Home Uncategorized RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 23

RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 23

17
0

Na

Ruƙayya Ibrahim Lawal (Ummu Inteesar)

PP 23

ƁANGAREN FATIMA

Kyakkyawan murmushi ta haske shi da shi wanda ita kaɗai ta san dalilin yin kayanta da ma’anarsa, dabara ce ta faɗo mata tamkar wahayi ta muskuta da nufin gyara zamanta ta dunƙule hannu mai maganin ta ƙara matsawa gefen gado da dabara ta saki ƙwayar a cikin lokon gefen gado ta komar da cinyarta a kai ta danne sa’annan ta karɓi ruwan ba tare da ta buɗe hannunta ba ta miƙo ɗayan hannun ta karɓi kofin ruwan ta watsa ƙwayoyin pracitamol a bakinta ta kora da ruwa.

Ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani daɗi yana ratsa zuciyarsa na ganin haƙarsa ta cimma ruwa ya miƙe fuska washar yana kallon ta. “Masha Allah! Yanzu ki kwanta ki ƙara hutawa kin ji sweetheart, zan je na haɗa miki breakfast me za ki iya ci?”

Ita ma da fara’a ta amsa masa “Kwaɗayin Irish na tashi da shi yau, idan zan samu zan so amma kada a saka ƙwai pls.”

“An gama ranki ya daɗe.” Ya faɗa yana yi mata salute alamun girmamawa ya juya ya fita.

Hararar ƙeyarsa ta yi a ranta tana masa dariya da faɗar ‘Ka ji da munafuncinka, in sha Allahu Fati ta wuce matakin wannan yaudarar taka.’

Yana ficewa ta miƙe ta ƙwaƙwulo ƙwayar a inda ta ɓoye ta ta je ta jefa a shadda ta yi flushing sannan ta koma kan gado ta kishingiɗa ta yi lamo tana faman saƙe-saƙe, haƙiƙa abubuwan da yake yi mata na cin zarafi sannu a hankali sun fara tasiri a zuciyarta wurin rage mata kaifin soyayyar shi da jin daɗin zama gidan auren.

Yana barin ɗakinta kitchen ya je ya shirya musu breakfast ya soya mata abin da take sha’awar ci wai duk don ya kawar da hankalinta a kan makircin da yake kitsawa kar ta fahimta.

Kusan awa ɗaya ya ɗauke shi kafin ya kammala komai ya fito ya bar madafar a wargatse, ya shigo falon da kayan ya ajiye sannan ya shiga ya yi wanka ya fito ya leƙa ɗakinta don kiranta.

A yadda ya bar ta a haka ya same ta ‘Ai kin banza duk ta ƙazance. Ciki hauka ne?’ Ya faɗa a ransa a zahiri kuwa faɗaɗa murmushinsa ya yi yana faɗar.

“Ranki ya daɗe sarauniya girkinki ya kammala, fito ki yi rating ɗina.” Ya juya ya koma inda ya fito.

Da murmushi ta raka shi sa’annan ta miƙe zuwa lokacin zafin zazzaɓin ya ragu a jikinta ta sauko daga gadon jiki ba ƙwari ta same shi a falo.

A ƙasan ta zauna inda suka saba zaman cin abinci ya zuba mata Irish ɗin a plate ya miƙa mata. Dafa hannunsa ta yi ta tura baya tana murmushi “Mayar ka haɗe mu ci tare.”

Maganar ta jijjiga shi ya ƙure ta da kallo kamar mai son tantance gaskiyar abin da kunnensa suka jiye masa. A ransa yake faɗar ‘Sabon salo kiran sallah da usur.’ A zahiri kuwa da yanayin maɗaukakin mamaki ya ci gaba da kallonta yana faɗar “Yau kuma ke ce za ki ci abinci kwano ɗaya da ni.”

Ta gyaɗa kai alamar eh tana masa ‘yar dariya.

Ga dai shi abin ne da yake fatan samu tsawon shekaru huɗu amma yau ya zo masa a lokacin da baya maraba da shi don shi dai ba zai iya haɗa kwano da mai ciki ba, salon suna tsaka da ci ta kwaro musu amai a ciki?

Ganin ta tsare shi da ido kuma yana so ya yaudare ta har sai ya tabbatar da zubar cikin, sai kawai ya nuna mata kwanon yana faɗin bismillah.

Hannu ta saka ta fara ci shi kuma ya haɗa tea ya fara sha da biredi. Jira take ta ga ya saka hannunsa a farantin Irish ɗin amma ta ji shiru. Ta ɗago ta kalle shi. “Ya yi daɗi sosai yaya, kai ba za ka ci ba ne?”

Busasshen murmushi ya yi mata yana jin kamar ya ɗauke ta da mari ya dai ƙume haushin a cikinsa ya ce “Ki ci ki ƙoshi sweetheart, idan na gama da tea ɗin nan na ga akwai gurbinsa a cikina zan ci.”

Wayonsa na yin hakan shi ne sai ta ƙoshi ta cire hannunta a kwanon idan ma zai ci kenan, sai ya ci ɓangaren da ba ta taɓa ba.

Ita ma da ta lura kamar akwai abin da yake saƙawa a ransa ta ɗauke idonta a kansa ita ma tana zancen zuci ‘Ka gama munafuncin naka dai, kai ne sarkin mita ba a cin abinci tare da kai, ba a nuna maka soyayya to yanzu kuma na zo gyarawa amma ba ka maraba da hakan.’

Kallon kallo suka ci gaba da yi kowa yana yin nasa ƙarin ba wanda ya ƙara cewa uffan, kowa da bikin zuciyarsa.

Ita ta riga shi kammalawa ta miƙe tsaye Allah ya taimake ta abincin ya zauna a cikinta. Waje ta fita ta wanko hannu, sai a lokacin ta ga yadda ganyen bishiyar da ke gidan makwaftansu duk ya kakkaɓo ya ɓata mata tsakar gidan.

Ba ta koma ciki ba ta je ta ɗauko tsintsiya ta fara tattare ganyayen ta kwashe kana ta koma cikin baranda ta fara sharowa.

Tana tsaka da wannan aikin ya fito kammale cikin shigar farin yadi mai laushi ya sha hula a kansa ga takalminsa kalar waɗanda ya fi yin ado dasu wato sawu-ciki hannunsa na dama riƙe da jakar aiki da makullan mota.

Ya zo ya tsaya kusa da ita yana fesa mata munafikin murmushi, “Madam ni zan tafi wurin aiki yau na kusa makara.”

Ɗagowa ta yi ta kafe shi da ido ya yi matuƙar kyau kamar ka sace shi, nan da nan ta ji kibiyar kishi ta caki ƙawon zuciyarta “Gaskiya yaya kyaun nan ya yi yawa da ka je ka canza tufafi, jami’ar nan fa wuri ne na mata barkatai.”

Yar dariya ya yi ko ba komai yana so ya ga ta nuna kishinta a kansa hakan na ba shi tabbacin har yanzu ruwa yana maganin datti, zai iya yin nasara a kanta idan ya dage. Wani ɓangare na zuciyarsa na azalzala masa ya yi sauri ya tafi inda ‘yanmata da yawa suke muradin ganinsa, suke jiransa domin buga wasan kyautata masa a tsakaninsu da suke yi kusan kullum.

“Ba zan iya da rigimarki ba Fatina, kin san dai aikin nan dole ne, shi ne rufin asirinmu. Ni zan tafi ki kula da kanki, don Allah ki nemo ko ‘ya’yan makwafta ne su taya ki zama, idan kin ji sauyi ko kaɗan ne a jikinki ki yi amfani da wayarsu a kira ni kin ji? Allah ya ƙara miki lafiya.”

Da amin kawai ta amsa yana fita ta bi bayansa da katuwar harara domin a yanzu ta tabbatar da zarginta a kan wancan maganin da ta yasar a ranta ta ce ‘Ai haƙar taka ba ta cimma ruwa ba, kuma ba za ta cimma ba. In Sha Allahu garas za ka dawo ka same ni.’

Ci gaba da ayyukanta ta yi hankali a kwance, ta kammala gyara gidan, ta je ta tarkato kwanukan da suke falo ta kai kitchen a can ta tarar da aika-aikar da ya yi, ta girgiza kai tana murmushin gefen baki a hankali tana furta “Maza akwai ƙazanta, yanzu da ni ce na aikata hakan abin mita ya samu.” Tattara duka kwanukan ta yi ta wanke ta gyara komai sannan ta ɗauki hijabi ta je maƙota gidansu Zinat.

Inna Hassana na ganin ta ta taso tana faɗar “Maraba! Maraba yau amarya ce a gidan namu?”

Ta gyaɗa kai alamar eh cikin fara’a ta gaishe da Innan.

Innan ta sake cewa “Jiya fa na ga kayan arziƙi Zinat ta kawo mini, na gode sosai.”

“Ai ba komai Inna.” Ƙatuwar baƙar ledar da ke hannunta ta miƙa mata tana faɗar “Ga wannan ki ajiyewa Zinat alƙawarin da na yi mata ne a jiyan.”

Washe da haƙora ta karɓe tana ƙoƙarin buɗe ledar da faɗar “Masha Allahu! An gode sosai Amarya. Ga kujera nan ki zauna na bar ki tsaye.” Ta yi maganar tana nuna mata kujerar roba da ke ajiye a tsakar gidan.
Ba musu ta zauna tana faɗar “Da ma Inna waya na zo a ara mini in kira mamanmu da alama kuma Zinat ta tafi makaranta.”

“Tabbas tana can jarabawa suke, amma dai bari na ba ki aron tawa idan za ta yi sai ki yi amfani da ita.”

Da to ta amsa, Inna ta shige ɗaki riƙe da ledar a hannunta sai ga shi ta dawo ba ledar sai ƙaramar wayarta ƙirar kamfanin itel kalar blue ta miƙawa Fatima.

Amsa ta yi ta loda katin mtn da ta shigo da shi a hannunta miƙe tana faɗar “Na gode Inna, idan ba damuwa zan je gida da ita idan na gama zan mayar miki.”

Ta yi hakan ne saboda tana buƙatar sirri.

“Ah haba dai amarya! Ki tafi da ita ki yi uzurinki a nutse idan kin gama kya maido mini.”

Godiya ta ƙara yi ta fice daga gidan ta dawo mata tare da zaunawa a falo ta loda number Innarta da ke cikin kanta tsaf.
Ringi ta yi har ta katse ba a ɗauka ba haka ta sake jarrabawa a karo na biyu ta ɗaga.

Sosai suka gaisa Innar ta tambaye ta “ya gidan komai dai lafiya ko?”
‘Ina fa lafiya Inna ina cikin wani hali a gidan nan.’

Wannan ne abin da ke ranta take so ta furta sai dai laɓɓanta sun yi gardama sai tsintar bakinta ta yi da shiryo kalaman ƙarya. “Lafiya lau inna, da ma na kira ki ne mu gaisa ya can Enugun?”

Ta ba ta amsa da “Komai lafiya na ma kusa shigowa Arewa in sha Allahu ko nan da wata biyu haka nake saka rai, sai dai mun daddale magana da baban naku zan sanar muku.”
Ta yi murna ƙwarai da jin cewa Innarta za ta zo kusa, ko ba komai za ta samu damar ganawa da ita ta kwanta kan kafaɗarta ta yi kuka ko ta ji sanyi da sassaucin maraicin rashin uba da a kwanakin nan yake damun ta sosai. Gani take kamar don mahaifinta ba ya raye ne Musa yake yi mata duk waɗannan abubuwan cin zarafin.

“Mama ya wajen Hauwa’u da yaronta suna lafiya kuwa?”

“Hauwa tana can Sokoto gidanta lafiyansu qlau, ba kwa gaisawa ne?”

Uzurin rashin waya ta ba wa Inna sai dai ba ta karɓi uzurin nata ba, ta fahimci hakan ne ta hanyar tambayar da ta watso mata. “Amma idan ke ba ki da waya shi mijinki ba yana da ita ba? Me zai hana ki saka ya kira miki ita ku gaisa?”

Ta fahimci Innan ba ta san ƙarfe nawa agogon rayuwar aurenta da Musa ke bugawa ba don haka ba ta ja ta da nisa ba ta ce “in Sha Allahu za a gyara Inna.”

“Yauwa ko ke fa? Ke ce babba Fatima ya kamata ki kula da zumuncinku da kyau ko bayan raina. A duniyar nan ba ki da wata ‘yar’uwa sama da ita, ku biyu kawai Allah ya ba ni. Allah ya jiƙan mahaifinku ko a ranar da zai mutu sai da ya yi ta jaddada mini batu a kan koya muku zumunci. Kar na sake ku raba kawunanku , wannan wasiyyar ita ce ma fi girman abin tunawa da ya bar mini a game da ku.”

Hawaye suka zubo ma Fatima ta saka tafin hannu ta share su, tana jin sabon fata na ina ma a ce za a dawo mata da rayuwar mahaifinta, ina ma a ce hannun a gogo zai koma baya su sake haɗuwa su zauna su huɗu innanta babanta, ita da ‘yar’uwarta. Tana ji da rayuwar za ta fi mata daɗi a kan wacce take ciki a yanzu.

Doguwar tattaunawar da suka kwararo tare da mahaifiyarta ta kusa mantar da ita maƙasudin kiran ta da ta yi.

Gyaran murya ta yi tana faɗar “Yauwa inna dama na kira ki ne in roƙi wata alfarma irin wacce ban taɓa nema ba tun bayan aurena.”

Innar ta tattare dukan hankalinta ta mayar gun sauraren gudar jinin tata don jin miye buƙatarta.

“Don Allah innarmu idan kina da kuɗi ko dubu goma ne ki turo mini zan…”

Sai kuma ta yi shiru zuciyarta na yi mata nauyi, ba ta so aikata hakan ba to amma ba ta da zaɓin da ya fi wannan a yanzu tun da ya kulle kayan abincinsa don ya ƙuntata mata.

Da zallar mamaki a cikin muryar Innan ta ce “Me za ki yi da wannan kuɗi Fatima? Ina mijinki ne da ba za ki tambaye shi ba? Yanzu ke duk ƙoƙarin da yaron nan yake yi a kanki tun kina gida ƙoƙarin ɓata masa suna kike?”

Ba ta yi mamakin furucin innan ba don ta san hakan za ta iya faruwa saboda yadda Musa yake nunawa duniya cewar yana ba ta cikakkiyar kulawa da kariya tun kafin aurensu. Ba iya mahaifiyarta ba daidai da waɗanda suka san rayuwar soyayyarta da shi ba za su yarda cewa Musa zai aikata irin wannan abun a gare ta ba, saboda yadda yake kyautatawa duka dangi na kusa da ita.

Da raunanniyar murya ta ce “Ba haka ba ne Inna da ma zan riƙe ne saboda yanayi na laulayi ba komai nake son ci ba, shi kuma kullum a gun aiki yake wuni.”

Sai a lokacin Innan ta ji ta gamsu da dalilin neman buƙatar cike da murna ta ce “Masha Allahu! Ki ce an kuma dacewa da rabo. To Allah ya raba lafiya, in sha Allahu zan saka babanku ya turo miki kuɗin ko zuwa dare ne, zan saka miki a asusun mai gidan naki.”

Cikin rawar baki ta ce “A’a inna ba na ma so ya san na karɓi kuɗi a hannunki zai yi faɗa, ki bari zan turo miki asusun da za ki sakan a ciki.”

Da wannan suka yi sallama suka rabu Innar tana ta farinciki da labarin cikin sai addu’o’i take jera mata na fatan sauka lafiya.

Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta sauka daga layin ta miƙe cike da nauyin zuciya ta koma gidansu Zinat ta ari asusun bankin Marwan (yayan Zinat) ta turawa mamansu sa’annan ta sake kiranta ta shaida mata tare da cewa ta kira wannan layin idan ta tura kuɗin za su sanar mata.

Al’amarin Musa kuwa tun da ya ƙarasa ofishinsa bai fi zaman mintuna goma ba ya kimtsa komai ya shiga lecture. A can ajin ma yana yi yana duba wayarsa cike da jiran tsammani har ya kammala darasinsa na awa ɗaya ya fito ya tada motarsa ya koma ofishinsu ya zauna kafin lokacin darasinsa na gaba ya kama.

Lokaci bayan lokaci yake duba wayarsa sai kuma ya ja tsaki ya ajiye, malam Isah wanda suke sharing ofis da shi yana lura da yanayinsa kamar yana da damuwa, to amma da ke malam Musan bai kasa da shi ba sai bai yi azarɓaɓɓin kwashewa ba yana dai ta faman bin sa da ido, ya san idan abin ya shafe shi shi da kansa zai labarta masa a kai.

Da Musa ya gaji da duba waya shiru sai ya miƙe ya fara safa da marwa cikin damuwa.

‘Ya aka yi ne har yanzu wuraren sha biyun rana ba kira daga gida? To ko dai ba ta sha maganin ba ne? Ya girgiza kai yana ƙaryata kansa da kansa.

‘Ina! Ba zai yiwu ba, da hannuna fa na ba ta maganin na tsare ta, da idanuna na ga sanda ta sha. A dai kwai abin da yake tafiya ba daidai ba.’

Wayarsa ya ɗauka daga kan teburin da ke gabansa wanda ke cike da jibgin takardu da na’ura ɗaya a kai ya fice zuwa ƙofar ofishin yana danna kiran wata lambar yana takawa cikin koridon yana nufar ƙofar wajen ginin da suke ciki.

Ringi biyu ana uku aka ɗaga daga can ɓangaren matar ke faɗar “Ya ta samu ne? Mun yi nasara?”

“Ina yaya, ba na jin alamun hakan ko a jikina shi ya sa na kira ki. Wai mutumin nan ba ce ana ya yi ƙwayar nan ba za ta fi awa uku ba a jikinta za ta fara aiki ba?”

Ta gyaɗa kai kamar yana ganin ta “Haka ya faɗa mana, kuma ni shaida ce a kan aikin wannan ƙwayar don na taɓa shayar da wata ‘yar ƙawata ita a lokacin da ta yi cikin shege. Sai dai fa cikakken aikinta bai kammala wani lokacin sai bayan kwana biyu, zuwa uku. Idan an yi sa’a kuma a kwana ɗaya ma zai yiwu ya danganta da yanayin jikinta. To amma ita Fatiman har yanzu ko alama ɗaya ba ta bayyana ba a jikinta?”

“Ba ni da cikakkiyar masaniya domin ina office yanzu, sai dai har zuwa yanzu ba wanda ya kira ni…”

Motsin da ya jiya a ta bayansa ya saka cikin hanzari ya rage sauti yana faɗar “Ina zuwa yaya zan kira ki idan na samu tabbaci.”

Yana gama faɗa bai jira cewarta ba ya kashe wayar cike da takaici ya ciji yatsarsa yana komawa inda ya fito da na bai gama ficewa daga dogon koridon ba.

Office ɗin ya shiga a gaggauce don bai fi saura mintuna biyu lokacin darasinsa na gaba ya fara ba. Ya shiga haɗa tarkacen system da handout ɗinsa da zai shiga da su ajin ya suri makullinsa ya fito tare da janyo ƙofar da ƙarfi har sai da ta yi ƙara. Malam Isah ya bi bayansa da kallo sake da baki a hankali ya furta “Tofah! Allah ya kyauta.”

Wa ce ce wannan matar da take ɗora Musa a keken ɓera? Ya alaƙarsu take?

Shin daga wannan Fatima ta tsira daga sharrin maigidan nata ko a kwai sauran kallo a gaba?

Ku ci gaba da biyo alkamin ummu Intisar

UMMU INTISAR CE

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here