ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 12
*NA MARUBUCIYA:-**AUNTY NICE*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-**NABEELAH ARABI**NUHU ARABI*
_*SADAUKARWAR PAGE ƊIN NA KUNE, HAFSAT ISAH PZ & HAUWA MUSTAPHA JAJERE A (Gaskiya Fans H) KUYI YANDA KU KE SO DA SHI, INA JIN DAƊIN YANDA KU KE SON WANNAN NOVEL ƊIN, SABODA HAKA MA BESTY NAH (Miss Xerks) TA CE NA GAISHE KU BOHOT-BOT… Kuji daɗin karatu lafiya.*_
*SHAFI NA 12
Daga Abbu har Ummi sun ji daɗin karramawar da na yi musu, bayan munga ma dinner ta re da su, Abbu ya maida hankalin shi kan kallon News da ake yi na ƙasan, ni da Ummi kuma kaman wanda mu ka shekara muna tare, sai hira muke yi na rayuwar Amal da irin wahalar da ta ke sha.
“Ummi to me zai hana Amal ta dawo wuri na mu zauna tare? Saboda yanayin ciwon ta ina ga bai dace ta zauna ita ɗaya ba, saboda wataran ina ga baza ta iya samun sararin yiwa Dr waya ba, ko me ki ke gani Ummi?”.
Na faɗa ina matsawa jikin ta, tsabar samun wuri irin nawa, dama asali ni mai son naga ana nuna mun kulawa ne, domin duk ranan da kaka ta tazo gidan mu ko naje wurin ta, sai Daddy yayi ta mana shari’a, zata yi ta mitan ina tumurmusan ta, amma ina primary 6 Allah ya yi mata rasuwa, Allah ya jiƙan ta da rahma.
Abbu ne ya juyo ya ƙurawa Ummi ido don jin mai za ta ce, amma sai Ummi naga ta sunkuyar da kanta ƙasa kaman mai tunani, har tsawon wani lokaci sai ta ɗago tace,
“Humaira ba wai naƙi shawaran ki bane, iyayen ki ina ga ba lallai ne su yadda ba, and secondly kuma ciwon Amal ba ita kaɗai ba, duk wanda ya raɓe ta ma sai ya sha wahalar jinya, keda aka kawo ki karatu, ai bai kamata mubar ki da jinyan Amal ba”.Ummi ta faɗa tana share guntun hawayen da ya biyo idon ta.
“Ummi Daddy na ba shi da matsala bazai hana ba, shima kullum sai yace tausayi na ya keyi na zama na ni kaɗai, kawai babu yadda ya iya ne, ciwon Amal kuma kawai nawa idan ya tashi ne na ƙira Dr ya tafi da ita asibiti, tun da asibitin su ba zama akeyi a wurin ba, ba kai musu abinci akeyi ba, komai acan ake musu, kinga ai babu wani matsala, bana son ta zauna ita ɗaya ne”.
Abbu ya yi gyaran murya yace, “Humaira bani number shi mahaifin kin, nima nayi tunani irin naki tun da muka shigo gidan nan, idan Allah yasa ya amince ni zan fi samun kwanciyar hankali ma”. ya faɗa yana miƙo mun wayar shi.
Da sauri na amshi wayar tsabar murna jiki na har rawa ya ke tayi, number Daddy na juye mishi, na miƙo mishi ina ta murmushi.
Bai daɗe wayan yana ringing ba naji muryan Daddy yana sallama, alamar ya ɗauki wayan, Abbu ne ya fara gaishe shi, sannan ya mishi bayanin shi ne mahaifin Amal ƙawar Humairah, Allah sarki Daddy daga muryan shi za kaji yaji daɗin ƙiran da Abbu ya mishi, tambayar jikin Amal ɗin yayi, Abbu cikin farin ciki da jin daɗin an nuna kula akan ƴar ta shi ya amsa da sauƙi, sannan Abbu ya gayawa Daddy manufar ƙiran shi da ya yi.
Daddy ma ya nuna jin daɗin shi in da ya ke cewa Abbu ai daman kulum zama na ni kaɗai tausayi na ya ke ji, don ma ya bada amana na wurin Dr Hussain ne ya samu ɗan sauƙin tunanin abun, amma ai bakamar yadda zasu zauna su biyu ba, don kuwa zata daina jin kaɗaici, kuma za suyi karatu tare.
Daddy yace mishi kuma zai yi bayani wa Dr Hussain ya saka musu ido sosai a rayuwar su da kuma karatun su, duk da kullum alkhairin mu yake gaya mishi, shima Abbun yace insha Allahu kafin ya tafi zai sake samun Dr Hussain ɗin, haka suka yi sallama kaman wanda su ka daɗe da sanin juna.
Kallon mu Abbu yayi yana murmushi, ya jawo flask yana zuba shayi mai cike da kayan ƙamshi, irin su citta da su kanamfari,
“wato Humaira ina ga a wurin mahaifin ki ki ka gaji karamci, mutumin nan bai san wacece Amal ba da kuma iyayen Amal amma ya amince ku zauna tare, domin shi ɗin ɗan halak ne”.sannan ya mana bayanin duk yadda su kayi da Daddyn, kowan mu sai farin ciki ya ke yi.
Ina kallon Ummi nace, “Ummi gobe zanje na kwaso kayan Amal ɗita, ina dawowa a school”.
Ummi tana mun dariya ta ce, “ki bari mana a sallame ta sai kuje tare, Ke kam ai gobe school ya kamata kije ki nutsu ki maida hankali a abinda za’a muku, ɗebo kayan kuma sai kubar shi sai weekend ko”.
Ɗaga kai nayi ina murmushi, sannan na ɗauki wayana da ake kirana, ganin sunan Dr Hussain sai ya sakani tashi na wuce bedroom ɗina.
Kan bed ɗin na hau na kwanta sannan na ɗauki wayan da ya sa ke shigowa a karo na biyu, manna shi kawai nayi a kunne na ba tare da nace uffan ba, sautin murmushin shi naji, sannan naji yace, “Babyn baby muna faɗa ne?”.
Turo baki na yi kaman yana kallo na, yadda kasan jikar kulu idan sun haura da amininta Hussain 80k, na yi magana ƙasa-ƙasa nace, “to ba kai bane ba”.
(Allah kajiƙan hussain 80k da rahma, 😭😭😭Allah sarki rayuwa, Na tuna sbd sabon mu da hussain 80k fah na saka sunan star ɗin book ɗin nan hussain, gashi yanzu mai rabawa ta raba, Allah yasa kana cikin rahma 80k nerh 😭😭😭😭)
“To kuma ba ke bace ba”.ya faɗa yana kwaikwayon murya na.
Dariya nayi a ɓoye ina rufe baki na, ya sa ke cewa, “kawai sai kice mata na kaman kwandon wanke-wanke, bayan irin kyaun ta da na ke gani bana tuna ita ɗin gajeruwa ce, amma yau kinsa na fara tunawa ashe fa da kaɗan tafi kwandon wanke-wanke”.
Ina dariya na ce, “Dr’n mu zaka daina son ta kenan?”.
“Idan na daina son ta wacece zan so? Ko zaki sama mun wata?”.
Rufe ido na yi ina jin daɗin da ban san meye dalilin shi ba, “To kace mun bata da kyau, kuma ka dai na son ta”.
“Tun da ki ka ce mun kaman kwandon wanke-wanke ta ke, sai na daina son ta, kuma na daina ganin kyaun ta”.ya faɗa shima yana jin daɗi da wani nutsuwa a ranshi daga in da ya ke.
Dariya na dingayi na daɗi wanda har sai da naji Dr ma ya fara dariyan, don yadda na kasa dainawa, ina wani jin daɗi a raina.
“Hummy’n mu kina jin daɗi ne?”. Ya tambaye ni murya a hankali cikin nutsuwa.
“Allah Dr’n mu yau daɗi na ke ji sosai, to yanzu zaka daina zuwa gidan ta ko? Kuma idan nayi kwalliya za ka ce ina da kyau?”.
Rufe idon shi ya yi daga in da ya ke yana ta murmushi, shi kanshi ya rasa yau wace irin rana ce a wurin shi mai girman gaske, shi fa ko lokacin da yake tsokanan ƙanwar shi Aisha baya samun jin daɗi da nutsuwa irin yadda ya keji yanzu idan ya zolayi Hummy, ɗari bisa ɗari Hummy ta canja mishi tsarin rayuwar shi, da ko kaɗan baya jin sakewa a zuciyar shi, idan bai yi ƙarya ba ya kan yi good 1yr wani abu bai saka shi dariya ba, amma yanzu kullum ne, kuma ko wani lokaci sai ya yi dariya ko da shi kaɗai ne idan ya tuno ta a ranshi, yanzun ma wani dariyan yayi sannan yace.
“To ai ke yarinya ce Hummy, bazan iya ganin kyaun ki ba yanzu, ki bari sai kin girma sai na duba naga kina da kyaun, abu ɗaya kawai nasani yanzu, Hummy ta mai hankali ce, Hummy ta mai baiwar ilimi ce, Hummy ta mai sakalci da shagwaɓa ce, Hummy ta mai rikici ne, wanda kullum sai ta birkita ƙwaƙwalwar Dr ta da rikici”.
“Uhmm ni kan ban yadda ba, wallahi na girma Dr ni kam kace ina da kyau, kace na fi ko wacce mace kyau, Allah Dr’n mu har na kusa iso ka tsayi fa, idan na ƙara 2yrs fa tsayin mu zai zama ɗaya”.
Yana murmushi mai sauti yace, “to mu bar shi ya kai 2yrs ɗin sai na gaya miki a lokacin”.
“To bazan sa ke kula ka ba sai lokacin, kuma kaima ba za ka sake kula kowa ba, sai ka jirani har lokacin”.Na faɗa kaman zan mishi kuka ta wayan.
“Wayyo Baby idan kin daina kula ni ae mutuwa zan yi, kullum kuka zan ta miki fa Baby”. ya faɗa shima yana kwaikwayo na.
Dariya ya sa ka ni sannan nace, “Ba zaka mutu ba insha’Allah sai na girma kace Humaira ta fi sauran mata kyau, Humairah tafi ko wacce macce iya kwalliya da girki, Hummy kin fi Aisha kyau”.na faɗa ina rufe baki na.
Shima dariyan ya fara yana cewa, “Hummy har Aisha’n mu baki so nace ta fiki kyau? Lallai ina da aiki a gaba na, anya zaki bar ni na kalli wasu matan kuwa? Hala daga ranan da nace kin fi kowa kyau to ƙwalele na da ganin kowacce mace ko?”.
Ina dariya na ce, “Dr’n mu na fiso kai ta ganin ni kaɗai ce mai kyau a duniya, duk ranan da kaga kyaun wata to mutuwa zanyi”.na faɗa mishi jiki na a sanyaye.
Ajiyan zuciya ya yi bayan ya daɗe dayin shiru, “Hummy na miki alƙawari duk ranan da nace kinfi sauran mata kyau to bazan sa ke ganin wata nace tana da kyau ba, bazan so ki mutu na zauna a duniya ba bu ke ba, na fi so na riga ki mutuwa, don ke nasan za ki iya riƙe mun yara na ko bayan bana duniya ko Hummy nah”.
“To ai baka kawo mun su nagan su ba”.na faɗa ina mishi shagwaɓa.
Dariya ya yi yace, “Hummy kema ai bai wuce na yi rainon ki ba, shiyasa bazan kawo miki nawa yaran yanzu ba, don zasu haukata mun ƴar Baby na da na su irin rikicin, ni kuma yanzu karatu na ke so Baby’n baby ta yi”.
“Ni dai naƙi wayon, ka kawo munsu a weekend, wallahi ina son yaran ka Dr”.
“Nasani ai Baby, duk duniya ai babu wacce zata fiki son ƴaƴana sai dai Ummi na ta biyo bayan ki, amma bana son yanzu su wahalar mun da ke ne, don nafi damuwa da kiyi karatu sama da kula mun da yaran”.
“Kana nufin ko Maman su ma na fita son su”?
“Kema ai Maman su ce, ko baki so suce miki Mama?”.
Ina dariya na ce, “kasan me nake so suce mun”?
“sai kin faɗa”.
Ina dariya nace, “Mamie, saboda idan na girma na yi aure na haihu haka na ke so yarana su ce mun Mamie”. na ci gaba da dariyan alaman naji kunya.
Shiru ya yi na wani lokaci, sannan yace, “ni kuma Abbie ko? Hummy kin taɓa son wani ne a zuciyar ki?”.
Shiru nayi, daga baya nace, “Dr ni ban san ya ya ake jin soyayyan ba, ai sai na girma tukun nasan yadda ake soyayya, kasan Daddy baya bari na naje ko ina, don baya son a cutar dani yace mun, kaga ni ko friends da maza ya hanani, ni kai kaɗai na taɓa sabawa da kai bayan Daddy na, sai na girma idan nayi saurayi zan gane, ko zaka gaya mun yadda akeyi tunda kai ka taɓa yi?”.
“Irin wanda ki ke yi yanzu”.
Dariya nayi nace, “Dr ance maka ina soyayya ne? Nifa bana kula kowa, kuma zaka na gani, Dr Abdallah ma da kace kada na kula shi, ai ɗaure fuska na na keyi kaman na zama Boss”.
Dariya ya yi tayi wanda har nima sai da na fara taya shi, a ƙarshe nace, “Dr’n mu yaushe za kaje wurin su Aisha?”
Lokaci ɗaya naji ya yi ɗiff bai ƙara cewa komai ba, magana nayi ta mishi amma bai kula ni ba, har sai da na fara mishi kuka tukun yace mun, “kada ki ƙara gaya mun haka, ke baki son na zauna da ke ne”?
Ina share hawayen ido na nace, “ina so Dr, ai na tambaye ka saboda bana son ka tafi ka bar ni ne”.
“Insha’Allahu bazan bar ki ba har iya ƙarshen rayuwa ta, sai dai ke idan kin guje ni”.
Murya ta tana rawa a hankali nace, “Dr nah! Bazan taɓa barin kaba, ko aure nayi da kai zan tafi, bazan bari mu rabuba har abada muna tare”.
“Bazan biki gidan mijin ki ba, saboda idan ya ɓata miki rai zan ƙarasa shi, kawai mu zauna tare, ko na miki tsufa?”.
“Ni bana ganin ka tsufa, ni kyau ka ke mun sosai, kuma kana burge ni, kai kaɗai na ke son na dinga gani kullum, na fasa auren ma, da kai zan zauna, amma kai ma ba zaka auri kowacce mace ba, mu kaɗai zamu zauna tare”.
Tashi Dr ya yi daga kwancen da yake ya riƙe kanshi, idon shi a lumshe yace, “me ki ke ji a kaina Hummy”?
Nima tashi nayi na zauna kaman zanyi kuka, don na rasa ni mai na keji ne yau akan shi, ina jin kaman zuciya ta zata fito, kuma na kasa gane yanayin da na ke ciki, a hankali nace,
“Dr nah! Ni kan kazo wuri na yanzu”.na faɗa kuka yana kuɓuce mun mai ƙarfin gaske.
Dafe kanshi ya cigaba da yi da ƙarfi ya furta, “ya Rabbi”. a zuciyar shi yace, “wayyo Baby nah kin yi nisa ya ya zan miki ne ni Aliyu Hussain”. Shima hawayen ya samu kanshi yana fito mishi.
“Dr kazo”.
“Baby kwanta kiyi bacci gobe akwai school, zamu ƙarasa maganan gobe”.
“ni kam naƙi Dr’n mu, to zuciya ta tana mun ciwo, zan gayawa Daddy yazo ya kaini asibiti”.na faɗa ina kuka.
“Kada ki gaya mishi, ki bari gobe zan kawo miki wani magani zaki daina ji, rufe idon ki na gaya miki wani abu”.
Da sauri na rufe, amma sai naji yana mun waƙan wani tsohun film ɗin india, wanda yawanci na kanji Daddy yana jin shi amma ni bai taɓa mun daɗi ba, amma yau sai naji daɗin shi kaman zai saka ni kuka, wani tsohun waƙa ne da Amit ya yi na film ɗin *KHABI KHABI*.
Allah sarki soyayyah, kada fah ace Dr da hummy son junan su sukeyi? Kai gaskiya haɗin baiyi ba
*TALLE! TALLE!! TALLE!!!*
*DR MOSES*
Daga marubuciyarBadariyyahƘaddara ta riga fataAna barin halal…
*AUNTY NICE*
Fatie kiyi haƙuri ki yafe mun, kije gida na sakeki saki biyu, ba wai kin mun laifin komai ba, sai dai mahaifiyata ta ce zata tsine mun idan ban rabu da ke ba, ina miki fatan Allah ya share miki hawayen ki da miji nagari wanda ya fini, hawaye ne yake zuba mun kaman an kunna ruwan pampo, ido na yana kan mijina farincikin zuciyata.
Fatie!!! Maganan auren mu dake gaskiya bazai yiwu ba, duba da yadda matata ta tayar da hankalinta dangane da maganan auren mu, ina ga idan na aureki zata barni, ni kuma ina sonta ban shiryah rabuwa da ita ba, saboda haka ke kiyi haƙuri na haƙura.
Fatie!!! maganan sadaki da aka kawo kiyi haƙuri na bar miki shi, bawai don kin mun komai ba, gaskiya auren ne nake jin bazan iya yin shi ba yanzu, idan Allah ya baki miji kiyi aurenki, idan da buƙatan wani abu ki mun magana nagode da ƙaunar ki gareni.
Fatie!!! idan kinaga akwai sarari ki sama mun wata mace mana mai kyau kamar ki, ke ina ga aure na dake bazai yiwu ba gaskiya, idan kuma zaki iya zuwa wurina Abuja sai na biya miki kuɗin jirgi babu matsala, ko hira sai ki zo muyi.
Kuka na tsuguna ina yi sosai a gaban mahaifina da mahaifiya ta da kuma yayah na, duk zagin da suka mun da nasihar da suka mun banji a zuciyata zan daina son Dr moses ba, banji kuma bazan aure shi ba, tou ina ma zan samu wanda yayi na’am da ni irin shi?
Moses baka da hankali ne? Yayah zakace zaka auri yarinyar fulani musulmah? Kana tunanin zata yadda ta aureka kana christan ne bata saka ka musulunta ba? Ko so kake ka chanja addini akan mace?
Ɗago kyawawan idon shi yayi ya zubawa ƴar shi Fatie da ta ke ɗaga mishi hannu bayan ya ajiyeta a islamiya, murmushinta da yake nuna tsantsar kamninta da mahaifiyarta kawai yake gani a fuskar ta, zuciyar shi yana mishi suya da tunanin Mummy fatie.
Juyawa maman moses tayi ta dubi ƴar da moses yake riƙe da hannunta mai tsananin kyau da dogon gashi, ko taƙi Allah lokaci ɗaya taji son yarinyar ya shiga zuciyarta a farar ɗaya, amma kada moses yayi tunanin ta karɓe shi ne shi da ƴar shi yasaka ta juyar da kanta fuskanta a ɗaure ta dubi baban moses daya ɗauko bindiga ya saita moses da ƴarshi fatie, amma kuma ya kasa aywatar da komai sai kallon yarinyar da take duban shi fuskanta ɗauke da murmushi tace, “kaka ka iya wasa da Gun ne”?
Hawaye ne ya zoba a fuskar moses, idon shi akan fatie da ita ma take ta kuka kaman ranta zai fita, bayan ta gaya mishi yadda sukayi da iyayenyta game da ƙin yadda da sukayi akan aurenta da shi. “Fatie ar ga Allah ina sonki, ina sonki da raina ne bada zuciyata ba, kuma bazan taɓa barinki ba ko da za’a tayar da garin bauchi ne da garin jos kuwa”.
Littafin Dr moses shima akwai chakwakiyar soyayyah a ciki.
*AUNTY NICE* 😘✍🏻