Za'a Gabatar Da Makashin Hanifa A Gaban Babbar Kotu 9 Ga Fabarairu 2022

Za'a Gabatar Da Makashin Hanifa A Gaban Babbar Kotu 9 Ga Fabarairu 2022

 

Kotun Majistare  ta bayar da umarnin mayar da  shari'ar kisan Hanifa Abubakar gaban babbar kotun jiha.

 

Mai gabatar da kara Barista Aisha Mahmud ce ta yi wannan roko a gaban kotun inda ta shaida wa kotun cewa duba da cewa kotun ba ta da hurumin yin shariar kisa don haka sun kammala rubutu  game da tuhumar da ake yi wa wadanda ake zargin  sun kuma  mika  gaban babbar kotu don fara sauraren shari'ar.

"Mun nemi kotu ta dage wannan sharia ne domin  wannan kotun ba ta da hurumi yin shariar laifukan da ake zargin wadannan mutane da su don haka za mu gurfanar da su gaban babbar kotun jiha karkashin Justis Usman Naabba."
Ana dai zargin Abdulmalik Tanko da Hashim Isyaku da Fatima Jibrin da laifukan Hadin baki da yin garkuwa da mutane da boyewa da kuma kisa laifukan da suka saba da sashe na 97 da 274 da 277 da 221 a kundin tsarin dokar jiha.
Alkalin Kotun Mai Sharia Muhammad Jibrin ya bayar da iznin  sake gurfanar da wadanda ake zargi gaban babbar kotun jiha. Ya kuma yi umarnin ci gaba da tsare su a gidan gyaran hali har zuwa ranar 9 ga watan Fabreru, 2022.