Home Siyasa Ɗan Takarar Gwamna A Zamfara Yayi Iƙirarin Kai ƙarshen Matsalar Tsaro Cikin...

Ɗan Takarar Gwamna A Zamfara Yayi Iƙirarin Kai ƙarshen Matsalar Tsaro Cikin Shekara Biyu, Ko yayi Murabus

17
0

Ɗan Takarar Gwamna A Zamfara Yayi Iƙirarin Kai ƙarshen Matsalar Tsaro Cikin Shekara Biyu, Ko yayi Murabus

Daga Aminu Abdullahi Gusau

Dan takarar gwamna na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Sanata Kabir Garba Marafa, ya yi alkawarin kawo karshen matsalar rashin tsaron da ke addabar jihar Zamfara tare da dawo da zaman lafiya mai dorewa cikin shekaru biyu idan aka zabe shi a matsayin gwamna, ko kuma ya yi murabus daga mukaminsa.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a gidansa da ke Gusau yayin tattaunawa da ‘yan jarida (musamman wakilan kungiyar ‘yan jarida ta kasa, NUJ) game da fitowarsa a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a jihar da kuma kudirinsa na kawo sauyi mai kyau idan aka zabe shi a zaben gama-gari na shekarar 2027.

Da yake jawabi, dan takarar gwamna na NDC a jihar Zamfara ya ce, “Na yi aiki a matsayin kwamishina na tsawon shekaru da dama a wannan jiha, haka kuma na yi aiki a matsayin Sanata na tsawon shekaru, na san matsalolin wannan jiha da kuma yadda za a magance su.”

“Idan aka zabe ni a matsayin gwamna a zaben gama-gari mai zuwa, ku ba ni wa’adin shekaru biyu, zan kawo karshen rashin tsaro a wannan jiha.”

“Idan na kasa kawo karshen rashin tsaro, ayyukan ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, da sauran laifuka a jihar Zamfara cikin wa’adin shekaru biyu, zan yi murabus da kaina,” in ji shi.

Marafa ya yi kira ga al’ummar jihar Zamfara da su goyi bayan jam’iyyar NDC tare da bayar da dukkan kokarinsu wajen tabbatar da nasarar dukkan ‘yan takarar jam’iyyar a zaben 2027, inda ya yi alkawarin samar da jiha mai zaman lafiya, ci gaba, da kwanciyar hankali idan aka zabe shi a matsayin gwamna.

Idan baku mantaba, Sanata Marafa a ranar Talata, ya bayar da motocin yakin neman zabe ga shugaban jam’iyyar NDC na jihar, da daraktan yakin neman zabe (DG), da sauran shugabannin yakin neman zabe na yankuna a jihar, bayan an kaddamar da yakin neman zaben cikin nasara a ranar Litinin.

Bayar da motocin ga shugabannin jam’iyya da na yakin neman zaben wani bangare ne na dabarunsa na karfafa gwiwar tawagar shugabannin domin su tashi tsaye wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar NDC baki daya a zaben gama-gari na 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here