Home Uncategorized ZAMFARA: Mutane 38 sun kamu da wata cuta da ba a gano...

ZAMFARA: Mutane 38 sun kamu da wata cuta da ba a gano ba a kananan hukumomi biyu

13
0

Gwamnatin Jihar Zamfara ta tabbatar da samun mutane 38 da suka kamu da wata cuta da ba a gano musabbabinta ba a kananan hukumomin Shinkafi da Zurmi.

Gwamnatin ta ce an samu rahoton bullar cutar ne a ranar 29 ga Oktoba, lamarin da ya sa ta tura tawagar jami’an lafiya ta musamman domin gudanar da bincike da dakile yaduwarta.

Rahoton Ma’aikatar Lafiya ta jihar ya nuna cewa mafi yawan wadanda suka kamu da cutar manya ne a Shinkafi, yayin da aka samu wasu a garin Moriki da ke karamar hukumar Zurmi.

Alamomin cutar sun hada da zazzabi, ciwon kai, rashin sha’awar abinci, amai, ciwon jiki da kuma kasala.

Binciken farko da likitoci suka gudanar ya nuna cewa cutar zazzabin cizon sauro, ciwon ciki da amai (Gastroenteritis) ko kuma sankarau na iya zama sanadin matsalar. Sai dai ma’aikatar ta ce ana bukatar gwajin dakin bincike domin gano ainihin musabbabin cutar.

Daraktan kula da harkokin lafiyar jama’a na jihar, Yusuf Abubakar, ne ke jagorantar tawagar kwararrun da aka tura domin gudanar da bincike, karfafa sa ido kan cututtuka da kuma hana ci gaba da yaduwarta.

Tawagar na duba marasa lafiyar a cibiyoyin kiwon lafiya da ke Shinkafi da Moriki, tare da raba magunguna da kayan aikin jinya, da kuma tattara samfurin jinin da sauran bayanan marasa lafiya domin gwaji a Sokoto.

A nata bangaren, kwamishiniyar lafiya ta jihar, Nafisa Maradun, ta bukaci al’ummar yankunan da abin ya shafa da su gaggauta zuwa asibiti idan sun fara fuskantar daya daga cikin alamomin cutar.

Ta kuma gargadi jama’a da su guji shan magunguna da kansu ba tare da shawarar likita ba, tare da kira gare su da su ba jami’an lafiya hadin kai yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here