*NA MARUBUCIYA:-**AUNTY NICE*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-**NABEELAH ARABI**NUHU ARABI*
*SHAFI NA 13*
* Ni dai ban san me ya faru ba, sai farkawa na yi cikin dare naga waya ta a yashe a gefe na, murmushi na yi ni ɗaya wayan na ɗaura a bedside drower, wato bacci nayi Dr yana mun waƙa ko? Kaɗa kai na nayi na shiga toilet.
Bayan na idar da sallan asuba, kitchen na wuce na zauna na fere dankalin, sannan na soya na soya ƙwai da plantain, na so na yi peppesoup, amma ganin babu time yasa kawai na kai musu kan dinning na ajiye ketchup a kan dinning ɗin, flasks na cika da ruwan lipton mai kayan ƙamshi, ina gama jerawa nayi sauri na shige toilet na yi wanka, gudu-gudu na fito na shirya, sannan na ɗauki breakfast ɗin kaɗan naci, note na ɗan rubutawa su Ummi sannan na ɗauki handbag ɗina na wuce zuwa school.
Ina fitowa na haɗu da Dr shima ya fito zai wuce school ɗin mu, murmushi yamun nima na mayar mishi, ƙarasowa yayi har in da na ke, sannan ya buɗe mun front sit na shiga, shi kuma ya zagaya wurin zaman driver.
Yana ta da motan na gaishe shi, yana kallon kan hanyan ya amsa, sannan ya tambaye ni ya ya baƙi na suka kwana? Ina murmushi na ce mishi, “lafiyan su ƙalau, amma basu fito ba na fito yanzu”.
“Break fast fa, kin musu dai ko”?
Ɗaga kai nayi alaman ehh na musu.
“Ni ne kawai ba kiyi dani ba ko?”. Hannu na saka na rufe baki na ina dariya.
“Hmmm dole kiyi dariya mana, tun da kin cika cikin ki ni kuma kin barni da yunwa, amma babu komai zanje wurin khadija nasan zata soya mun egg nasha da tea”, ya faɗa yana murmushi.
Hararan shi nayi na turo baki na gaba ina ta ƙunƙuni.
“Ki faɗi abinda ya ke bakin ki zaifi miki sauƙi, amma harara na ba zai miki sauƙi a ranki ba”.
“Ni bance komai ba, tun da nasan matar ka bata iya girki ba, hala ma idan taje soya ƙwan ya ƙone bata san yadda akeyi ba”.
Dariya ya yi ya na shiga gate ɗin school ɗin, juyowa ya yi ya kalle ni bai ce komai ba sai murmushi, yana ta rawa da kanshi yana murmushi yana kallo na.
Muna isowa ƙofan department ɗin mu ya yi parking idon shi yana kallon wani wuri yana munafukin murmushi.
Hararan shi nayi a hankali na dubi in da ya ke kallon, Dr Khadija ce tsaye tana rufe motan ta, gefen ta kuma wata friend ɗin ta ce a tsaye suna magana, dawo da kallo na nayi kanshi, buɗe motan nayi na fita bata re da na ce mishi komai ba, ganin saura 15mnt a shiga mana class nayi sauri na ƙara sa class ɗin da muke lectures, ina ganin yadda Dr Khadija da ƙawar ta suka bini da kallon mamaki, haka ma wasu daga cikin students da lecturers suka dinga bina da kallon mamaki.
Ina wucewa shima ya fito bayan yayi parking motan shi, ko kallon in da suke bai yi ba ya wuce office ɗin shi, ganin haka yasa Dr Khadija bin bayan shi da sauri ranta a ɓace, duk ƙiran da ƙawarta ke mata bata kula ta ba, ita dai sauri kawai take ta iso shi taji dalilin shi na ɗauko ni a motan shi.
Ina shiga class ƴan class ɗin mu suka yi ta tambaya na ina Amal, wasu na gaya musu bata da lafiya, wasu kuma na sha re su ina duba note ɗin cost accounting da Ezeh ya miƙo mun, kuma ina maida hankali na kaɗan kanshi da naji shi ƙasa-ƙasa yana ce mun.
“Beauty dama Dr Hussain brother ɗin kine ko?”. Ina kan buɗe note ɗin ban kalle shi ba nace, “Uncle ɗina ne, shi ɗin ƙanin Daddy na ne”.
“Heyyyy no wonder mana naga yana tolerating ɗin ki, kaman wancan ranan da ki ka ba shi haƙuri ai ya dawo ya ci gaba da lectures, so yanzu kawai kice zan kama ƙafan ki don gaskiya bana son na faɗi a course ɗin shi seriously, kinsan 4 credit unit ne, kuma ga shi shine *PROGRAMME CO-ORDINATOR* Namu, don ma naji ance Professors ɗin nan ake bawa Heads of Departments, amma da an bashi na department na mu, saboda ƙoƙarin shi a department ɗin”.
haka muka yi ta magana akan course ɗin, kafin lecturer su fara shigowa.
Dr Khadija tana shigo mana ranan naga bala’in ɓacin rai kwance a fuskar ta, sai wani ɓata rai ta keyi kaman an saka ta dole, kuma tambaya ɗaya zata ɗaga ni tayi mun, abinda na lura nema ta keyi ta ga gazawa na, amma daya ke ni ɗin ba kanwar lasa bace, sai ta kasa samun in da zata ƙure ni, domin idan ba yabon kai ba, idan ku ka cire Ezeh to duk class ɗin ba zaka samu na sama dani ba, amma baza kasan hakan ba, sai an taɓo ni, saboda ni karatu na bana nunawa mutane bane.
Tana gamawa ta dubi ƙofa dai-dai lokacin Dr Hussain ya iso, dawo da kan ta tayi ta dube ni, fuska a ɗaure cikin shegen haɗaɗɗen turancin ta kaman na tsohuwar baturiyar england tace na sameta a office after na gama lectures.
Bance mata komai ba sai bin ta da ido da nayi ta tayi har ta bar class ɗin, a lokacin Dr Hussain kuma ya shigo, ina ganin shi ya kauce ma ta ta fita, domin da yi tayi kaman zata bangaje shi, amma ba zaka gane ya ya yanayin fuskar shi yake ba, saboda babu yabo babu fallasa akan face ɗin shi.
Tun da ya fara lectures bai kalli in da nake ba, sannan idan ya yi question baya duban in da na ke ballanta na ya mun tambayan, haka ya gama lectures ɗin shi, yana gamawa ya tako har in da na ke zaune, yana kallon cikin ido na yace,
“kada na yadda naga kinje ƙiran da Khadija ta miki kin ji ko”. Ɗaga mishi kai nayi alaman naji.
Yana duba na fuska a ya mutse yaɗan sunkuyo da fuskan shi saitin in da nawa ya ke yace,
“yunwa na keji Babyn baby”.ya ƙarasa faɗi kaman zai mun kuka, juyawa nayi da sauri na dubi ƴan class ɗin amma sai naga duk idon su yana kan mu.
ya mutsa fuska na yi ina nu na mishi alaman ana kallon mu fa, amma sai ya wani ɗaga kafaɗa irin ko ajikin shi, ya sa ke sunkuyowa ya kwaikwayi murya na yace, “Baby yunwa, wayyo babyn baby”.ya faɗa yana ɗaura hannun shi akan cikin shi.
Dariya nayi na miƙe tsaye ina kallon shi, a hankali nace , “to muje gida na soya maka egg ɗin da singulura ta kasa yi maka, muje na samu ladan ka”. yana dariya shima ya biyo baya na muka fita a class ɗin.
Ko sauƙa a brandan class ɗin ba muyi ba muka ji ihu da buga desk da ƴan class ɗin suka yi, ina jin muryan wani yana cewa wallahi girl friend ɗin shi ce, Ezeh yana ta rantse musu akan uncle ɗina ne.
Kallon Dr nayi baki na a buɗe ina nuna mishi yaji mai ƴan class ɗin suke cewa, shima dariyan yayi ya dawo kusa dani yana cewa, “To girl friend ɗin ne ko ni Uncle ɗin ki ne?”.
Tsayawa na yi da tafiyan ina kallon shi cike da mamaki nace, “kai kuma sai ka biyewa abin da zasu ce maka?”.
“To ya ya zan yi da rigan da babu wuya? Nikam kawai yau baki isa ba sai kin gaya mun waye ni a wurin ki”.
“Nikam ba bu ruwa na Dr, kai kawai Dr’n mu ne, kai malamin mu ne”.
“ni dai baki isa ba sai kingaya mun a tsakanin abin da su ka tambaya”.
Hararan Aunty Faraa nayi don ganin Hummy zata mishi bayani ita kuma ta wani daka tsalle tana ihu tana cewa, “sai Dr da Hummy Allah ya bar ƙauna ta gaskiya”.
da sauri Miss Xerks ta jawota da ƙarfi tace, “to kin yiwa kan ki, gobe baza mu ta ho da ke ba, kuma yau zan saka *NEAT LADY* ta turo jet ɗin ƴan gaskiya writers a koma da ke nigeria, saboda ihun nan da kika yi gashi kin sa ka sun yi shiru suna kallon mu”.
Juyowa ta yi tana duba na irin na hana Miss Xerks sakawa a maida ta gida, hararan ta nayi nace, “wallah komawa za kiyi yanzu yanzu ma, tun da ihu za kiyi a dinga jinmu, da naso ranan da za ace………”.
*DR MOSES*
Daga marubuciyarBadariyyahƘaddara ta riga fataAna barin halal…
*AUNTY NICE*
Fatie kiyi haƙuri ki yafe mun, kije gida na sakeki saki biyu, ba wai kin mun laifin komai ba, sai dai mahaifiyata ta ce zata tsine mun idan ban rabu da ke ba, ina miki fatan Allah ya share miki hawayen ki da miji nagari wanda ya fini, hawaye ne yake zuba mun kaman an kunna ruwan pampo, ido na yana kan mijina farincikin zuciyata.
Fatie!!! Maganan auren mu dake gaskiya bazai yiwu ba, duba da yadda matata ta tayar da hankalinta dangane da maganan auren mu, ina ga idan na aureki zata barni, ni kuma ina sonta ban shiryah rabuwa da ita ba, saboda haka ke kiyi haƙuri na haƙura.
Fatie!!! maganan sadaki da aka kawo kiyi haƙuri na bar miki shi, bawai don kin mun komai ba, gaskiya auren ne nake jin bazan iya yin shi ba yanzu, idan Allah ya baki miji kiyi aurenki, idan da buƙatan wani abu ki mun magana nagode da ƙaunar ki gareni.
Fatie!!! idan kinaga akwai sarari ki sama mun wata mace mana mai kyau kamar ki, ke ina ga aure na dake bazai yiwu ba gaskiya, idan kuma zaki iya zuwa wurina Abuja sai na biya miki kuɗin jirgi babu matsala, ko hira sai ki zo muyi.
Kuka na tsuguna ina yi sosai a gaban mahaifina da mahaifiya ta da kuma yayah na, duk zagin da suka mun da nasihar da suka mun banji a zuciyata zan daina son Dr moses ba, banji kuma bazan aure shi ba, tou ina ma zan samu wanda yayi na’am da ni irin shi?
Moses baka da hankali ne? Yayah zakace zaka auri yarinyar fulani musulmah? Kana tunanin zata yadda ta aureka kana christan ne bata saka ka musulunta ba? Ko so kake ka chanja addini akan mace?
Ɗago kyawawan idon shi yayi ya zubawa ƴar shi Fatie da ta ke ɗaga mishi hannu bayan ya ajiyeta a islamiya, murmushinta da yake nuna tsantsar kamninta da mahaifiyarta kawai yake gani a fuskar ta, zuciyar shi yana mishi suya da tunanin Mummy fatie.
Juyawa maman moses tayi ta dubi ƴar da moses yake riƙe da hannunta mai tsananin kyau da dogon gashi, ko taƙi Allah lokaci ɗaya taji son yarinyar ya shiga zuciyarta a farar ɗaya, amma kada moses yayi tunanin ta karɓe shi ne shi da ƴar shi yasaka ta juyar da kanta fuskanta a ɗaure ta dubi baban moses daya ɗauko bindiga ya saita moses da ƴarshi fatie, amma kuma ya kasa aywatar da komai sai kallon yarinyar da take duban shi fuskanta ɗauke da murmushi tace, “kaka ka iya wasa da Gun ne”?
Hawaye ne ya zoba a fuskar moses, idon shi akan fatie da ita ma take ta kuka kaman ranta zai fita, bayan ta gaya mishi yadda sukayi da iyayenyta game da ƙin yadda da sukayi akan aurenta da shi. “Fatie ar ga Allah ina sonki, ina sonki da raina ne bada zuciyata ba, kuma bazan taɓa barinki ba ko da za’a tayar da garin bauchi ne da garin jos kuwa”.
Littafin Dr moses shima akwai chakwakiyar soyayyah a ciki.
*AUNTY NICE* 😘✍🏻




