SOKOTO TA KARBI KUSAN ₦780 BILLION A CIKIN SHEKARU 3 DA RABI TO INA TAFIYAR KUDIN???
Bayanan da Dan gwagwarmaya “IG WALA” ya wallafa a shafinsa da harshen turanci kan rabon kudaden FAAC da IGR, Jihar Sokoto ta samu kusan ₦102 biliyan a shekarar 2023, ₦262 biliyan a 2024, ₦275 biliyan a 2025, sannan kusan ₦141 biliyan a rabin farko na 2026. Idan aka hada wadannan adadin, jimillar kudin ya kai kusan ₦780 biliyan cikin wannan lokacin.
Wannan ba ƙaramin kudi ba ne, kusan ₦780,000,000,000 ne kudin da aka karɓa a lokacin da jihar Sokoto da wasu sassan jihar ke fama da matsalar tsaro, hare-haren “yan bindiga, kashe-kashe, garkuwa da mutane, lalacewar ilimi, rashin isasshen kiwon lafiya, talauci da matsalolin more rayuwa.
Abin da ya kamata al’ummar Sokoto su tambaya shi ne, shin mene ne ainihin sakamakon wadannan kudade a rayuwar talaka?
Idan jihar na karbar irin wannan dimbin kudi daga Abuja, me ya sa har yanzu akwai al’ummomin da suke kwana cikin fargabar “yan bindiga? me ya sa mutane ke gudun hijira daga garuruwansu inda yunwa ta samu malaba a cikin su? me ya sa har yanzu akwai wuraren da al’umma ba su da cikakkiyar kariya, hanyoyi, asibitoci, makarantu da sauran muhimman abubuwan more rayuwa?
Ba wai muna cewa kudin ya kamata a kashe gaba daya wajen tsaro ba. A’a. Amma tsaro shi ne ginshikin komai, Idan rayuwar dan adam ba ta da tsaro, duk wani titi, gini, roundabout ko wani aikin more rayuwa ba zai iya maye gurbin rayuwar da aka rasa ba.
Abin da muke buƙata yanzu shi ne accountability. Jama’ar Sokoto suna da haƙƙin sanin yadda aka samu wadannan kudade, nawa gwamnatin jiha ta karba, nawa ƙananan hukumomi suka samu, nawa aka ware wa tsaro, nawa aka kashe a ilimi, lafiya, ruwa, hanyoyi da sauran ayyuka, kuma menene ainihin sakamakon kudaden a ƙasa.???
Ba siyasa Shetteeman Goronyo ke magana ba. Ina magana ne akan rayukan talakawan Sokoto.
Idan kusan ₦780 billion ya ratsa hannun tsarin gwamnati cikin shekaru uku da rabi, to ya kamata mu ga wani babban canji a rayuwar al’umma. Idan ba mu gani ba, tambayar da ta dace ita ce:
WHERE DID THE MONEY GO???
Ya zama wajibi ga majalisar dokokin jihar, ƙananan hukumomi, da dukkan “yan jarida, kungiyoyin farar hula da kuma al’ummar jihar su nemi cikakken bayani kan yadda aka samu da kuma yadda aka kashe wadannan kudade.
Sokoto ba ta rasa kudi kawai ba, abin da muke bukata shi ne gaskiya, da kuma cikakken bayanin inda kudin al’umma suka tafi.
Kuma idan har wannan adadin da IG WALA ya wallafa ya yi kuskure, to gwamnati ta fito ta gyara shi da official figures. Idan kuwa adadin daidai ne, to al’ummar jihar Sokoto suna da cikakken haƙƙin tambaya:
ME AKA YI DA KUSAN ₦780 BILLION?
Wannan tambaya ba ta APC ba ce, ba ta ADC ko PDP ba ce, ba ta opposition ba ce.
TAMBAYAR TALAKAWAN SOKOTO CE.????






