Sai jajirtattun ‘yan siyasa ne kaɗai za su iya shiga ADC – Tambuwal
Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa jajirtattun ƴan siyasa ne kaɗai, da suka maida hankali wajen yi wa al’umma hidima maimakon neman biyan buƙatun kansu, za su iya shiga jam’iyyar ADC.






