Home Labarai ‘Yan sanda sun daƙile harin ‘yan bindiga sun ƙwato dabbobi da yawa...

‘Yan sanda sun daƙile harin ‘yan bindiga sun ƙwato dabbobi da yawa a Sakkwato

15
0

 

Jami’an ‘yan sandan jihar Sakkwato sun daƙile wani hari da aka kai a Horo Birni da Marake a karamar hukumar Shagari in da ‘yan bindiga suka shiga ƙauyukkan suka yi ta harbe harbe kan mai uwa da wabi suka shiga gidajen mutane suka tattara dabbobin da ke yankin.

Bayan da jami’an ‘yan sanda suka samu labari suka haɗa ‘yan uwansu da sojoji aka tunkari ɓatagarin an shafe lokaci ana musayar wuta, da abin ya fi ƙarfin su suka gudu a cikin daji suka bar dabbobin da suka sato.

A bayanin da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda DSP Ahmad Rufa’i ya fitar ya ce an ƙwato Shanu 195 da Tumakai 84 da Raƙumi biyu, mutanen ƙauye mutum biyu ne harbin ‘yan bindiga ya samu yanzu suna asibiti domin magani.

Haka kuma ya ce a ranar Larabar ‘yan bindigar sun shiga ƙauyen Maikujera a ƙaramar hukumar Raɓah sun sace dabbobi 171 da suka haɗa da Shanu da Raƙummai da Akuyoyi da Tumakai, suma ba su yi nasara ba an ƙwato dabbobin amma ‘yan bindigar sun tsere a dajin da ke kusa da garin.

Daga cikin dabbobin da aka ƙwato 171 sun haɗa da raƙummai da shanu da Tumakai da Akuyoyi.

Kwamishinan ‘yan sanda CP Hayatu Hassan Shaffa ya yabawa jami’an tsaron da suka nuna ƙwazo da yin aiki cikin ƙwarewa har suka daƙile harin ‘yan bindiga suka kuma da dawo da dabbobin da aka sace a ƙauyukkan Sakkwato.

Ya roƙi mutane su cigaba da ba da goyon baya ga jami’an tsaro, a shirye suke su hukunta duk wanda aka samu da laifi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here