Home Rahoto ‘Yan sandan Sakkwato sun sanya lokacin fara kamun masu aron hannu da...

‘Yan sandan Sakkwato sun sanya lokacin fara kamun masu aron hannu da sanya baƙin gilas na mota

13
0

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sokoto ta ce za ta fara aiwatar da Operation Velvet domin kama masu aron hannu da wadanda ke amfani da baƙin gilashin mota ba tare da rijista ba a fadin jihar.

Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Kakakin Rundunar, DSP Ahmad Rufa’i, ya fitar a ranar Talata 11 ga Agusta 2026.

Ya ce, za a fara aikin a ranar Alhamis 13 ga Agusta 2026, inda za a mayar da hankali kan motocin da ba su da izinin gilashi mai duhu wato Tinted, tuƙin a ron One Way, motocin da ba su da rajista, lambobin mota na bogi da kuma lambobin mota da aka rufe ko aka ɓoye.

Haka kuma za a ɗauki mataki kan sauran laifukan hanya da suka haɗa da tuƙin ganganci, ɗaukar kaya fiye da kima, rashin bin alamun hanya da tuƙi ba tare da lasisin tuƙi mai inganci ba.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Sokoto, CP Hayatu Hassan Shaffa, ya umurci jami’an da aka tura aikin su gudanar da shi cikin ƙwarewa da mutunta haƙƙin jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here