Home Labarai ‘Yan bindiga sun kashe mutane 32 a wani ƙauyen Sokoto

‘Yan bindiga sun kashe mutane 32 a wani ƙauyen Sokoto

43
0

Akalla mutane 32 ne suka rasa rayukansu bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai mummunan hari a garin Ungushi, da ke ƙaramar hukumar Kebbe ta Jihar Sokoto.

Mazauna yankin sun ce maharan sun shiga garin ne da misalin ƙarfe 2:15 na rana ranar Juma’a, a lokacin da jama’a ke gudanar da sallar Juma’a. Sun ce maharan sun ajiye baburansu a gaban masallaci, kafin su tarwatsa masu ibada sannan suka shiga cikin garin inda suka kashe mutane biyar.

Wani mazaunin garin da ya shaida harin ya ce bayan maharan sun tafi, mazauna sun fara shirye-shiryen binne waɗanda aka kashe, amma ‘yan bindigar sun sake dawowa suka kashe wasu mutane biyu. Daga bisani suka rika harbe-harbe daga sassa daban-daban, lamarin da ya tilasta wa wasu mazauna tserewa zuwa kan wani tsauni domin tsira.

Ya ce maharan sun ci gaba da zama a garin har zuwa misalin ƙarfe 1 na dare, sannan suka dawo da safe suka ci gaba da kashe wasu mazauna. Daga bisani jami’an tsaro sun isa yankin, abin da ya tilasta wa maharan ficewa.

Mazauna sun ce bayan sun koma garin ranar Lahadi, sun fara nemo gawarwakin wadanda aka kashe, inda daga ƙarshe suka gano tare da binne gawarwaki 32. Wani mazaunin ya kuma ce ya ga gawarwakin wasu ‘yan bindiga 13 da aka kashe yayin da mazauna ke kare kansu, amma daga baya sauran maharan suka kwashe gawarwakin abokan aikinsu.

An kuma ce maharan sun kona gidaje bakwai, shaguna biyu da motoci uku, yayin da suka kutsa cikin wasu al’ummomi kamar Umbutu, Maikurhuna, Gwandi, Girkau da Zugu, inda suka sace dabbobi da sauran kayayyaki.

Rahotanni sun ce hare-haren sun tilasta wa dimbin mazauna barin gidajensu zuwa garuruwa kamar Kebbe, Jega, Koko, Tambuwal, Aleiro, Agwada da wasu sassan jihohin Sokoto da Kebbi.

A gefe guda, Rundunar Sojin Najeriya ta ce Manjo Janar Bemgha Paul Koughna, Kwamandan Runduna ta 8 da ke Sokoto, ya kai ziyarar tantance yanayin tsaro a Kebbe da yankunan da abin ya shafa. Rundunar ta ce an sake tsara tsarin tsaro a yankin domin dakile kutse da hare-haren ‘yan ta’adda.

Rundunar ta kuma ce sojoji na nan daram domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da kira ga mazauna yankin da su ba jami’an tsaro sahihan bayanan sirri domin taimakawa wajen gano tare da dakile ayyukan kungiyoyin ta’addanci.

Sai dai Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Sokoto, CP Hayatu Hassan Shaffa, ya ce rundunar ba ta da cikakken bayani kan adadin wadanda aka kashe, amma ya tabbatar da cewa sojoji sun kai ziyara yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here