Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya musanta zargin da Fadar Shugaban Ƙasa ta yi masa na cewa bai yi tsokaci ba bayan ceto ɗalibai da malamai da aka sace a Jihar Oyo, yana mai cewa ya fitar da sanarwa tun da farko inda ya yi maraba da ceton tare da yaba wa jami’an tsaro.
Atiku ya ce abin da bai yi ba shi ne yabon Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa shugaban ya fi mayar da hankali kan harkokin siyasa maimakon ya jagoranci al’umma bayan nasarar aikin ceto.
Ya kuma buƙaci Fadar Shugaban Ƙasa ta fi mayar da hankali kan magance matsalar tsaro maimakon ce-ce-ku-ce da ’yan adawa.





