Home Hausa Films Yar wasan Hausa Radeeya Jibril: Misali Na Gaskiya Wajen Haɗa Sana’a Da...

Yar wasan Hausa Radeeya Jibril: Misali Na Gaskiya Wajen Haɗa Sana’a Da Mutunci

18
0

Radeeya Jibril na daya daga cikin fitattun tauraruwa a masana’antar Kannywood waɗanda suka tabbatar da cewa nasara ta gaske ba ta ta’allaka ga samun shahara kaɗai ba, face tana zuwa ne tare da ginshiƙan ɗabi’a, jajircewa, da kuma kyakkyawar mu’amala da jama’a.

Tun da ta fara taka rawa a fagen fim, ta yi fice saboda hazaka da fasaha ta musamman wajen isar da saƙon da ke cikin fina-finai ta hanyar da ta dace da zuciyar mai kallo. Halayenta na nutsuwa da kuma ƙwarewa sun ba ta damar mallakar wuri na musamman a cikin zukatan masoyanta.

Babban abin burgewa shi ne yadda ta kasance mai girmamawa da kula da abokan aikinta da masoyanta duk da cewa harkar fim ta cika da matsaloli da ƙalubale iri-iri.

Matakin da ta ɗauka na shiga daga ciki zuwa rayuwar aure ya nuna wa duniya cewa rayuwa tana da matakai daban-daban, kuma mutum na iya sauya alkiblar rayuwarsa ta hanyar da ta dace ba tare da ya rasa daraja ko mutuncinsa ba. Wannan ya sa ta zama abin koyi ga kowa, musamman ga ƙannenmu ‘yan mata masu burin cimma nasara ba tare da sun saki linzamin tarbiyya da mutunci ba.

Muna mata fatan Allah Ya sanya albarka a rayuwar aurenta, Ya ba ta lafiya, da zama lafiya, da farin ciki tare da ɗaukaka. Tarihinta zai ci gaba da kasancewa abin abin alfahari a masana’antar fim ta Hausa, kuma masoyanta za su ci gaba da tuna gudummawar da ta bayar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here