Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta Uku

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta Uku

12
0

©AUNTY NICE
°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE✍🏼

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

SHAFI NA 3📑

__📖 Girgizamata kai kawai nayi alamun babu wani dangantaka a tsakanin mu, wuri ta nema kusa dani ta zauna ƙasa-ƙasa tana gaya mun wai yanzu taji wani ɗan class ɗin mu yana cewa a tarihin Dr Hussain bai taɓa fita a class ya dawo ba, sunyi mamaki da sukaga ya dawo, shiyasa suke tunanin ko yasan ni ne.

A hankali na dubeta sannan nace, “Vicky ban san shi ba, a school ɗin nan na fara ganin shi, kuma shima ina tunanin bai sanni ba, don na lura ko kallon fuskana bai yi ba, kawai may be yaga laifina na farko ne, shiyasa yamun uzuri”.

na faɗa ina kallon ta, ita ma girgiza kai tayi alamun magana na haka yake.

Bayan mun dawo break ne muka yi lecture ɗaya sannan muka ta shi, Amal ta dube ni lokacin muna fita a school ɗin tace,

“Hummy yaushe zamuje muyi shooping ne? Don gaskiya akwai abubuwan da nake son na ƙara”……kaman bazan yi magana ba saboda tunanin daya cika zuciya ta, har ta manta dani sai kuma na samu bakina da furta,

“Mu bari ranan saturday sai muje wani mall dana gani kusa da inda nake, naga wurin yana da kyau da girma, ina ga zamu samu duk abinda muke buƙata a wurin”.

dafa kafaɗa na tayi muka tsaya dai-dai lokacin da ta tsayar mana da taxi, BAILEN, CARRER DE ta faɗawa mai taxi ɗin sunan unguwan da take, nima na gaya mishi inda nake, saboda ni nafita kusa da school ɗin, haka muka shiga har inda nake na sauƙa ita kuma ta wuce.

Ina ƙarasowa gidan da nake wanda gida huɗu ne a compound ɗin gidan, wanda yake kusa danawa ban taɓa ganin an buɗe gidan ba, sai biyun da suke gaban namu suma wasu students ne a ciki amma dukan su maza ne, ina ƙarasowa wanda muke haɗe da shi naga yau alaman akwai mutane a gidan don ina zuwa kusa da wurin naji ƙamshin kaman ana soya ƙwai, har cikin zuciyata naji daɗi domin ina tunanin ko macece a gidan nima na samu wacce zatana tayani hira wani lokacin.

Naso ace naga wanda take gidan amma har na shiga gida na ban ga kowa ba, ina shiga direct toilet na shige na ɗan watsa ruwa, riga dai-dai gwiwa na nasaka domin na samu sakewa na ɗan taɓa karatu, ina shiga kitchen naji nayi missing Daddy da yanzu har ya dafa mana abinci, amma yanzu gashi yunwa na keji kuma ina jin lalacin dafa komai, kunkumina na riƙe ina hararan kitchen ɗin kaman shi ya haɗa ni da yunwan, zuwa can na juya na koma parlon na zauna akan dinning ina ta tunani.

Kaman an zabure ni na miƙe na shige kitchen ɗin da sauri, egg guda uku na ɗauko na fasa na fara soyawa saboda na tuna ita ma neighbor nah ma shi naji tana soyawa, ni kaɗai na fara murmushi a zuciyata ina cewa Allah kasa macece a gidan.

Bayan na gama na dawo parlor na sauƙa akan ƙwaina gefe ɗaya kuma na haɗa cornflakes ina sha, ko cin rabi banyi ba naji ana nocking ƙofa na, dariya naji ya ɗan suɓuce mun a fuskana, a zuciyata nace hala neighbor na taji na dawo shine ta zo duba ni, sai kawai nayi tsalle na miƙe, ko duba kayan jikina banyi ba saboda murna da ɗaukin zuwa ganin neighbor.

Ina buɗe ƙofan sai naji da ƙaran buɗe ƙofan da bugawan zuciyata sunyi a lokaci ɗaya, da ƙarfi na rike ƙofan don kada na faɗi, idona kuma a zare kaman zasu zazzago ƙasa, kuma alokaci ɗaya naji na kasa rufe bakina dana buɗe zanyi magana.

Haka zalika shima a gefen shi ba ƙaramin faɗuwar gaba da gigita yayi ba, domin bai taɓa tsammanin ganina ba, domin yayi tunanin namiji ne a gidan don last week kaman namiji yagani ya fito ya daɗe tsaye a ƙofan gidan, shi kuma tun ranan Allah bai nufa ya dawo gidan ba sai yau.

Sake juya idon shi yayi yana Ƙara zuba min ido, daga gani kuma zuciyar shi tana harbawa kaman zata faɗo ƙasa, a zuciyar shi yace, “kaddai wannan yarinyar da yaji muryanta sak irin na AISHA ce a gaban shi, yarinyar da tunda yaji muryanta ɗaxu faɗuwar gaba yaƙi barin shi da wani irin mummunan tsoro a zuciyar shi, duk da ɗazu bai kalli fuskarta sosai ba, kawai muryanta da tsarin maganan ta babu maraba dana Aishan.”

saidai zuwa yanzu duk ta kunce mishi notinan kanshi daya ga hattah zaro idonta da ɗan bakinta data buɗe kaman na Aisha, kai shi idan ba karya yake so yayi wa zuciyar shi ba sai yaga hatta fuskan kaman na Aisha aka maka mata, sannnan kuma tsayin ta ma kaman na Aishan ne, ba zuciyar shi ba yau yana ji hatta huhunshi ma kaɗawa suke yi, yau wani irin gamo yayi? Shiyasa tunda tayi mishi magana yaƙi yabar kanshi ya dubi fuskanta ɗazu.

“Dr mu kai…ne…a..nan…wurin?” Lokaci ɗaya ta samu kanta dayin in’inan da bata san ko tana yi ba ko yanzu ne ya zo mata.

Shi dai bai ce mata komai ba sai kaɗuwan da zuciyar shi ta sake yi don jin yadda tace mi shi wai, “Dr mu”.

innalillahi ya furta a zuciyar shi, kaddai Aisha ce tazo har inda yake? Wato duniyan nan ƙaramar wuri ne ko? Duk inda kaje sai an tarar da kai? A hankali ya buɗe baki yana kallonta yace,” AISHA

Zaro ido Humairah tayi da sauri tana duban shi cikin mamaki, sannan tace, “lahhh kaima Aisha kake son ƙirana da shi? Kasan kakana ne kawai suke ce mun Aisha, Daddy yace mun duk ranan da yace mun Aisha sai ya wuni bashi da lafiya, dama kasanni ne? Shiyasa ɗazu dana baka haƙuri sai kaima kamun uzuri a rayuwa ko? Don kasan laifin da mutum zai yi a farko yaka mata ana mishi uzuri, idan ya sake kuma sai ace gangancine ko kuma da son ran shi yayi, ta ƙarisa maganan tana mishi murmushi, wanda lokaci ɗaya yaji faɗuwar gaban shi ya ƙaru, wanda baisan ya dafa jikin bangon gidan da ƙarfi ya furta.

“Aisha ya ya kike bina kuma a rayuwa ta, meye ya saura kuma? Bana ce……”.

sai kuma ya rufe bakin shi da hannun shi da ƙarfi, ya kifa kan shi a kan hannun shi ɗayan daya dafa bangon yana mai runtse idon shi, a hankali yana bawa kanshi haƙuri yana gayawa kan shi ba zai taɓa yiwuwa Aisha ta zauna yadda take kaman daba, bayan yanzu rabon shi da ita ya kai 18yrs, wannan da take gaban shi kuma bazata wuce 16yrs zuwa 17yrs ba. Ya kamata zuwa yanzu ace Aisha ta kai 35yrs, tunda shi dai yanzu yana 39 zuwa 40yrs.

Sake ɗago idon shi yayi ya ƙura mun idon shi, wanda ni ma zuwa lokacin na fara tsorata da yanayin da na ga ya shiga, ina bin shi da kallo cikin damuwa nace, “Dr mu baka da lafiya ne? Na baka paracetamol?”.

Juyawa yayi da sauri yayi hanyan gidan shi, duk illahirin jikin shi kuma yana rawa, wannan wani irin kamane tayi da Aisha hatta yanayin yarintar su da shagwaɓar su iri ɗaya ne, cikin maganar zuci da yakeyi, idan bai manta ba babu hali da ya zauna yayi shiru za kaji Aisha tana cewa,

“na kawo maka paracetamol?” Wato ɗabi’un suma ɗaya ne, to ko dai ita ce? A haka har ya wuce gidan shi ya rufe kanshi, sannan ya runtse idon shi bayan ya faɗa kan gadon shi.

Humairah tana tsaye har saida ta daina ganin shi tukun ta koma nata parlon ta zauna, sai da ta daɗe idonta yana kallon abincin tana tunanin meye ya samu mutumin nan? Can taji kan ta ba zai ɗauki tunanin ba kawai sai ta share ta cigaba da cin abincinta.

Har ranan friday ban sake ganin Dr ba a cikin compound ɗin mu, ko alaman ana zama a gidan ban ga anayi ba, kawai sai tayi tunanin ko yana tafiya wurin familyn shine, don bana jin motsin mata ko yara a gidan, can kuma na saka hannuna na riƙe haɓanna kaman mai tunani zuwa can sai nayi dariya nace “yes hakane ma tunanina dai-dai ne, wato matar shi da yaran shi suna wani gida, may be matar shi tana aiki a wani wurin ne shiya sa ya barta da yaran shi, shi kuma nan yafi kusa mishi da school ɗin da yake aiki, wataran ya zauna anan wataran ya koma wurinta, sai nayi tsalle na jinjinawa kaina ina dariya irin tunaninna dai-dai yake.

Ranan friday muna da Dr Hussain a 8:00 to 9:30, tun 7:30 muka shiga class, don duk ƴan class ɗin suna tsoron Dr Hussain, muna zama class reps ya tashi yace,

“duk ku kashe wayoyin ku gudun abinda ya faru ran monday”.

kaman ance na bar wayana a kashe sai duk aka juya ana kallona, murguɗa musu baki nayi na juyar da kaina gefe, dai-dai lokacin da ya shigo class ɗin, sai kaji kaman babu sauran wasu halittu masu numfashi a class ɗin duk an ɗauke wuta.

Yafi minti uku a tsaye yana duban books ɗin da suke hannun shi, ba tare da ya dubi kowa ba, can ya rufe ya fara mana lectures yana yi yana ɗan zaga class ɗin, wanda bai taɓa musu haka ba sai ranan, yana zuwa dai-dai inda nake zaune ya tsaya ya cigaba da bayanin shi yana tsaye a wurin, can ya miƙa mun hannu alaman na bashi abu.

Duk sai naji na ruɗe na waiwaya na dubi class ɗin naga kowa ni yake kallo, haka shima Dr idon shi yana kaina ya ƙura mun idon shi, batare daya daina bayanin da yake yi ba, a hankali na nuna mishi ban fahimci mai yake nufi ba, abinda bai taɓa yiba yayi shine ya saka hannu ya buɗe handbag ɗinna ya ɗauko wayana ya duba yaga a kashe yake, amma duk da haka bai maida mun ba, sai kawai ya jefa a aljihun shi, ya wuce gaban class ɗin inda yake tsayuwa da.

A haka yayi muna lecture har ya gama ya fita, kuma ko tunanin ya miƙa mun wayan bai yi ba kawai fitan shi yayi, ni ma ban yi wani yunƙurin tashi ba ballantana na nemi ya bani.

yana fita Amal ta dube ni tace, “Hummy yaya baki karɓi phone ɗinki ba”?

Juya ido nayi cikin yanga da yabi jikinna nace, “idan yana so zai bani ai, ba lallai sai na bishi ba”.

Amal ta sake cewa, “yaufa friday ne Hummy, kinga sai monday ne fa ya dawo class ɗinnan, zaki iya zama babu wayan?”.

“idan bai bani ba yaya zanyi Amal?”.

Kowa class ɗin da abinda yake faɗi, can uwar rawan kai ta taso jiki na rawa ta zo wurin mu ta zauna tana cewa,

“Humairah yaya me yake faruwa ne?”.

Juya idon na nayi kaman mai jin bacci nace,

“me yasa kuke damun kan ku ne?”.

Sai na juya na buɗe book ɗin da yake gabana ba tare dana ce komai ba, ganin ba zan ce komai ba sai kowa ya ƙunshe guntun gulman shi yayi shiru, har wanda yake ɗaukan mu Eng ltr ya shigo.

Har na kai yamma banga alaman Dr a compound ɗin gidan mu ba, duk damuwata yau friday kada Daddy ya ƙirani yaji wayan a kashe ko kuma a hannun wani, nasan Daddy ba zai ji daɗi ba.

Can nayi tunanin bari na leƙa ɗayan neighbor na da yake yawan gaishe ni idan zan fita na tambaye shi ya bani aron wayan shi, idan na ƙira phone ɗina naji a kashe, sai na kira Daddy nace mishi na manta wayan a school ne, ina fitowa na kusan cin karo da mutum a ƙofan shigowa gida na, sai dana razana ban san lokacin dana saka ihu ba na juya da gudu kaman wanda naga ƙadangare.

Ido ya sake runtsewa yana tunawa wani yanayi kaman irin haka daya taɓa faruwa tsakanin shi da Aisha, ta fito daga kitchen shi kuma zai shiga kitchen suka haɗu, a take ta zunduma ihu ta juya da gudu har saida ƴan gidan suka fito ana tambayan lafiya? Shi dai kallon su ya keyi yana nuna ta da hannu akan su tambayeta shima bai san me ya saka ta ihun ba, duk kan su dariyan Aisha su keyi suna maganan tsoron ta, sai yaji hawaye ya cika mishi ido a ran shi yana cewa,

“to ita wannan yarinyar wacece ita ne?

Duk kamanin su da yanayin su iri ɗaya ne da Aisha, shi yau ina zaiga Aishan shi ya nuna mata mai irinta, amma ya saka wa ranshi yadda ya bar nonon uwar shi to ya bar Aisha har abada, sai yana jin wani hawaye mai zafin gaske wanda duk ranan da yayi wannan tunanin sai yayi hawayen da bai shirya ba, haka ya shige ya rufe kan shi.

Ina komawa cikin parlon sai kuma abinda nayi ya fara bani dariya, a raina nace kullum fa Daddy sai ya mun faɗan yawan tsorona, faɗawa kan kujera nayi ina ta dariya, can na tuna ko wayana fa ban karɓa ba, sai nayi saurin tashi don nabi bayan shi na karɓi wayan.

MAI DAMBUN AUNTY NICE, WANNAN SHAFI NAKI NE KE KAƊANKI, KIYI YADDA KIKE SO DASHI, AUNTY NICE TANA MAI KARA JINJINA MIKI, KUMA AMIƘA MUN GAISUWA GUN MAI SUNAN ƳAN GAYU, (JAN PARIH)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here