Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Biyar

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Biyar

10
0

©AUNTY NICE•
ƘADDARA TA RIGA FATA

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

Shafin Sadaukarwar ki ce Hauwa Alhassan Yunus.

SHAFI NA 5📑

_ Ina shiga parlon nayi tsallen murna, a fili nace, “yehhhh gobe idan Allah ya kaimu Dr’n mu zai ci girki na”.

har ɗaki na shiga baki na bai iya rufuwa ba, sai wani murmushin daɗi nake yi, a zuciya ta nace gaskiya ban taɓa jin zuciyata ta damu da wani halitta ba bayan Daddy na, sai yanzu da nake jin Dr kaman ɗan’uwa na, wanda muka daɗe muna mu’amala tare, ina shiga na wuce toilet na sake ɗauro alwalah, domin yabi jikina bana iya zama babu alwala, ina fitowa na ɗale gado na sai bacci.

Washe gari da wurin misalin 8:00 na shiga kitchen, na gyara wake na jiƙa shi, sannan na markaɗa shinkafa da gyaɗa na a tare, ina gamawa na ɗaura kunu na, 8:30 kunu na ya gamu da sauri na markaɗa wake na, ina gamawa na wuce naje nayi wanka, yau ɗaya sai naji kayan mu na hausa nake son sakawa.

Wata dogon rigan atamfa na saka wanda gaba ɗaya gaban ta stones ne a jere reras, sai wani ɗaukan ido suke yi, kitchen na koma na buga ƙullin ƙosai na, bayan ya bugu na saka mangyaɗa, yana zafi na fara zuba ƙosan, baifi kasko biyu nayi ba na sauke na juye su a cikin wani kwano mai kyau, dama ina da yaji mai daɗi wanda da zan taho wata ƙanwar Daddy ta kawo mun shi mai yawa, haka na zuba a ɗan ƙaramin rober, na ɗaura akan basket ɗin dana saka ƙosan, ɗayan hannu na kuma ina riƙe da flask ɗin kunun wanda yaji peak milk.

Ban daɗe da yin knocking ba Dr yazo ya buɗe mun, ina kallon shi nayi murmushi wanda na rasa me yasa nake jin daɗi idan na kalle shi, yana sanye da baƙin wandon jeans da red ɗin t-sheet a jikin shi, har ila yau idon shi ɗauke da farin glass ɗin da baya barin idon shi kullum.

Hannu ya saka ya karɓi flask ɗin hannu na, sannan ya ɗan matsa mun na shigo cikin parlon da yake fitar da daddaɗan ƙamshi, rufe ƙofan yayi ya shigo, kai tsaye wurin dinning ya wuce ba tare da yace mun komai ba, nima ganin inda ya nufa na bishi a baya, muna ajiyewa ya juyo ya kalle ni tun daga sama har ƙasa, amma bai furta ko kalma ɗaya ba, sai dai ƙura mun ido da yayi.

Ina ɗan murmushi mai alamar dariya nace, “Dr’mu nayi kyau ko?”.

Harara na yayi sannan ya buɗe baki yace,
“Ni banga wani kyau anan ba, tunda ke baki iya gaisuwa ba, ni kuma bazan gane kin yi kyau ba”.

ya faɗa yana jan kujeran dinning ɗin ɗaya ya zauna a kai, nima ganin ya zauna sai nayi sauri naja ɗaya na zauna, ɗago kanshi yayi yana duba na, wanda ni kuma a dole raina ya ɓaci sai na zunɓuro baki na gaba, fuska na kaman zanyi kuka a dole bai ce nayi kyau ba, bayan irin zagewan dana yi ina adon.

Taɓe bakin shi yayi bai sake bin ta kaina ba, ina gani ya ɗago cups ɗin guda biyu da nasa a basket ɗin ya zuba kunun gyaɗan da sai turiri yake fitarwa, gashi yayi fari sol sai ƙamshin gyaɗa yake fitarwa, ga wani ƙamshin flavour mai daɗin ji yana tashi, ɗaukan ɗayan cup ɗin da bai cika sosai ba yayi ya turo mun gaba na, sannan ya ɗauki ɗayan cup ɗin ya ɗan kurɓi kunun kaɗan, amma sai naga ya juyo da kanshi kaina yana bina kuma da harara, ganin abinda yayi sai gaba na ya faɗi da sauri na kalle shi da bakina kaman zan fashe da kuka nace.

“Dr’n mu kunun ma bai yi daɗi bane?”.

Ko kallo na bai yi ba ballantana nayi tunanin zai bani amsa, buɗe kwannon ƙosan yayi ya ɗauki ɗaya bayan ya buɗe rober’n yaji, ya saka a bakin shi ya tauna, ina ganin shi ya runtse idon shi, sai kuma ya buɗe da sauri ya sake harara na.

Ganin abinda yayi kawai sai na fashe da kuka ina buga ƙafa na a ƙasa ina faɗin,
“nikam wallahi nasan yayi daɗi Dr’n mu, kullum Daddy yaci abinci na sai yace duk duniya nafi kowa iya girki, kai kuma tun dana shigo baka yaba kwalliya na ba, baka kuma yaba abinci na ba, bayan Daddy yace ina da kyau kuma na iya gayu sosai, idan ya tashi aurar dani sai an yi layi ya zaɓa mun miji”.

na faɗa ina ƙara fashewa da kuka.

“To ki bari hawaye ya ƙara sa ɓata miki mummunan kwalliyan kin, dama ba kyau ki kayi ba”.
naji muryan shi yana gaya mun ba tare da ya kalli inda nake ba.

“Dr’n mu banyi kyau ba ne?”.
na tashi tsaye ina juyawa a gaban shi ina ƙara gaya mishi bai ganni bane da kyau.

Bai sake kallo na ba yace, “zauna kici abincin ki kada yayi sanyi, duk ranan da kika koyi gaisuwa zan gaya miki kinyi kyau ko ba kiyi ba”.
ya faɗa yana cigaba da cin ƙosan shi da kunu.

“Dr’n mu ina kwana”.
na faɗa ina zunɓuro baki na gaba.

Gyaɗa kanshi yayi ba tare daya amsa mun ba, amma ya mun alaman ya amsa, saboda haka jawo plet nayi na zuba ƙosan na saka yajin a gefe na fara ci nima, ya rigani gamawa, bai ce mun komai ba, ya ƙara jawo flask ɗin ya ƙara kunun kusan rabin cup ɗin sannan ya ɗauka ya miƙe tsaye ya koma cikin parlon, kunna T.V yayi sannan ya nemi wuri ya zauna yana kallon news yana kuma kurɓan kunun shi, maida hankalina nayi kan abinci na har nagama ci, ina gamawa na tashi ina maida cup da plets ɗin da muka ci ƙosan cikin basket ɗina.

“Aisha ki bar mun flask ɗin kunun”.
ya faɗa idon shi yana kan T.V ɗin, nima bance komai ba na mayar da flask ɗin na ajiye, sannan na ɗauko basket ɗin na taho inda yake, ina kallon shi nace.

“Dr zan tafi me kake so a lunch?”.

Idon shi masu tsananin kyau a cikin glass ɗin shi ya ƙura mun, ganin haka ya saka ni saurin ɗauke nawa idon ina ƙara maida fuskana alaman zanyi kuka, don ni bana so nayi abu ba’a yaba mun ba, wanda kullum hakan shi yake haɗa ni faɗa da ƴan gidan mu, amma Daddy komai nayi sai ya yaba mun, shi yasa nake jin daɗin yi mishi komai.

“Jeki ɗauko mun books ɗin ki kizo”.
ya maida idon shi kan kallon da ya keyi bayan ya gama faɗin abinda zai ce.

Buga ƙafa na nayi a ƙasa ina ƙananun gunaguni,
“nikam har yanzu baka ce mun abincin yayi daɗi ba, tunda baka ce nayi kyau ba ai ya kamata kace abincin yayi daɗi, tunda nasan dai ni ɗin mai kyau ce, tunda Daddy yace duk family’n mu babu mai kyau na”.
na faɗa ina murguɗa mishi baki na don ganin ya juyo yana gani na.

Harara na yayi sannan yace,
“zaki wuce da shirmen ki kije ki ɗauko mun books ɗin ki ko sai na kira Daddy’n shi na gaya mishi baki son karatu”?.

“Toh ai baka da number’n Daddy, ta ina zaka gaya mishi”.
Kallo na ya ke yi can sai naji ya karanto mun number Daddy.

Baki na buɗe ina kallon shi da mamaki, “dama ka san Daddy ne?”.

“Wuce ki bani wuri ko na kira shi”.

Da sauri na ɗauki cup ɗin da ya gama shan kunun nayi hanyar waje, ina fita yayi murmushin shi kaɗan yana girgiza kan shi, a hankali yace,

“Rigimammiya, komai nata irin na Aishan’n mu, nasan dai Ummi na bata sake haihuwa ba, da nace wannan ƴar Ummi ce, domin Aisha kowa yaganta sai yace babu abinda ta bari na Ummi, yadda nida Hassan babu abinda muka bari na Abban mu, sai dai banbancin hali da mukayi da Hassan”.

da sauri ya kawar da tunanin a zuciyar shi, domin baya so ya dinga tunawa da su a rayuwar shi, fatan shi yadda yabar su har abada ya zama har cikin zuciyar shi ya manta da su, wanda duk yadda yayi a wannan tsawon shekarun da yayi babu su ya kasa, sai dai idan sun faɗo mishi a rai yayi sauri ya kawar da su.

Dai-dai lokacin da yaji Abban shi ya faɗo mishi a rai na furucin da yake yawan yi kullum a kan shi, ni kuma na dawo, ina kallon yadda ya ƙurawa ƙasan parlon ido kaman yana ƙirge, nima yasa nabi wurin da kallo, banga komai ba sai zanen flower carpet ɗin shi da yake tsakiyan parlon kawai nabi da ido, da sauri na ƙaraso wurin shi dai-dai fuskan shi nace.

“Dr’n mu yanayin ka irin na mutane masu haƙuri da nutsuwa wallahi, kuma baka da hayani amma ni kuma gaskiya ina da surutu kaman wanda naci…..”.
Sai kuma na rufe baki na ina dariya.

Da sauri ya ɗago idon shi da suka yi ja ya ƙura mun ido, ina dariya na sake cewa,
“Dr’n mu idon ka kaman na zaki, dama ALIYU aka saka maka”.
na faɗa ina binshi da murmushi.

Da ƙarfi ya runtse idon shi, kuma da ƙarfi ya furta, “Ya Allah”.

sannan ya buɗe idon shi ya ɗora a kaina yana mai da numfashi kaman wanda yayi tsere, a zuciyar shi kuma yana maimaita,
innalillahi wa’inna ilahir raji’un, ya fara tuna wata rana haka Aisha ta taɓa gaya mishi lokacin suna zaune a parlon Abba ana karya wa sai ga Hassan ya shigo da fuska a ɗaure yana duban Hussain yace,

“Bros wani irin wulaƙanci ne an kirani a waya ba zaka ɗauka kace ina wanka ba, irin haka sai mai kiran yace ina wulaƙanci ne”.

ya faɗa ya na ture mun ƙafa na da nashi ƙafan don neman ayi faɗa, ni kuma a rayuwa na tsani ka hau kaina da masifa kaman kai ka haife ni, don duk shiru na da haƙuri na bana iya ɗaukan raini da wulaƙanci, shi yasa kafin kaji baki na a abu sai komai ya ɓaci, cikin ɗaure fuska da nuna bana son raini na ɗago zan mishi masifa, kawai sai naji Abba ya dafa kafaɗa na yana ɗan bubbugawa yana cewa.

“Ubana Aliyu tabbas kai mai haƙuri ne da nutsuwa kaman mai sunan ka, kada ka yadda ka dinga biyewa ɗan’uwan ka ana jin kan ku, domin shi haƙuri baiwa ne wanda ba kowa yake da shi ba, tabbasa ALIYU da mai suna ALIYU basu son raini, amma sun kasa masu haƙuri da kuma nuna soyayya wa ɗan’uwan su mai tsafta, shi baka ga sayyadina Aliyu yadda yake son ɗan’uwan shi (Annabin rahma S.A.W ba?) to kayi koyi da shi kaji ZAKI NA“.

Babu ɓata lokaci Ummi ta amsa da cewa,
“gaskiya Abban su baka yi mun kara yadda nake maka, nima fa Hassan yaci sunan nawa mahaifin ABUBAKAR Kuma kasan yadda shima Sayyadina ABUBAKAR ya kasance babban amini kuma masoyin manzon Allah (S.A.W), kuma koda ya kasance shi Hassan mai neman faɗa ne da ɗan’uwan sa ai zaka na min kara saboda dai Baba na mai haƙuri ne da kuma kawar da kai, don dai shi Hassan ya ɗauko halin ƙanwa tace HAUWA domin ita ce mai yawan neman tsokana da son ayi rikici”.

ta faɗa wanda gaba ɗaya parlon muka kwashe da dariya saboda tunawa da halin Aunty Hauwa, wanda babu inda Hassan ya bar halinta kaman ita ta haife shi wurin neman tsokana da kuma masifa, don kullum ta zo gidan mu sai sun kancale da Ummi duk kuwa da haƙurin Ummi, sai dai duk gidan su Ummi babu mai son ƴan’uwa da zumunci irin nata, ga kuma faɗan gaskiya, wanda idan ka ganta sai ka rantse mutum ɗaya ne ita da Ummi tsabar kaman nin su, sai dai banbancin shekaru, tunda mutane biyu ne a tsakanin su.

Ina dariya na kalli Ummi nace, “hmmm Ummi wallahi neman faɗan sune da yawan surutun su kaɗai iri ɗaya da Hassan, amma ita Aunty Hauwa ai nine na ɗauko son faɗin gaskiyar ta da halinta na son zumunci, amma shi wannan ai idan na gaya miki halin shi sai kin wuntsila shi ƙauyen ningi, kince sam wannan ba halinki na dattaku irin na mutanen garin MISAU yake da shi ba”.

na faɗa ina kallon Hassan da yake harara na, dariya na fara mishi ina cewa, “ko na faɗa ne my heart?”.

“Munafur ci kenan zaka koma, don nasan duk inda mai shiru yake, randa ya falle to munafurci zai haɗa, kuma ni nasan Ummi na da Abba na sun yadda da ni kawai nema kake su fi sonka a kaina shiya sa zaka mun sharri”.
ya faɗa yana jinginuwa da jikin Ummin mu.

Abba dariya yayi yace, “kaga shalelen Ummi’n shi, daɗinta ma ga Aisha nan, dole kayi haƙuri da cinyar Ummi”.

A lokacin Hassan hararan Aisha yayi, ita kuma ta murguɗa mishi baki, wanda kullum na rasa mai yasa basu zama inuwa ɗaya, amma ni bana da lokacin tanka musu.

“Dr’mu ka kula ni mana”.
na mishi magana cikin shagwaɓa, don tunda yayi mun tsawa ya razanani sai kuma ya koma yayi shiru idon shi a runtse, wanda daga dukkan alamu tunani ya tafi.

Ƙura mun ido yayi duk alaman hawaye ya cika idon shi, a hankali ya miƙo mun hannu muryan shi can ƙasa yace,

“Aishan mu taho wurina ki bani labarin Hassan da Ummi na da Abba na, yanzu ciwon Ummi na yana tashi? Ko kuma tunda komai ya riga ya faru zuciyar ta bazata sake barinta ta samu lafiya ba, zo kusa da ni Aisha na, ni kaɗai nake son ki sama da irin wanda Ummi ta ke miki”.

Tsoro naji ya lulluɓe ni domin hawaye ne masu gudun gaske suke biyo fuskan Dr mu, wanda duk sai naji na rasa abinda yake mun daɗi, da sauri ina jijjiga kaina alaman ba haka bane, nima hawaye yana zuba mun amma nawa na ganin abinda nake girmamawa yana hawaye shi ya dame ni nace.

“Dr’n mu bani bace fa Aisha’n, ni fa Hummaira ake gaya mun, Dr’n mu wacece Aishan? Matar ka ce? Ƴar’uwar kace? Wacece ita ne Dr na?”.
na faɗa lokacin da sautin kuka na ya ƙaru.

“Aisha ce kaɗai take ce mun Yaya Hussain ɗina, ke kuma kina cemun Dr’n mu keda sauran students ɗina, yanzu kuma kince mun Dr’n ki? To wallahi kece Aisha ta, kina neman yi min wasa da hankali nane, Ki taho wuri na Aisha na!!”.

Ya faɗa da iya ƙarfin shi wanda sai da na zubar da books ɗin hannu na, na fita da gudu a parlon nayi nawa gidan ina kuka, da ƙarfi na shiga na mayar da ƙofar na rufe ina kuka, ina jingine da ƙofan naji muryan Dr’n mu yana cewa.

“ki buɗe ƙofan Aisha ki gaya mun wacece ke? Tabbas kece Aisha na, kuma yau zan tabbatar miki da cewa ke ɗin Aisha tace”.

Da ƙarfi yake maganan wanda lokaci ɗaya naji tsoro ya rufe ni, a zuciya ta nace,

“ko dai Aisha’n ba mutum bace? Ko shima Dr aljani ne?”.
Can kuma nayi sauri na girgiza kaina nace, “Dr na mutum ne, amma Aisha’n ba mutum ba ce”.

Buga ƙofan yayi da ƙarfi yana cewa, “ki buɗe Aisha ko na ɓalle ƙofan na shigo”.

Jin furucin shi ya saka na ruga da gudu na shige ɗakina na sake rufu ƙofan ɗakin, duk jikina rawa yake yi, tsabar tsoron da ya shige mun zuciya ta.

“Aunty Nice ko ta kitchen zamu koma mu samu hanyar guduwa ne?, don idan wannan aljanin mutumin ya shigo ina ga har da mu zai haɗa”.

cewar Miss Xerks da tayi zuru-zuru da idon ta tana kallo na a tsorace, nima haɗiyan yawun tsoro nayi ina maida numfashi da sauri-sauri nace,

“Miss Xerks ina cikin zama na kika ce anyi sallah lafiya mu fito ɗaukan rahotanni domin masoyan Gaskiya writers su samu goron sallan da bamu basu ba, haka kika izo ƙeyata muka taho har nan spain, tsabar mita bamu tsaya a ƙasar mu ba, da yanzu a nigeria ne kiran Ummu Nabeel zamuyi su taho da rundunan ƴan Gaskiya writers su fitar da mu ko ta saman kwanon gidan nan ne”.

na faɗa ina fashewa da kuka don wallahi yanayin Dr Hussain ya bani tsoro.

Ƙaran buga ƙofan ya saka naga Miss Xerks ta sandare a wurin, nima daga ganin haka naji komai na hannu na sun zube, babu sauran ɗaukan rahoto sai mun farfaɗo, saboda haka a jiraye mu tukun mu dawo hayyacin mu.

Masoya na masu bibiya ta godiya nake a gare ku, Kar dai ku manta da danna min vote da kuma yin comment domin jin ra’ayoyin ku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here