saitin heart ɗinshi, inajin yadda heart ɗin ya ke bugawa da sauri- da sauri na fara kuka ina cewa, “baby ni na daina jin ciwo a hannuna, kawai inajin ciwon ta ɓata mun ranka ne, baby kaji heart ɗinka yadda yake bugawa da sauri da sauri, idan wani abu ya saman mu kai wallahi bazan yafe mata ba, ni wallahi sai na faɗawa Daddy na”, na faɗa ina ƙaea sautin kuka na.

Ɗago ni yayi a hankali yana duba na yace, “baby kada ki gayawa Daddy, zaiyi tunanin na gaza da baki kulawa ne, kiyi haƙuri babu abinda zai same ni insha Allahu, kawai na damu ne don bazan iya barin wani ma haluƙi yaci zarafin ki ina gani ba, kuma ina baki tabbacin baxan taɓa barin Khadijah ta sake maimaita miki ba, sai dai ta bar school ɗin nan, nidai kiyi haƙuri bari naje na dawo sai muje hospital ɗin”.

“kada ka damu baby na, zan shafa maganin Amaal, dama damuwa na kai ne, kaje sai kadawo my dear, Allah ya tsare mun kai”, na faɗa ina buɗe motan, haka yaja ya tafi, ni kuma na dubi Amaal muka shigo cikin gidan.

muna shigowa Amaal ta kalle ni tace, “munasira babu maganin da zan baki ki shafa, don nasan babu inda yake miki ciwo, sai tsabar sakalcin soyayyah da yake ɓuɓɓula duk wani gaɓa na jikin ki, toh yau hankalin ki ya kwanta , Dr Hussain ya nuna wa duniya babu kaman ki a zuciyar shi ƙorafi ya ƙare daga yau”, ta faɗa tana buɗe mana gidan mu.

Dariya nayi na faɗi ƙasan carpet ɗin ina ta juyi a ƙasa ina cewa, “wayyo my one and only, wayyo babyn baby, wayyo my heart, wayyo honey na, yau kasa ina maka ɓulɓulan so, babu abinda ya saura sai kadawo na riƙe ka wunin yau inyi ta shagwaɓa iya son raina, kai kuma kayita jinya”, na faɗa ina ƙara kwashewa da dariya.

Harara Amaal ta mun tace, “amma ke baki da imani, kibar bawan Allah nan yaji da tafiyan da zamuyi gibe mubar shi, har na tsawon 1month, kibari kuyi sallama basai kin ɗaga mishi hankali ba”.

Tashi nayi na zauna ina kallonta, “lallai ma Amaal, ae saina lugwaigwaita mishi zuciya, wanda idan na tafi tsanani ya daure yayi 1week bai bi baya na ba, kina ganin zan iya 1month babu shi kusa dani? Bazai taɓa yiwuwa ba, tunda Abbu suka ɗauki nauyin Hummy toh dole su haɗa dana Dr nah”, na faɗa ina ƙyalƙyala dariya, ganin yadda Amaal ta bar abinda ta keyi tana kallo na.

“Hmm Hummy kice yau na yi laɓe naga yadda zaki birkita mun kan Dr”?

Dariya na sakeyi nace, “ki tsaya gulma dai kada kije ki birkita kan naki Dr, nidai babu ruwana idan kinga Dr na ya biyoni ke kuma na barki da zaman hira da Ummu”.

“Hummm ni Hummy yanzu gaba ɗaya mamaki kike bani, yadda kika iya ɗauke hankalin wannan babban mutumin, babu wani fargaba yau ya yanƙwana ƙatuwar mata kaman Dr Khadijah akanki”?

Nima Aunty Nice mamaki nakeji na yadda mutumin da bazai iya furta kalmar so ba, amma yayi mata abinda yafi ƙarfin furta kalmaɓ so ɗin ma yau a idon student da malaman su, besty ta dubeni tace “humm Aunty nice mamakin namiji kikeyi?ae ya wuce haka ma idan akan abinda yake sone, kawai yanzu ki bari mujira da wuwan shi muji yayah za ayi sallaman nan”, kallonta nayi nace , “toh bari na tafi na nemo neat lady, saboda mutane suna ta neman book ɗin ta amma ni ban san ina take laɓewa ba, gara naje har gida na fito da ita taxo tayi typing dole yau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here