Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 20

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 20

9
0

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE✍🏼
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

SHAFI NA 20📑

__📖 Tunda ya fara maganan na ke jin hawaye suna bin fuska ta, har ya fita ban samu ikon tashi daga wurin ba, ina zaune a inda ya bar ni Amaal ta fito, da sauri ta rungume ni tana faɗin,
“ALHAMDULILLAH, yau Dr ya bankaɗo sirrin zuciyar shi”.

Juyowa na yi ina duban ta, hawaye na zuba kan fuska na, girgiza ma ta kaina na keyi alaman a’a, ɗaure fuska tayi tana tambaya na, “me yake sa ka ki kuka? Kefa murna ya kamace ki da yi”.

Tashi nayi tsaye na riƙo hannun Amaal,
“Amaal ko ɗaya banji kalmar yana sona daga bakin shi ba, kawai cewa ya yi yana son muyi rayuwa tare a inuwa ɗaya, kawai aure na ya ke son yi bawai yana so na ba, ina ga akwai wacce ya tana da ma ta wannan matsayin”.
na faɗa ina sha re hawayen da ke zubowa.

Ɗakin mu na wuce Amaal tana bina a baya, wanka na shiga nayi, ina fitowa ta shiga domin itama tayi wankan, mun kwanta bayan kowa ta gama shirinta, amma babu wacce tace da ƴar’uwarta uffan.

“Hummy! Kiyi haƙuri ki bi Dr da irin nashi tsarin, na miki imani da Allah Dr yana son ki, kuma ba ƙaramin so ba, insha’Allahu kuma wata ran ke da bakin ki zaki bani labari, kuma ina miki albishir duk ranan da Dr ya furta miki kalmar ina son ki, sai kinfi jin daɗin kalmar da ganin muhimman cin ta sama da yanzu”.
cewar Amaal.

Juyowa nayi ina hararanta da wasa,
“to Amaal saboda Allah a hakan zan yadda yana so na? Shi bazai buɗe baki ya furta mun kalman so yadda ko wani saurayi ya ke yiwa budurwa ba?”.
Na faɗa ina shirin sa ke sabon kuka.

“Don Allah bance kimun kuka ba, wai ke Hummy har sai zuwa yaushe za kiyi wayo ne? Ni fa ban ɗauki wai sai saurayi yace yana sona da ba jin shi ba za muyi soyayya, ai ɗabi’un shi da idon shi ma kaɗai ya wadatar da mace, kawai namiji yace miki yana son ki ai tun zamanin su Ummi a kayi shi”.
Ta faɗa tana ƙyalƙyala dariya.

Kallon ta nayi baki na buɗe, “kina nufin kina soyayya da wani ne Amaal?”.
na faɗa ina duban ta tana shiga cikin duvet tana ta ƙyalƙyala dariya.

Sai da taga na dame ta da magiyan sai ta gayamun, tukun ta buɗe idon ta tana kan dariyan, ta wani kashe ido ɗaya tace, “to ke banda shirme ya yi miki yawa har yau baki fahimce meye ke tsakanina da Dr Abdallah ba ko?”.

Ido na zaro ina duban ta cike da mamaki, “kina nufin Dr Abdallah yace miki yana son ki?”.
na faɗa cike da mamaki.

Dariya tayi mai ɗan sauti, sannan ta tashi daga kwancen itama ta zauna bayan ta jingina bayan ta da jikin gado, tana duba na tace,

“kina tunanin ni irin kice sakaliya wacce ban san ya ya rayuwa ta ke tafiya ba? Mufa ko acikin larabawa muna da family sosai, kuma akwai kyakkyawan zumunci a tsakanin mu, ina ganin yadda ƴan mata da samarin family’n mu suke tafiyar da al’amarin su, kinga basai an mun bayanin yanayin maza ba, zan iya karantar su”.

Ɗago ido nayi na dube ta, sai naji lokaci ɗaya kewan mahaifiya yazo mun, wato da gaske ne wata friend ɗi ta Ruƙayyah muna secondry school ta ce mun,

“Humairah wataran idan kin yi abu sai naga kaman goyon kakace ke, gaba ɗaya baki da wayo, sai buhun wauta, yanzu banda ke Humairah baki lura Umaimah gatse ta miki ba ko? Ke sai yaushe za kiyi wayo ne?”.

Ta faɗa tana dariyan wautan da nayi a wancan lokacin, sai Umaimah ta dube mu tana dariya tace.

“Ruƙayyah ai na gaya miki Humairah rayuwar kan carpet ce, domin ni kullum ƴan aikin gidan su nake ganin suna hidima da ita, tunda na ke zuwa gidan su ban taɓa haɗuwa da Maman ta ba sai dai step mum ɗin ta, kuma sai su wuni basu haɗu ba, to ina za tayi wayo bata zauna a gaban masu saita ta a kan layi ba, shiyasa wataran idan tayi abu sai taban haushi wataran ta ban tausayi”.

ta faɗa dukkan su suna mun dariya, nima dariyan nayi dana lura da shirme da wautan dana tabka musu a lokacin.

Ina dawowa gidan mu daga school kai tsaye parlon Daddy na wuce, in da na tarar da shi da Mama da Yayah Ahmed da Adda Hafsat da Adda Halima a zaune kan dinning suna lunch, gaishe da su nayi na ƙarasa gefen Daddy na rungume shi ina faɗin,

“oyoyooo Daddy nadawo a school”.
shima murmushi yayi yace, “oyoyo Humairan Daddy, zo muci abinci”.
ya faɗa yana manna mun kiss a forehead ɗina.

Da sauri na juyo na dubi Mama jin wani tsaki da taja, muna haɗa ido ta sauƙe mun wani harara wanda sai dana ji zuciyata ta yanke, Adda Halima da Yayah Ahmed ma hararan suka bini da shi, Adda Hafsat ce kawai ta mun murmushi ta sunkuyar da kanta ƙasa ta cigaba da cin abincin ta, ganin abinda suka mun yasa na dubi Daddy ina murmushi nace,

“Daddy ni banyi wanka ba banyi sallah bama fa, kawai nazo na tambaye ka wai da gaske duk ɗan da bai girma agaban Maman shi ba baya wayo?”.

“Jeki kici abinci sai muyi labarin, amma ki kwantar da hankalin ki, kinsan duk yadda Allah yaso mutum ya yi rayuwa haka zaiyi, wani zai yi rayuwa babu uwa babu uba, to shi kuma ya yi ya ya a rayuwa? Wani kuma bai san kowa na shi bama, a gidan marayu ya tashi, to shima ya ya zai yi? Dole duk haƙuri akeyi a rayuwar, ke da duk duniya babu wata ƴar da tayi dace da soyayyan uba irin ki to mai zai dame ki Humairah na? Kawai kiyi addu’a wa Mama’n ki Allah ya kai rahama da haske kabarinta, ni kuma nine uwa kuma nine uba a gare ki, kada ki damu, nima soyayya ta ya isa ya hanaki zama marar wayo, kina da zuciya mai kyau ne, shiyasa ake ganin kaman baki da wayo, je kiyi wanka my dear”.

ya faɗa yana buga kafaɗa na.

Hawayen idona na sha re da sauri na dubi Adda Hafsat da itama ta ke sha re hawayen ta, murmushi na mayar mata yadda itama ta mun, sannan na wuce sama domin tafiya nawa side ɗin, amma ina ganin Mama da su Adda Halima sai bina da harara suke yi.

Ajiyan zuciya nayi na saka hannu na sha re hawayen ido na, sannan na dubi Amaal nace, “Amaal nima ina so naga ina rayuwa da Mama na da Baba na da ƴan’uwa na, ina son naji ya ya kuke ji, amma Allah bai nufa ba, bani labarin ki da Dr Abdallah”.
Na faɗa ina ƙara sha re hawayen da yaƙi tsaya mun.

“Dr Abdallah tun ranan da muka zo registration Abbu ya haɗa ni da shi a matsayin Dr na, kuma tun lokacin na fahimci ya faɗa cikin soyayya ta, amma ban ƙarasa fahimta ba, sai da nayi ciwo na tafi gida, ya kasa zama ya bini har ƙasan mu, duk da shima ɗan can ne kuma cikin gari ɗaya muke, amma nasan ya yi haka ne don ni, soyayya ce kawai zai kawo haka, sannan wannan kwanciya ta ɗin ya nuna mun babu wata mace da ya ke so da tausayi iri na, ranan farko yace mun, ya kamata na auri likita domin na dinga samun kula, sannan ya dawo yace shi zai sama mun wanda zai kula dani, washe gari yace duk duniya shi zai fi bani kula saboda haka ya zaɓa mun kanshi don ya kula dani, ai dai baki ji yace so na yake yi ba, amma kuma yanzu ni da shi mun san soyayya muke yi, ke kuma abunda kika kasa fahimta da Dr Hussain kenan, yana miki son da ko a gaban waye sai ya nuna, amma ke duk bai ishe kiba kinfi son yace yana son ki kije kiyi tunani bayan 2 days ko? Irin yadda su Ummi suka yi da ko?”.
Ta faɗa tana harara na.

Bansan lokacin dana kwashe da dariya ba, duk wannan ɓacin ran lokaci ɗaya naji ya gudu, duk dariya muke yi ni da Amaal, sai naji waya ta ta fara ringing, da sauri na jawota ina dubawa, ganin sunan Dr Hussain ya saka ni zaro ido na duban Amaal.

Harara ta mun taja duvet ta shige ta bar ni, haka na ɗauki wayan yana dab da tsinkewa,
“hello babyn Baby ba kiyi bacci bane?”.
Naji yana tambaya na da wani irin murya wanda baza ka taɓa cewa muryan shi bane.

Lumshe ido nayi a hankali na furta,
“na kasa bacci saboda bansan ko Baby ya yi bacci ba”.
na faɗa ina jin yadda zuciya ta ta ke bugawa da sauri da sauri, saboda ban taɓa tunanin baki na zai iya furta haka ba.

Daga in da Dr yake ya tashi ya zauna, murya ƙasa-ƙasa yace, “da gaske?”.

“iya kacin gaskiyan da yake zuciyata kenan my Dr”.
na sa ke tabbatar mishi.

Ajiyan zuciya ya yi yace, “Baby ina son ganin ki wallahi yanzu a gaba na, Baby bugawan zuciyata yana ƙaruwa, Baby ki leƙo na gan ki don Allah”.

Runtse ido na nayi saboda yadda na kejin muryan shi yana rawa, a hankali nace,
“Baby ni sai dai kazo ka ɗauke ni wallahi tsoron fitowa nake yi ni ɗaya, kuma ni sai nagan ka kafin nayi bacci”.
na faɗa ina mishi sheshsheƙan kukan ƙarya.

“Ba,,byy,yy!” Yaja sunan da ɗan sauti sannan yace, “bana gajjiya da ganin ki, bana gajjiya da jin muryan ki, ki fito na ganki kin ji”.

Tashi nayi wayan na riƙe a kunne na ina ta sauƙe mishi buhun shagwaɓa har nazo jikin ƙofan parlon na tsaya, ina jin shi ya buɗe na shi ƙofan ya ƙaraso, sai na kasa buɗe ƙofan, shi kuma sai magiya yake ta mun, ganin nayi da shi ya koma ya ƙi kawai sai na saka hannu na buɗe ƙofan, kallon shi nayi sanye da wasu kayan bacci cotton masu masifan kyau, three quater da riga mai kyau, ƙafan shi sanye da wani silifas fari, ido ya ƙura mun wayan shi yana kare a kunnen shi, har lokacin bai yanke ba, nima ina kallon idon shi ban yanke wayan ba, naji yace,

“Baby’n baby!” ta cikin wayan, ina kallon shi nace, “baby nerh!”. runtse ido yayi.

MUM SAYYEED GA KYAUTAR WANNAN SHAFIN,BAWAI DON YA ISA YA NUNA MIKI IRIN ƘAUNAR KI DA MUKE YI NIDA BESTY BA, KO ƊAYA KINFI KYAUTAN LITTAFI GUDA MA A WURIN MU, KINA NAN CIKIN RAN MU, MUNA MIKI SON SO.

Plsss keep following, commenting, voting and sharing.
Love you all my fans❤️😘.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here