ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 15
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
_*NANA FIDDAUSI, ƊIYAR JIKAR KULU WANNAN SHAFI NA KINE KYAUTA, ALLAH YA ALBARKACI RAYUWAR KI, YA KAWO MIKI ƘANNE MASU ALBARKA*_
*SHAFI NA 15📑*
*__________📖* Kan bed ɗina na faɗa ina kuka mai zafi a zuciya, ni na rasa me yasa na damu da sai Dr ya yaba ni, bayan nasan ba zai ta ɓa yabawa ba, gara ma nayi haƙuri kawai, ina cikin kukan naji an buɗe ƙofan ɗakin an shigo.
Dafa baya na naji anyi, wanda daga dukkan alamu Ummi ce, ban ɗago na kalle ta ba, amma na rage sautin kukan nawa.
“Tashi Aisha Humaira muyi magana kinji”.
cewar Ummi, tashi nayi zaune ina ta sauke ajiyan zuciya.
Hannu na ta riƙe gam a cikin nata tana duba na cikin nutsuwa, a hankali ta jeho mun da tambayan da ya kusa sakani dariya, “Humaira kina son Dr ne?”.
Kallon ta na yi kaman zanyi dariya nace, “Ummi son Dr kuma? Ni kam ban taɓa jin son shi ba, ni Ummi ba bu wanda na taɓa so a duniya irin Daddy na, sai kuma Amal da na ke son ta, ni bayan su bana son kowa”.
“Har maman ki baki son ta?”.
Kallon ta na yi ido na yana cikowa da hawaye, juyar da kaina nayi gefe sannan nace, “Mama na ta rasu”.
Jawo ni jikin ta tayi ta rungume ni saboda ganin hawayen da ya fara gangaro mun, a hankali tace,
“Allah ya jiƙan ta da rahma, Allah ya ƙara miki haƙuri da juriya na rashin ta”.
ni dai ban ce komai ba ina dai kwance a jikin ta nayi shiru hawaye yana bin fuska na, tun ranan da na bar ƙasar mu na daina zubar da hawaye na rashin Mama na, amma yau kuma kewar ta ya dawo mun zuciya ta mai rauni.
_*ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU DA SU KA RIGA MU GIDAN GASKIYA, TABBAS RASHIN UWA WANI BABBAN MIKI NE WANDA BAYA CIKEWA, DUK WANDA TAYI RAYUWA BABU UWA GASKIYA ABUN TAUSAYI CE 😭😭😭ALLAH KA KAI HASKE A KABARAIN MAMA NAH!* 👏🏻👏🏻
“A hannun wa kika tashi?”.
ta jeho mun wani tambayan kuma.
“Hannun Daddy nah da matar shi wanda muke ce mata Mama, tana da yara guda uku, Yaya Ahmad shine babba a cikin yaran ta, sai kuma Yaya Aliyu shike bin shi, sai Yaya kabir shi ne ƙara min su, shi kuma ya bani 2yrs, yanzu haka yana karatu a ATBU, ni kuma ni kaɗai Mama na ta haifa, kuma ni kaɗai ce ƴa mace a wurin Daddy nah, shi yasa ya ke sona sosai”.
na faɗa hawaye yana ɗan bin fuska na kaɗan kaɗan ina sharewa.
“Hummy tunda kince ba son Dr ki ke yi ba, to zan baki shawara a matsayi na na mahaifiya a gare ki, daga yau ki daure ki daina damuwa idan baice kina da kyau ba, ko baice kin iya abinci ba, yaga kin damu ne shi yasa yake bawa zuciyar ki wahala, saboda duk ranan da ya tunkari zuciyar ki bazai samu matsala ba, saboda ya gama lugwaigwaita ta da soyayyar shi, kowa ya ganki yasan tsakanin larabawa da indiyawa sai anyi da gaske a samu mai irin kyaun ki, saboda ranan da na fara ganin ki na ɗauka aljanu ne zasu buɗe mun ido, Humaira ke ɗin ɗiya ce mai kyau da daraja, kada ki yadda da ga yau Dr ya sa ke saka ki kuka kin ji, daga yau ki nuna mishi baki son yabawan shi tunda ke mai kyau ce, kuma kin iya girki mai daɗi da, domin ina hankalce da shi, lomar farko da yafara yi sai da ya lumshe idon shi don daɗi, saboda haka ko ya faɗa ko kada ya faɗa, girkin ki ya mishi daɗi”.
ta faɗa tana mun murmushi, saboda ganin nima na ke ta murmushi.
“Humaira kin ji daɗi ne da nace miki yaji daɗin girkin?”.
Dariya nayi ina ɗaga mata kai alaman na ji daɗi.
Lumshe ido tayi ta buɗe a hankali, a zuciyar Ummi tana jin tausayi na, domin tasan babu yadda za tayi na riga da nayi nisa a son Dr, sai dai fatan Allah yasa shi kuma ya riƙe amana, tasan komai zai ta gaya mun ba zaiyi tasiri ba, saboda bani da wayon da zan fahimce ta, saboda shi wayo bawai a shekaru bane, kawai baiwa ne, wasu kuma zama da iyaye suna nusantar dasu abinda ya kamata shi ke sakawa su fahimci rayuwa, wasu kuma irin mutanen da suka zauna dasu yake sakawa su fahimci rayuwa, amma abin tausayi tasan ni nayi rayuwa ne da giɓi na rashin uwa.
“Ummi to ya ya ake jin so ɗin?”.
Na jeho mata tambayan da ba ta yi tsammani ba.
Shiru tayi na wani lokaci, sannan ta ɗago ni zaune tana duban fuska na,
“zaki na yawan tunanin mutumin, Za ki na yawan jin kishin wata akan shi, za ki na yawan jin tausayin shi, Za ki na son kina yawan ganin shi, ba za ki na gajjiya da jin muryan shi ba, Za ki na so kiga komai ki ka yi ya yabe ki, Komai aka faɗa na laifi akan shi baza kina gani ba, zai zama kullum hasken shi ki ke gani
Za ki na ……”.
abubuwa da yawa Ummi ta lissafo mun akan yadda za ka ji kana son mutum.
Da sauri na dafa zuciya ta ina lumshe ido na, duk wani tsoro naji ya kamani, a hankali na sa ke buɗe ido na ina kallon Ummi, “Ummi daga shekara nawa ka ke ji ka fara son wani?”.
Dariya ta yi mai ɗan sauti, sannan ta dube ni tace ” soyayya bata da shekaru, ba ta da lokaci, ba ta shawara, bata zaɓe, duk lokacin da Allah ya hukunta za ka fara to babu makawa ko kashirya mata ko baka shirya ba zaka fara”.
“Na shiga uku Ummi, to wallahi zuciya ta tana son Dr Hussain, amma ni kam bana son shi Ummi”.
na faɗa ido na yana cikowa da hawaye, saboda gaskiya ni ban shirya yin soyayya ba, kuma bamuyi haka da Daddy na ba.
“To ita kuma zuciyar ki ta shirya karɓan soyayya’n Dr, to ya ya za kiyi kenan?”. Cewar Ummi.
“Ummi ni kam bana son shi”.
“Me yasa baki son shi? Yana da wani problem ne?”.
“Ummi ni fa saurayi na ke son aure kuma yaro iri na, amma shi fa yana da mata, kuma ya yi mun tsufa, kuma Daddy yace mun kada nayi soyayya da kowa saboda maza basu da kir ki”.
Shiru Ummi tayi har zuwa wani lokacin tukun tace, “to ai ke baki da Laifi, tun ke baki san kin fara son shi ba, kawai yanzu abu ɗaya za kiyi ki kare kan ki”.
Da sauri nace “me zanyi Ummi”?
“Kada ki gayawa kowa kina son shi, ko da Amal ce, shima kada ki bari ya gane kina son shi, don zai gayawa Daddy’n ki, itama Amal idan taji zata gayawa Abbu’n ta, shi ma zai iya faɗawa Daddy’n ki”.
zaro ido nayi ina duban ta da tsoro, sannan a hankali murya can ƙasa nace, “Ummi to ai bazan taɓa gaya mishi ina son shi ba, ban ma san ina son shin ba”.
na faɗa kaman zan yi kuka.
“Yauwa ɗiya ta Hummy, kada ki bari kowa ya sani, shima ki daina damuwa da matar shi, ki dena damuwa da sai yace kina da kyau ko kin iya abinci, amma kiyi ta kwalliya da abinci mai daɗi kina bashi yana ci, kuma kada kina shiga gidan shi ke kaɗai, kina zuwa tare da ƴar’uwar ki Amal kuna kai mishi, ina miki albishir wataran da kan shi zai furta miki kin fi kowa kyau, amma sai kin kama kan ki, ki daina nuna kin damu da komai, kuma idan mun tafi duk abinda ya shige miki duhu ki kira ni ki gaya mun, ni kuma na miki alƙawarin warware miki komai kin ji doughter na”.
Abun tausayi yau jirgin ƙarfe 12:00pm na dare su Abbu suka tashi, ba Amal ba har ni sai dana yi kukan tafiyan su, saboda tun da nazo duniya ban taɓa jin na shaƙu da wata mace ta nuna mun ita uwa bace a gare ni sai ita, gara-gara kakanni na guda biyu duk sun nuna mun ƙauna, wanda ta haifi Daddy na ina primary 6 Allah ya mata rasuwa, amma ina tuna yadda ta ke masifa idan an mun abu ba dai-dai ba, sai kuma wanda ta haifi Mama na, duk da ba wani yawan ganin ta na keyi ba, saboda bata ƙasan, sai tayi shekaru kafin ta zo, amma duk ranan da tazo gani na takan nuna mun soyayya kaman ita ta haife ni, amma Daddy baya taɓa barin ta ta tafi dani gidan ta, haka kuma bai taɓa sakawa ta nuna ɓacin ran ta ba, saboda a gidan mu gefe na daban ne, in da ya zama na Mama na shi aka gyara mun, ina tare da masu mun aiki, so ko tazo ma takan iya wuni guda bata ga Matar gidan ba, a sake muke zama da ita.
Basu bar mu mun rakasu airport ba, saboda yanayin jikin Amal, basu suka dawo ba sai wurin after 1, domin naji shigowan motan Dr Hussain.
Da safe bayan mun yi wanka, sauri-sauri na soya mana egg muka sha Tea da bread da shi, haka muka fito domin tafiya school.
A waje muka haɗu da Dr Hussain yana tsaye jikin motan shi, daga dukkan alamu mu ya ke jira, rufe ƙofan mu nayi, sannan muka ƙarasa in da ya ke tsaye, gaishe shi muka yi amma ban kalli idon shi ba, sai dai a jiki na naji ni ya ke kallo, tuna maganan Ummi nayi kada na bari ya gane na damu da shi, ina tuna hakan nayi saurin na buɗe sit ɗin baya na zauna, ƙura mun ido suka yi daga shi har Amal, amma naƙi kallon su, sai gyara books ɗi na da suke cikin bag ɗina kawai na keyi.
Ganin zamu ɓata mishi lokaci gashi ni ban fito ba, ita kuma Amal bata shiga ko’ina ba, sai yayi sauri ya dube ni yace “ya ya kika zauna a baya?”.
Ina kallon books ɗina nace, “ai duk ɗaya ne da zaman bayan da gaba, ga Amal ta zauna a gaba kada mu mayar da kai driver bayan kai lecturer mu ne”.
Shiga ta yi ta zauna, haka yaja motan babu wanda ya sake cewa uffan acikin mu, muna isa Department ɗin mu nayi sauri na riga fita a motan domin na hango su Ezeh zasu shiga class ɗin mu, da sauri na isa in da suke muka tsaya muna gaisawa, sannan na jira Amal ta ƙaraso in da nake muka wuce class.
Muna zama akayita zuwa ana gaishe ta, bayan kowa ya koma sit ɗin shi ta dube ni tace, “me yasa ki ka yi haka Hummy?”.
“Me nayi kuma yau?”.
Hmm tayi tsaki tana harara na tace, “meye ana cewa ki dawo front sit ɗin ki zauna ki ka ƙi? Bayan kinsan ke ya kamata ki zauna a wurin”.
“wani irin ni ya kamata na zauna? Yadda Dr ya ke malami na kema fa malamin kine, yadda Daddy ya bashi amana na, kema fa naki Parent ɗin sun bashi, yadda yake neighbour na kema yanzu ya zama naki, duk ɗaya yake a wurin mu, kuma ɗaya muke a wurin shi”.
Tsaki ta sake ja sannan tace, “amma dai kinsan da ke yafara sabawa ko”.
“kema zaku saba sosai, yau da gobe ne ai babu wuya, kuma daga yau ke zaki dinga zama a gaban motan saboda ku saba kema da shi”.
ina faɗa na juya na bar maganan da mu keyi haka.
Ranan yana shiga mana lectures duk ya maida hankalin shi kaina, duk abunda ya ke yi idon shi yana kaina, sannan tambaya ɗaya zai jeho mun, amma tashi na keyi na mishi bayani babu wani tsoro ko shakku a ciki.
Muna tashi na ɗauko mana handbags ɗin mu har dana Amal muka fita domin tafiya gida, a zaune a cikin motan muka sa me shi, yana ganin mu ya ƙura mun ido, amma sai nayi kaman ban ganshi ba, na kawar da kaina gefe har muka ƙarasa jikin motan, buɗe bayan nayi na shige ,ita kuma Amal ta buɗe gaban motan ta shiga.
Ina ɗaga kaina naga ya sauke mun wani mummunan harara ta madubin motan, murguɗa mishi baki nayi na kawar da kaina, jijjiga kanshi yayi irin alaman zai haɗu da ni, kallon Amal ya yi yace,
“Amal zaku iya dafa wani abu ko muje mu yi take-away?”.
Juyowa ta yi ta dube ni, tana jiran taji me zance, ni kuma ganin haka ya saka na harare ta na mayar da kaina window ina kallon waje, ganin haka yasa ka ta juya tace,
“yanzu yunwa muke ji, ina ga muna yin take-away da lunch, idan yaso breakfast da dinner sai mu dinga yi da kan mu”.
ta faɗa tana juyo tana kallo na.
“Hakan ma ya yi, amma maganan breakfast kam ai baku san mun, sai dai naji ƙanshi ana soya abu, saboda haka dinner ma ina tsoron na saka a raina zan samu”.
ya faɗa yana kallo na ta glass ɗin motan.
Dariya Amal tayi sannan tace, “kayi haƙuri wallahi yau mun makara ne, egg kawai Hummy ta soya mana, muka sha da tea, amma insha’Allahu zamu dinga yi da kai daga yau, kuma dinner ma da kai zamu dinga yi”.
Take-away yaje ya mana, muna isowa gida Amal ta ɗauki ledan da ya miƙa mata, ni kuma na ɗauki bags ɗin muka fito, har nayi kusan ƙarasawa ya ƙirani, dawowa nayi wurin shi, kallo na ya yi ganin bance komai ba yace, “wani abu yana damun ki ne?”.
Turo baki na nayi gaba kaman bazan yi magana ba, can kuma na dube shi ganin irin kallon da ya ke bina da shi nayi saurin sauke ido na ƙasa ina jin faɗuwar gaba, “ni babu abinda ya ke damu na”.
“To me na miki ki ka ƙi zama a front sit yau?”.
Ina duban shi nace, “ba Amal ta zauna ba”.
“Amal ɗin na saba da ita ne?”.
ya faɗa yana hararana da wasa.
Ɗan ya mutsa fuska na nayi sannan nace, “ita ma ai zaku saba, ni yunwa na ke ji sai anjuma”.
ina faɗa na juya na bar shi a tsaye a wurin.
Kasa ɗaga ƙafan shi ya yi ya bar wurin saboda mamakin irin yadda na mishi, ko kulawa na ƙi nuna mishi yau, sai yaji babu daɗi a ranshi.



